Koma ka ga abin da ke ciki

Me Ya Sa Ya Kamata Mu Yi Addu’a a Cikin Sunan Yesu?

Me Ya Sa Ya Kamata Mu Yi Addu’a a Cikin Sunan Yesu?

Amsar Littafi Mai Tsarki

 Wajibi ne mu yi addu’a ga Allah cikin sunan Yesu domin ta hakan ne kadai Allah ya ce mu yi masa Addu’a. Yesu ya ce: “Ni ne hanya, Ni ne gaskiya, Ni ne rai: ba mai-zuwa wurin Uban sai ta wurina.” (Yohanna 14:6) Yesu ya kuma gaya wa manzanninsa masu aminci: “Hakika, hakika, ina ce muku, Idan kun roki komi ga Uba, za ya ba ku a cikin sunana.”—Yohanna 16:23.

Karin dalilai na yin addu’a a cikin sunan Yesu

  •   Muna daraja Yesu da Ubansa, Jehobah Allah.—Filibiyawa 2:9-11.

  •   Muna nuna godiya ga Allah saboda tanadin mutuwar Yesu don cetonmu.—Matta 20:28; Ayyukan Manzanni 4:12.

  •   Muna nuna mun fahimci matsayin Yesu na Matsakaici tsakanin mutane da Allah.—Ibraniyawa 7:25.

  •   Muna nuna mun daraja aikin da Yesu yake yi na Babban Firist da zai taimake mu mu kasance da tsayawa mai kyau wajen Allah.—Ibraniyawa 4:14-16.