Koma ka ga abin da ke ciki

Mene ne Ma’anar Abubuwan da Ke Cikin Littafin Ru’ya ta Yohanna?

Mene ne Ma’anar Abubuwan da Ke Cikin Littafin Ru’ya ta Yohanna?

Amsar Littafi Mai Tsarki

 Sunan littafin Ru’ya ta Yohanna a Helenanci shi ne, A·po·kaʹly·psis (apocalypse) kuma yana nufin “Ganowa” ko kuma “Bayyana Abu.” Wannan sunan ya bayyana ma’anar abubuwa da ke Ru’ya ta Yohanna, wato abubuwan da ba a gane ba kuma ya fadi abubuwan da za su auku shekaru da yawa bayan da aka rubuta shi. Annabce-annabce da yawa a cikin wannan littafin ba su cika ba tukun.

Takaitawar littafin Ru’ya ta Yohanna

  •   Gabatarwa.​—Ru’ya ta Yohanna 1:​1-9.

  •   Sakonni daga Yesu zuwa ga Ikilisiyoyi bakwai.​—Ru’ya ta Yohanna 1:10–​3:​22.

  •   Wahayin da ya nuna Allah yana zaune a kan kursiyinsa a sama.​—Ru’ya ta Yohanna 4:1-​11.

  •   Wahayi da dama daya bayan daya:

    •   Hatimai bakwai.​—Ru’ya ta Yohanna 5:1–​8:6.

    •   Kahoni bakwai, kuma guda uku na karshe sun gabatar da kaito guda uku.​—Ru’ya ta Yohanna 8:7–​14:20.

    •   Kasko guda bakwai, kuma kowannensu na dauke da annoba da ke wakiltar hukuncin Allah a kan duniyar nan.​—Ru’ya ta Yohanna 15:1–​16:21.

    •   Wahayin yadda Allah zai hallaka magabtansa.​—Ru’ya ta Yohanna 17:1–​20:10.

    •   Wahayin da suke nuna albarka da Allah zai yi wa sama da duniya.​—Ru’ya ta Yohanna 20:11–​22:5.

  •   Kammalawa.​—Ru’ya ta Yohanna 22:​6-​21.

Abin da zai taimaka maka ka fahimci littafin Ru’ya ta Yohanna

  1.   Ma’anar littafin Ru’ya ta Yohanna tana da ban karfafa ga bayin Allah kuma ba ya tsorata su. Ko da yake yawancin mutane suna daukan wannan kalmar “apocalypse” a matsayin wani bala’i mai girma, an soma da kuma kammala littafin Ru’ya ta Yohanna da cewa wadanda suka karanta, suka fahimta kuma suka yi amfani da abin da ke cikin littafin za su yi farin ciki.​—Ru’ya ta Yohanna 1:3; 22:7.

  2.   Akwai abubuwa da yawa da littafin Ru’ya ta Yohanna ya bayyana a alamance saboda haka, bai kamata a fahimce su a zahiri ba.​—Ru’ya ta Yohanna 1:1.

  3.   Muhimman batutuwa da kuma abubuwa da aka bayyana a alamance a cikin littafin Ru’ya ta Yohanna suna rubuce a wasu littattafan Littafi Mai Tsarki:

    •   Jehobah ne “Allah cikin sama” kuma shi ne Mahaliccin dukan abubuwa.​—Kubawar Shari’a 4:39; Zabura 103:19; Ru’ya ta Yohanna 4:11; 15:3.

    •   Yesu Kristi ne “Dan rago na Allah.”​—Yohanna 1:29; Ru’ya ta Yohanna 5:6; 14:1.

    •   Shaidan Iblis ne Magabcin Allah.​—Farawa 3:14, 15; Yohanna 8:44; Ru’ya ta Yohanna 12:9.

    •   Babila Babba tana kama da Babila ta dā (wato, Babel), magabcin Jehobah da bayinsa kuma shi ne tushen koyarwar addinan karya.​—Farawa 11:2-9; Ishaya 13:1, 11; Ru’ya ta Yohanna 17:4-6; 18:4, 20.

    •   “Teku” yana nufin ’yan Adam masu mugunta da suke hamayya da Allah.​—Ishaya 57:20; Ru’ya ta Yohanna 13:1; 21:1.

    •   Abubuwan da aka yi amfani da su da suka yi daidai da wadanda aka yi amfani da su a mazauni na dā don yi wa Allah ibada sun hada da sanduki na alkawari da teku na madubi (wato, daro don wanki) da fitilu da hadayun turare ta konewa da kuma bagadi don hadaya.​—Fitowa 25:10, 17, 18; 40:24-32; Ru’ya ta Yohanna 4:5, 6; 5:8; 8:3; 11:19.

    •   Bisan tana wakiltar gwamnatocin ’yan Adam.​—Daniyel 7:​1-8, 17-​26; Ru’ya ta Yohanna 13:​2, 11; 17:3.

    •   Lambobi da aka yi amfani da su a alamance.​—Ru’ya ta Yohanna 1:20; 8:13; 13:18; 21:16.

  4.   Su wahayin da suke ciki game da “ranar Ubangiji” ne, wadda ta soma a lokacin da aka kafa Mulkin Allah a shekara ta 1914 kuma lokacin ne Yesu ya soma sarauta. (Ru’ya ta Yohanna 1:10) Wannan ya nuna cewa a zamaninmu ne za mu ga cikar muhimman annabce-annabce da ke cikin littafin Ru’ya ta Yohanna.

  5.   Idan muna so mu fahimci abin da ke cikin littafin Ru’ya ta Yohanna, muna bukatar mu yi amfani da abubuwan da suka taimaka mana mu fahimci sauran littattafan Littafi Mai Tsarki. Wadannan abubuwan sun hada da hikima daga wurin Allah da kuma taimako daga wurin wadanda sun riga sun fahimci wadannan wahayin.​—Ayyukan Manzanni 8:26-39; Yakub 1:5.