Koma ka ga abin da ke ciki

Koma ga abubuwan da ke ciki

ABIN DA KE SHAFIN FARKO

Yadda Za Mu Jimre Sa’ad da Wani Ya Rasu

Yadda Za Mu Jimre Sa’ad da Wani Ya Rasu

“Allah ya san abin da ya fi dacewa da mu, ƙawata. . . . Kada . . . ki yi . . . kuka.”

Abin da aka gaya wa wata mai suna Barbara ke nan, sa’ad da ake jana’izar mahaifinta da ya rasu sanadiyyar hatsarin mota.

Barbara * ta shaƙu da mahaifinta sosai kafin ya rasu. Shi ya sa abin da ƙawarta ta gaya mata bai ta’azantar da ita ba. Ta riƙa tunani cewa: “To, rasuwa ce ta fi dacewa da shi?” Shekaru bayan haka, Barbara ta rubuta abin da ya faru a littafi kuma ta gane cewa har ila, ba ta daina makoki ba.

Barbara ta kuma gane cewa yana ɗaukan lokaci kafin a daina makoki, musamman ma idan an shaƙu sosai da mutumin kafin ya rasu. Littafi Mai Tsarki ya ce mutuwa “magabciyar ƙarshe” ce. (1 Korintiyawa 15:​26, Littafi Mai Tsarki) Mutuwa tana zuwa ba zato ba tsammani kuma hakan yana sa mu baƙin ciki sosai. Ba yadda za mu iya guje mata. Ba abin mamaki ba ne idan muka rasa na yi bayan wani ya rasu.

Wataƙila ka taɓa tunani cewa: ‘Yaushe zan daina makokin nan? Ta yaya zan sami ta’aziya? Yaya zan iya ta’azantar da wasu da suke makoki? Zan ƙara ganin dangina ko abokaina da suka rasu kuwa?’

[Ƙarin bayani]

^ sakin layi na 5 An canja sunan.