Koma ka ga abin da ke ciki

Littafi Mai Tsarki Ya Ce Mutane Za Su Rika Yin Abubuwan da Suke Yi a Yau Ne?

Littafi Mai Tsarki Ya Ce Mutane Za Su Rika Yin Abubuwan da Suke Yi a Yau Ne?

Amsar Littafi Mai Tsarki

 E, Littafi Mai tsarki ya ce mutane za su dada yin abubuwa marasa kyau a zamaninmu. Ya ce yawancin mutane za su ki bin dabiꞌu masu kyau da kuma abubuwan da za su taimaka musu su zauna lafiya da juna. a (2 Timoti 3:​1-5) Amma Littafi Mai tsarki ya ce akwai wadanda ba za su bi irin halin nan ba. Kuma da taimakon Allah, za su guji halaye marasa kyau kuma su sa rayuwarsu da tunaninsu su jitu da yin nufinsa.​—Ishaya 2:​2, 3.

A wannan talifin za ka ga

 Mene ne Littafi Mai Tsarki ya ce game da abubuwan da mutane suke yi a yau?

 Littafi Mai Tsarki ya kwatanta munanan halayen da za su zama ruwan dare a zamanin nan, kuma hakan yana faruwa don son kai da mutane suke nunawa. Mutane za su zama “marasa kame kansu” da “masu sonkansu” da kuma “masu son jin dadin kansu fiye da son Allah.”​—2 Timoti 3:​2-4.

 Kamar yadda aka fada a Littafi Mai Tsarki, mutane da yawa a yau sun fi son kansu da abin da zai amfane su da abin da zai sa su yi farin ciki da abin da zai sa su ji kamar rayuwarsu tana da maꞌana, da dai sauransu. Irin halayen suna koꞌina kuma abin yana dada muni. Mutane da yawa sun dukufa wajen son kansu har ma sun zama “masu kin nagarta” wato ba sa son halayen kirki. Kari ga haka, su “marasa godiya” ne, suna gani kamar ba sa bukata su yi godiya don abin da suke da shi ko kuma don abin da wasu suka yi musu.​—2 Timoti 3:​2, 3.

 Son kai ne yake jawo wasu halayen da muke gani a zamaninmu, kamar su:

  •   Hadama. Mutane da yawa “masu son kudi” ne. Kuma suna gani kamar dukiyarsu ce take nuna cewa sun yi nasara a rayuwa.​—2 Timoti 3:2.

  •   Girman kai. Mutane da yawa “masu takama” ne da “girman kai,” da kuma “masu cika da daga kai.” (2 Timoti 3:​2, 4) Irin su sukan yi fahariya da kuma daukaka abin da suka iya ko halayensu ko kuma dukiyarsu.

  •   Bata sunan mutane. “Masu zage-zage” da “masu bata sunayen wadansu” suna koꞌina a duniya. (2 Timoti 3:​2, 3) Irin mutanen nan suna zagin wasu ko Allah ko kuma su yi karya game da su.

  •   Taurin kai. Mutane da yawa “marasa tsarki” ne, “masu rike juna a zuciya,” da “masu cin amana,” da kuma “marasa hankali.” (2 Timoti 3:​2-4) Suna nuna irin halayen nan, ta wajen kin canja raꞌayinsu ko kin amincewa da abin da wani ya fada, ko kuma kin cika alkawarin da suka dauka.

  •   Mugunta. Mutane da yawa “marasa tausayi” ne, suna saurin fushi, kuma hakan yakan kai ga mugunta.​—2 Timoti 3:3.

  •   Kin bin doka. Yesu ya ce “rashin bin doka zai karu” a zamaninmu. (Matiyu 24:​12, NWT.) Ya kuma ce a duk fadin duniya za a sami “tashin hankali.”​—Luka 21:9.

  •   Rashin kauna a iyali. “Marasa biyayya” da “marasa kauna” a iyali, sun sa ana samun rashin kula da cin zarafi da kuma mugunta a iyalai.​—2 Timoti 3:​2, 3.

  •   Mutum ya nuna kamar shi ibada ne. Ana samun karuwan mutanen da suke “nuna su masu addini ne.” (2 Timoti 3:5) Maimakon su yi nufin Allah, sukan bi ja-gorancin limamai da suke gaya musu abin da suke so su ji.​—2 Timoti 4:​3, 4.

 Ta yaya masu son kai suke bata halin wasu?

 Da yake mutane da yawa suna nuna son kai, ana samun karuwar mutanen da suke fama da matsalar kwakwalwa da kuma bakin ciki mai tsanani. (Mai-Waꞌazi 7:7) Alal misali, masu son kudi suna iya kokarinsu wajen cucin mutane. Marasa kauna za su iya cin zarafin mambobin iyalinsu, kuma hakan zai sa su soma bakin ciki mai tsanani ko ma su soma tunanin kashe kansu. Mutanen da ba su da rikon amana sukan jefa wadanda suka ci amanar su cikin damuwa na dogon lokaci.

 Me ya sa halayen mutane za su dada muni?

 Littafi Mai Tsarki ya bayyana ainihin da dalilin da yake sa halayen mutane suke dada muni:

  •   Kaunar da mutane suke yi wa Allah da kuma makwabtansu tana raguwa. (Matiyu 24:12) Don haka, mutane suna dada nuna son kai.

  •   An turo Shaidan daga sama zuwa duniyar nan. (Ruꞌuyar da Aka Yi wa Yohanna 12:​9, 12) Tun lokacin, yana sa mutane su dada zama masu son kai.​—1 Yohanna 5:19.

 Me ya kamata mu yi game da munanan halayen mutane?

 Kalmar Allah ta ce: “Ka guje wa irin mutanen nan.” (2 Timoti 3:5) Hakan ba ya nufin cewa za mu guji yin cudanya da mutane. Amma mu guji yin abokantaka na kud da kud da mutane masu son kai da kuma marasa ibada.​—Yakub 4:4.

 Halayen dukan mutane ne za su dada muni?

 Aꞌa. Littafi Mai Tsarki ya ce akwai mutanen za su rika “nishe-nishe suna kuka saboda dukan abubuwa masu ban kyamar da ake yi.” (Ezekiyel 9:4) Za su guji son kai kuma su rika bin kaꞌidodin Allah a rayuwarsu. Maganganunsu da ayyukansu za su yi dabam da na yawancin mutane. (Malakai 3:​16, 18) Alal misali, za su yi kokari su zauna lafiya da mutane kuma za su ki saka hannu a yake-yake da kuma mugunta.​—Mika 4:3.

 Halayen mutane za su rika tabarbarewa har duniya ta cika da mugunta da tashin hankali?

 Aꞌa. Halayen mutane ba za su tabarbare gabaki daya ba. A maimakon haka, Allah zai kawar da mutanen da suka ki bin dokokinsa. (Zabura 37:38) Zai kafa “sabuwar kasa” wato zai sa mutanen masu adalci su zauna a duniya cikin salama har abada. (2 Bitrus 3:13; Zabura 37:​11, 29) Wannan alkawarin ba tatsuniya ba ce. Yanzu haka ma, Littafi Mai Tsarki yana taimaka wa mutane su canja rayuwa su kuma soma bin kaꞌidodin Allah.​—Afisawa 4:​23, 24.

a Annabce-annabcen Littafi Mai Tsarki da kuma abubuwan da suke faruwa a duniya sun nuna cewa muna rayuwa a “kwanakin karshe,” da aka ce za a “sha wahala sosai.” (2 Timoti 3:1) Don karin bayani, ka duba talifin nan ‘Mene ne Alamar “Kwanakin Karshe”?