Koma ka ga abin da ke ciki


NAZARIN LITTAFI MAI TSARKI DA TAIMAKON WANI KO WATA

Ka Ji Dadin Rayuwa Har Abada!

Wannan nazarin kyauta ne, kuma tattaunawa ake yi bisa abin da Littafi Mai Tsarki ya ce. Nazarin zai taimaka maka ka san amsoshin tambayoyi kamar su:

  • Me zan yi don in samu farin ciki a rayuwata?

  • Shin za a daina mugunta da shan wahala kuwa?

  • Zan sake ganin mutanena da suka rasu kuwa?

  • Allah ya damu da ni kuwa?

  • Yaya zan yi addu’a don Allah ya ji ni?

Kyauta Ne

Duk nazarin da za a yi da kai kyauta ne. Littafin da ke taimakawa wajen nazarin, wato Ka Ji Dadin Rayuwa Har Abada! shi ma kyauta ake bayarwa. Za a kuma ba ka Littafi Mai Tsarki idan kana bukata.

Yadda Kake So Za A Yi Shi

Wanda zai koyar da kai zai iya zuwa inda kake, ko kuma ku yi nazarin ta waya. Wato duk lokaci da kuma wuri da ka zaba.

Babu Tilas a Ciki

Duk lokacin da ka ji ba ka son nazarin, za ka iya dainawa. Ba dole ba ne.

Yaya ake yin nazarin?

Za ka sami wanda zai taimaka maka ka fahimci abin da Littafi Mai Tsarki ya ce game da batutuwa dabam-dabam, daya bayan daya. (Idan mace ce, za a hada ta da mace.) Littafin nan Ka Ji Dadin Rayuwa Har Abada! ne za ku yi amfani da shi. Littafin yana da tambayoyi da nassosi. Yayin da kuke tattauna nassosin, a hankali za ka fahimci ainihin sakon da ke Littafi Mai Tsarki da kuma yadda zai amfane ka. Don karin bayani, ka kalli bidiyon nan ko ka karanta amsoshin tambayoyin da ake yawan yi game da nazarin.

Za ka so ka dan ga yadda littafin yake?

Ka ga darussan da ke farko farkon littafin

Za ka so ka yi nazarin?

Ka danna alamar da ke kasa don ka shirya yadda za a fara nazarin da kai.