Koma ka ga abin da ke ciki

Koma ga abubuwan da ke ciki

ABIN DA KE SHAFIN FARKO | ME LITTAFI MAI TSARKI YA CE GAME DA RAI DA MUTUWA?

Abin da Littafi Mai Tsarki Ya Ce Game da Rai da Mutuwa

Abin da Littafi Mai Tsarki Ya Ce Game da Rai da Mutuwa

Labarin da ke cikin littafin Farawa ya nuna abin da Allah ya gaya wa mutum na farko, wato Adamu. Allah ya ce masa: “An yarda maka ka ci daga kowane itacen gona a sāke: amma daga itace na sanin nagarta da mugunta ba za ka ɗiba ba ka ci: cikin rana da ka ci, mutuwa za ka yi lallai.” (Farawa 2:​16, 17) Wannan ayar ta nuna sarai cewa da a ce Adamu ya bi dokar Allah, da ba zai mutu ba amma zai ci gaba da rayuwa a lambun da ake kira Adnin.

Amma maimakon Adamu da matarsa Hauwa’u su bi dokar Allah don su ci gaba da rayuwa, sun ci ’ya’yan itacen da Allah ya ce kada su ci. (Farawa 3:​1-6) Har a yau, muna jin jiki don rashin biyayyar da suka yi. Manzo Bulus ya bayyana abin da ya faru. Ya ce: “Zunubi ya shigo cikin duniya ta wurin mutum ɗaya, mutuwa kuwa ta wurin zunubi; har fa mutuwa ta bi kan dukan mutane, da yake duka sun yi zunubi.” (Romawa 5:12) Babu shakka, wannan “mutum ɗaya,” Adamu ne. Amma wane zunubi ne ya yi kuma me ya sa hakan ya jawo mutuwa?

Adamu ya yi zunubi sa’ad da ya karya dokar Allah da gangan. (1 Yohanna 3:4) Kuma Allah ya gaya masa cewa sakamakon zunubi mutuwa ne. Da a ce Adamu da ’ya’yansa sun bi dokar Allah, ba za su yi zunubi ba kuma ba za su taɓa mutuwa ba. Allah bai halicci mutane don su riƙa mutuwa ba, amma don su riƙa rayuwa har abada.

A bayyane yake cewa mutuwa ta “bi kan dukan mutane,” kamar yadda Littafi Mai Tsarki ya faɗa. Amma shin da akwai wani abu a jikin ’yan Adam da ke ci gaba da rayuwa bayan sun mutu? Mutane da yawa sun ce da akwai wani abu da ake kira kurwa da ba ta mutuwa. Amma idan hakan gaskiya ne, to abin da Allah ya gaya wa Adamu ba gaskiya ba ne. Me ya sa? Domin idan akwai wani abu a jikinmu da ke ci gaba da rayuwa bayan mun mutu, hakan ya nuna cewa sakamakon zunubi ba mutuwa ba ne. Amma Littafi Mai Tsarki ya ce: “Ba shi yiwuwa Allah ya yi ƙarya.” (Ibraniyawa 6:18) A gaskiya, Shaiɗan ne ya yi ƙarya sa’ad da ya gaya wa Hauwa’u cewa: “Hakika ba za ku mutu ba.”​—Farawa 3:​4, Littafi Mai Tsarki.

Ga wata muhimmiyar tambaya, Idan koyarwar nan cewa kurwa ba ta mutuwa ba gaskiya ba ce, to, mene ne ke faruwa sa’ad da muka mutu?

LITTAFI MAI TSARKI YA FAƊI GASKIYA

Littafin Farawa ya ce: “Ubangiji Allah kuwa ya sifanta mutum daga turɓayar ƙasa, ya hura masa numfashin rai cikin hancinsa; mutum kuma ya zama rayayyen mai-rai.” An fassara furucin nan “rayayyen mai-rai” daga kalmar Ibranancin nan ne’phesh, * wanda ke nufin “halitta mai numfashi.”​—Farawa 2:7.

Littafi Mai Tsarki bai ce an saka wa ’yan Adam kurwar da ba ta mutuwa ba sa’ad da aka halicce su. Maimakon haka, kowane mutum “mai rai” ne. Shi ya sa ko da ka yi shekaru dubu kana bincika Littafi Mai Tsarki, ba za ka taɓa ganin furucin nan “kurwa marar mutuwa” ba.

Tun da Littafi Mai Tsarki bai ce ’yan Adam suna da kurwar da ba ta mutuwa ba, me ya sa addinai da yawa suke fifita wannan koyarwar? Abin da ya faru a ƙasar Masar zai sa mu sami amsar wannan tambayar.

KOYARWAR ƘARYA TA YAƊU

Wani ɗan tarihi Baheleni, mai suna Herodotus da ya rayu a ƙarni na biyar ya ce: “Masarawa ne suka fara yin imani cewa kurwa ba ta mutuwa.” Babiloniyawa ma sun yi imani da wannan koyarwar. A lokacin da Iskandari Mai Girma ya yi nasara a kan Gabas ta Tsakiya a shekara ta 332 kafin haihuwar Yesu, malaman Helenawa sun riga sun yaɗa wannan ra’ayin sosai. Jim kaɗan bayan haka, sai koyarwar ta bazu a ko’ina a Daular Helas.

Ba za ka taɓa ganin furucin nan “kurwa marar mutuwa” a cikin Littafi Mai Tsarki ba

A ƙarni na farko bayan haihuwar Yesu, ɗarikun nan biyu na Yahudawa, wato Farisiyawa da ’yan addinin Essenes suna koyar da cewa idan mutum ya mutu, kurwarsa ba ta mutuwa. Littafin nan The Jewish Encyclopedia ya ce: “Helenawa da kuma musamman Plato ne suka sa Yahudawa suka soma imani da koyarwa game da kurwar da ba ta mutuwa.” Hakazalika, wani ɗan tarihi Bayahude mai suna Josephus ya ce wannan koyarwar ta samo asali daga “abin da Helenawa” suka yi imani da shi ba daga Littafi Mai Tsarki ba. Kuma ya ce wannan koyarwar tatsuniya ce.

Da al’adar Helenawa ta soma yaɗuwa a ko’ina, sai ’yan coci suka soma imani da wannan koyarwar. Wani ɗan tarihi mai suna Jona Lendering ya ce: “Plato ya koyar da cewa a dā kurwarmu tana wuri mai kyau, amma yanzu tana cikin muguwar duniya. Hakan ne ya sa ya kasance da sauƙi ’yan coci su yi imani da koyarwarsa.” Ta haka, wannan koyarwar ƙarya ta shigo cikin coci kuma ta yi fice sosai.

‘GASKIYA ZA TA ’YANTAR DA KU’

A ƙarni na farko, manzo Bulus ya yi wannan gargaɗin: “Ruhu musamman ya ce, a can wani zamani waɗansu za su fanɗare wa bangaskiya, su mai da hankali ga aljannu masu ruɗi, da kuma koyarwar aljannu.” (1 Timotawus 4:​1, LMT) Wannan furucin ya cika da gaske! Koyarwar kurwa da ba ta mutuwa tana ɗaya daga cikin “koyarwar aljannu.” Koyarwar ba ta cikin Littafi Mai Tsarki kuma an samo ta ne daga addinan ƙarya na zamanin dā da kuma ra’ayoyin mutane.

Amma muna farin ciki domin Yesu ya ce: “Za ku san gaskiya, gaskiyar kuwa za ta ’yantar da ku.” (Yohanna 8:32) Mun san gaskiyar da ke cikin Littafi Mai Tsarki kuma gaskiyar ta ’yantar da mu daga koyarwar ƙarya da ke ɓata wa Allah rai da kuma abubuwan da addinai da yawa suka yi imani da su. Ƙari ga haka, gaskiyar da ke cikin Kalmar Allah ta ’yantar da mu daga al’adun da ake bi sa’ad da wani ya mutu.​—Ka duba akwatin nan “ Ina Matattu Suke?

Ba nufin Mahaliccinmu ba ne mutane su rayu shekara 70 ko 80 a duniya, bayan haka sai su yi rayuwa har abada a wani wuri dabam. Amma nufinsa shi ne mutane su yi rayuwa a duniyar nan har abada. Wannan ya nuna cewa Allah yana ƙaunarmu kuma babu kome da zai iya canja abin da ya shirya wa mutane. (Malakai 3:6) Wani marubucin zabura ya ce: “Masu-adalci za su gāji ƙasan, su zauna a cikinta har abada.”​—Zabura 37:29.

 

^ sakin layi na 9 Wasu juyin Littafi Mai Tsarki, kamar su Littafi Mai-Tsarki Mai Makamantu Ayoyi, ya fassara ne’phesh zuwa “rayayyen taliki,” juyin nan kuma Littafi Mai Tsarki Juyi Mai Fitar da Ma’ana ya ce “mai rai.”