Koma ka ga abin da ke ciki

YUNI 28, 2017
Kazakhstan

Kotun Kazakhstan Ya Amince da Rashin Adalcin da Aka Yi wa Teymur Akhmedov

Kotun Kazakhstan Ya Amince da Rashin Adalcin da Aka Yi wa Teymur Akhmedov

A ranar 20 ga Yuni 2017, Kotun Astana ya yi watsi da karar da Teymur Akhmedov ya shigar don yanke masa hukuncin shekara biyar a kurkuku da aka yi masa da kuma hana shi yin addininsa har na shekara 3 bayan ya fito daga kurkuku. Wani lauya da yake wajen sa’ad da kotun ya yanke hukuncin nan ya ce: “Wannan rashin adalci ne domin akwai hujjoji da yawa da suka nuna cewa Malam Akhmedov yana da gaskiya.” Lauyoyinsa za su ci gaba da daukaka karar.

A watan Janairu na 2017 ne jami’an Kwamitin Tsaro Na Kasa suka kama Malam Akhmedov don ya saka hannu a ayyukan addini da aka haramta a kasar. Ba su sake shi ba har sai ranar da aka yi masa shari’a a ranar 2 ga Mayu, 2017. A ranar, Kotun Yanki na Saryarkinskiy ya bi talifi na 174 karkashin sashe 2 na dokar kasar, wato Kazakhstan’s Criminal Code, kuma ya yanke masa hukunci. Dokar ta ba da izinin hukunta duk wanda ke da tsattsaurar ra’ayi game da addini. Malam Akhmedov bai amince da zargin da aka yi masa ba. Ya ce yana bayyana abin da ya yi imani da su ne kuma yana nuna kauna ne ga makwabtansa. Kundun tsarin mulkin kasar Kazakhstan ya ba wa kowane dan kasar ‘yancin fadan abubuwan da ya yi imani da su a addininsa. Kuma kasar Kazakhstan ta amince da ‘yanci na addini kamar yadda hukumar kāre hakkin dan Adam ta majalisar dinkin duniya ma ta amince da shi.