Koma ka ga abin da ke ciki

Wanene ko menene “Alpha da Omega”?

Wanene ko menene “Alpha da Omega”?

Amsar Littafi Mai Tsarki

 Lakabin nan “Alpha da Omega” suna nuni ne ga Jehobah Allah, Madaukaki. An ambata lakabin nan sau uku a cikin Littafi Mai Tsarki.​—Ruya ta Yohanna 1:8; 21:6; 22:13. a

Me ya sa Allah yake kiran kansa “Alpha da Omega”?

 Alpha da Omega su ne harafi na farko da na karshe a harufan Hellenanci, kuma shi ne yaren da aka yi amfani wajen rubuta sashen Littafi Mai Tsarki da ake kira Sabon Alkawari, da ya kunshi littafin Ruya ta Yohanna. An yi amfani da inda wadannan harufa suke a cikin harufan Hellenanci domin a misalta cewa Jehobah ne kadai wanda shi ne farko da kuma karshe. (Ruya ta Yohanna 21:6) Shi Allah Madaukaki ne tun can baya kuma zai ci gaba da zama Allah Madaukaki har abada. Shi ne kadai wanda yake ‘ba shi da farko, ba shi da karshe.’​—Zabura 90:2

Wane ne “na farko da kuma na karshe”?

 Littafi Mai Tsarki ya kira Allah da dansa Yesu da wadannan lakabin, amma ma’anarsu ya bambanta. Ga misalai guda biyu.

  •   A littafin Ishaya 44:6, Jehobah ya ce: “Ni ne na fari, ni ne kuma na karshe; ban da ni babu wani Allah.” A nan Jehobah ya nuna cewa shi ne Allah na gaskiya har abada, ban da shi, babu wani. (Kubawar Shari’a 4:​35, 39) Saboda haka, furucin nan, “na fari da na karshe” na nufin “Alpha da Omega.”

  •   Kari ga haka, an yi amfani da lakabin nan “na fari [pro’tos, ba alpha ba] da na karshe [e’skha·tos, ba omega ba]” a littafin Ruya ta Yohanna 1:​17, 18 da kuma 2:8. Ayoyin nan sun nuna cewa wanda ake zancensa ya mutu ya kuma tashi. Saboda haka, wadannan ayoyin ba sa magana game da Allah domin Allah bai taba mutuwa ba. (Habakkuk 1:​12) Amma Yesu ya mutu ya kuma tashi. (Ayyukan Manzanni 3:13-15) Shi ne na farko da ya taso daga matattu zuwa ga rai marar mutuwa a sama, inda yanzu yake zama “har abada abadin.” (Ruya ta Yohanna 1:​18; Kolosiyawa 1:​18) Yesu shi ne zai ta da matattu a nan gaba. (Yohanna 6:​40, 44) Saboda haka, shi ne na karshe wanda Jehobah da kansa ya ta da daga mutuwa. (Ayyukan Manzanni 10:40) Don haka, za a iya kiran Yesu “na Farko da na Karshe.”

Shin littafin Ruya ta Yohanna 22:13 ya ba da tabbaci cewa Yesu shi ne “Alpha da Omega”?

 A’a. Ba a bayyana ko wane ne ya yi furucin da ke Ruya ta Yohanna 22:13 ba, ban da haka, akwai masu magana dabam-dabam a wannan surar. Farfesa Willaim Barclay ya yi kalamai a kan wannan sashen Ruyar, ya cewa: “Ba a tsara rubutun wannan nassin ba, . . . don haka yana da wuya a san ainihin wane ne ke magana.” (The Revelation of John, Volume 2, Revised Edition, page 223) Saboda haka, za a iya cewa “Alpha da Omega” da aka ambata a Ruya ta Yohanna 22:13 da kuma wadanda aka ambata a wasu ayoyi a littafin, suna nuni ne ga Jehobah Allah.

a An sake yin amfani da lakabin nan a littafin Ruya ta Yohanna 1:​11 a cikin juyin King James. Amma, an cire lakabin a wannan ayar a yawancin juyin Littafi Mai Tsarki yanzu domin ba a sami furucin a tsohon rubutun Hellenanci ba amma an gano cewa daga baya ne aka yi karin sa’ad da ake kofan Littattafan.