Koma ka ga abin da ke ciki

Koma ga abubuwan da ke ciki

Mene ne Sunan Allah?

Mene ne Sunan Allah?

Idan kana son ka san game da wani, ba mamaki za ka soma da yi masa wannan tambayar, “Mene ne sunanka?” Idan ka yi wa Allah wannan tambayar, me kake ganin zai ce?

“Ni ne Yahweh [Jehobah], sunana ke nan.”​Ishaya 42:8.

Mai yiwuwa wannan ne ƙaro na farko da ka soma jin sunan nan domin yawancin mafassaran Littafi Mai Tsarki ba sa cika amfani da ainihin sunan Allah. Wasu ma sun cire sunan gaba ɗaya daga nasu juyin. Sukan maye gurbinsa da laƙabin nan “UBANGIJI.” Amma sunan Allah ya bayyana aƙalla sau 7,000 a cikin ainihin yaren da aka rubuta Littafi Mai Tsarki da shi. An rubuta sunan da baƙaƙen harufa guda huɗu, wato YHWH ko kuma JHVH, kuma an daɗe ana fassara shi zuwa “Jehovah” ko Jehobah a Hausa.

Sunan Allah ya bayyana sau da yawa a cikin littattafan Ibrananci da kuma wasu juyin Littafi Mai Tsarki da yawa

Ƙarni na farko bayan haihuwar Yesu, IBRANANCI

Fassarar Tyndale 1530, TURANCI

Juyin Reina-Valera 1602, Sifanisanci

Juyin Union 1919, Cinanci

ABIN DA YA SA SUNAN ALLAH YAKE DA MUHIMMANCI

Sunan yana da muhimmanci ga Allah. Allah ne ya saka wa kansa sunan, ba wani ba. Jehobah ya ce: “Wannan shi ne sunana har abada, da wannan suna za a dinga kirana har dukan tsara masu zuwa.” (Fitowa 3:15) Sunan Allah ya bayyana a cikin Littafi Mai Tsarki fiye da laƙabin nan da ake kiransa da shi, wato Maɗaukaki da Ubangiji, ko kuma Allah. Ya kuma bayyana fiye da sunayen bayinsa, kamar su Ibrahim da Musa da Dauda da kuma Yesu. Ƙari ga haka, Jehobah yana son kowa da kowa ya san sunansa. Littafi Mai Tsarki ya ce: “Bari su san cewa kai kaɗai ne Mai suna Yahweh, Mafi Ɗaukaka a dukan duniya.”​—Zabura 83:18.

Sunan yana da muhimmanci ga Yesu. A cikin addu’ar da Yesu ya koyar da aka fi sani da Addu’ar Ubangiji, ya gaya wa almajiransa su yi addu’a ga Allah cewa: ‘A kiyaye sunanka da tsarki.’ (Matiyu 6:9) Yesu ma da kansa ya yi addu’a ga Allah ya ce: ‘Ya Uba, ka ɗaukaka sunanka.’ (Yohanna 12:28) Ɗaukaka ko kuma tsarkake sunan Allah yana da muhimmanci ga Yesu, shi ya sa ya ce: “Na kuma sanar musu da sunanka, zan kuma sanar da shi.”​—Yohanna 17:​26, Littafi Mai Tsarki.

Sunan yana da muhimmanci ga waɗanda suka san Allah. Bayin Allah a zamanin dā sun gaskata cewa sunan Allah yana kāre su da kuma sa su sami ceto. “Sunan Yahweh katanga mai ƙarfi ne, mai adalci yakan gudu ya shiga ya zauna lafiya.” (Karin Magana 18:10) “Duk wanda ya kira ga Sunan Yahweh domin neman taimako za a cece shi.” (Yowel 2:32) Littafi Mai Tsarki ya kuma nuna cewa sunan Allah ne zai sa a san waɗanda suke bauta masa. Ya ce: “Gama dukan ƙabilan mutane za su yi biyayya da sunan allahnsu, mu kuwa za mu yi biyayya da sunan Ubangiji Allahnmu har abada abadin.”​—Mika 4:​5, LMT; Ayyukan Manzanni 15:14.

ME SUNAN YAKE NUFI?

Sunan yana wakiltar Allah shi kaɗai. Masanan Littafi Mai Tsarki da yawa sun ce sunan yana nufin “Yana Sa Ya Kasance.” Jehobah ya sa mun fahimci ma’anar sunansa ta abin da ya gaya wa Musa: “Zan Zama Abin da Nake So In Zama.” (Fitowa 3:​14, New World Translation) Saboda haka, sunan bai nuna mana cewa shi ne mahaliccin kome da kome kawai ba. Amma ya nuna cewa yana da ikon sa kansa ko kuma halittunsa su yi duk wani abin da yake so. Laƙabi da ake kiran Allah da shi yana nuna matsayinsa ko ikonsa ko kuma ƙarfinsa, amma sunansa ne kaɗai yake wakiltar kome game da shi da kuma abubuwan da zai iya yi.

Sunan ya nuna cewa Allah yana ƙaunar mu. Ma’anar sunan Allah ta nuna cewa yana ƙaunar halittunsa har da mu ’yan Adam. Ƙari ga haka, tun da Allah ya sanar da sunansa, hakan yana nufin cewa yana son mu san shi. Domin shi ya gaya mana sunansa tun kafin mu tambaye shi. Hakika, Allah yana so mu san cewa za mu iya kusantar sa kuma mu zama aminansa.​—Zabura 73:28.

Idan muna amfani da sunan Allah, hakan zai nuna cewa muna ƙaunarsa. Alal misali, a ce ka gaya ma wani ainihin sunanka don kana so ya zama abokinka. Yaya za ka ji idan mutumin ya ƙi ya kira ka da ainihin sunanka? Da shigewar lokaci, za ka ji cewa mutumin ba ya son ya zama abokinka. Haka yake da Allah. Jehobah ya gaya ma ’yan Adam sunansa kuma ya ce mu riƙa kiransa da shi. Idan mun yi amfani da sunan, muna nuna ma Jehobah cewa muna so mu zama aminansa. Domin yana sane da waɗanda suke “yin tunanin sunansa.”​—Malakai 3:16.

Abu na farko da ya kamata mu yi idan muna son mu san Allah shi ne mu san sunansa. Amma bai ƙare a nan ba. Muna bukatar mu san halayensa.

MENE NE SUNAN ALLAH? Sunan Allah shi ne Jehobah ko kuma Yahweh. Sunan yana wakiltar Allah shi kaɗai kuma ya nuna cewa Allah zai iya yin duk wani abin da yake so