Koma ka ga abin da ke ciki

Koma ga abubuwan da ke ciki

ABIN DA KE SHAFIN FARKO | YADDA AKA KĀRE LITTAFI MAI TSARKI

’Yan Hamayya Sun Kasa Halaka Littafi Mai Tsarki

’Yan Hamayya Sun Kasa Halaka Littafi Mai Tsarki

ƘALUBALE: ’Yan siyasa da kuma malaman addinai da yawa sun yi abubuwan da suka saɓa wa saƙon da ke cikin Littafi Mai Tsarki. Sau da yawa, sun yi amfani da ikonsu wajen neman su hana mutane kasancewa da Littafi Mai Tsarki da buga shi ko kuma fassara shi. Ka yi la’akari da misalai biyu:

  • A Wajen Shekara ta 167 Kafin Haihuwar Yesu: Sarki Antiochus Epiphanes, wanda ya nemi ya sa Yahudawa su bi addinin Helenawa ƙarfi da yaji ya sa a halaka dukan kofofin Nassosin Ibrananci. Wani ɗan tarihi mai suna Heinrich Graetz ya ce: “Bayin Sarki Epiphanes sun ƙona dukan nassosin da suka gani kuma sun kashe duk wani mutumin da bai ba su haɗin kai ba ko kuma ya kai ƙara.”

  • Bayan Zamanin Manzanni: Wasu limaman Katolika sun yi fushi cewa mutanen da ba limamai ba suna koyar da Littafi Mai Tsarki maimakon koyarwar cocin Katolika. Don haka, suka hana su kasancewa da Littafi Mai Tsarki, sai dai littafin Zabura kawai na yaren Latin. A wani babban taro da limaman coci suka yi, sun ba da umurni cewa a riƙa bi gida-gida da sako-sako don a tabbatar da cewa ana bin wannan dokar kuma a ƙona duk wani gidan da aka ga waɗannan littattafan a ciki.

Da a ce maƙiyan Littafi Mai Tsarki sun yi nasara wajen halaka shi, da a yau ba mu san saƙon da ke cikinsa ba.

Littafi Mai Tsarki da William Tyndale ya juya zuwa Turanci ya tsira duk da cewa an sa masa takunkumi, an ƙona wasu, kuma an kashe Tyndale a shekara ta 1536

YADDA LITTAFI MAI TSARKI YA TSIRA: Sarki Antiochus ya fi tsananta harinsa a ƙasar Isra’ila, amma Yahudawa da yawa sun riga sun ƙaura zuwa wasu ƙasashe. Masana sun ce sama da kashi sittin na Yahudawa suna zama a wasu ƙasashe a ƙarni na farko bayan haihuwar Yesu. Yahudawa sun ajiye Nassosi a majami’u kuma waɗannan Nassosin ne Kiristoci da kuma mutanen da suka rayu bayan wannan zamanin suka yi amfani da su.—Ayyukan Manzanni 15:21.

Bayan zamanin manzannin Yesu, mutanen da suke son Littafi Mai Tsarki sun ci gaba da fassara da kuma kofe Nassosi duk da hamayya. An riga an fassara littattafai dabam-dabam na Littafi Mai Tsarki zuwa harsuna talatin da uku kafin tsakiyar ƙarni na 15 da aka soma ƙera na’urorin buga littattafai. Bayan haka, an fassara da kuma buga Littafi Mai Tsarki a hanyar da ba a taɓa yi ba.

SAKAMAKO: Duk da hamayya daga sarakuna da kuma wasu limamai, Littafi Mai Tsarki ne littafin da aka fi karantawa da kuma fassarawa a duniya. Ƙari ga haka, Littafi Mai Tsarki ya inganta dokoki da kuma yaren wasu ƙasashe kuma yana gyara rayuwar miliyoyin mutane.