Koma ka ga abin da ke ciki

Koma ga abubuwan da ke ciki

Ka Sani?

Ka Sani?

Kwatancin da Yesu ya bayar game da “karnuka” zagi ne?

Wata yarinya riƙe da kare (Romawa ko Helenawa ne suka ƙera ta a tsakanin ƙarni na farko K.H.Y. zuwa ƙarni na biyu B.H.Y.)

Wata rana da Yesu yake Suriya a yankin ƙasar Roma, wata Baheleniya ta zo neman taimako wurinsa. A cikin amsar da ya ba ta, ya kwatanta mutanen da ba Yahudawa ba da “karnuka.” A Dokar da aka ba da ta hannun Musa, karnuka dabbobi marasa tsabta ne. (Levitikus 11:27) Shin hakan yana nufin cewa Yesu ya zagi wannan ’yar Helas da kuma sauran mutanen da ba Yahudawa ba ne?

A’a. Kamar yadda Yesu ya bayyana wa mabiyansa, Yahudawa ne kawai yake so ya taimaka wa a lokacin. Shi ya sa ya ce wa matar: “Bai da kyau a ɗauki abincin ’ya’ya a jefa wa karnuka.” (Matta 15:​21-26; Markus 7:26) Helenawa da Romawa suna son karnuka sosai kuma sukan ajiye su a gidajensu don su riƙa wasa da yara. Saboda haka, sa’ad da Yesu ya yi furucin, ba ta ji cewa ya yi mata baƙar magana ba. A maimakon haka, ta ga cewa yana ƙaunarta. Matar ta ce: “Gaskiya, Ubangiji; gama ko karnuka sukan ci cikin ɓarɓashin da ke faɗiwa daga tebur na iyayengijinsu.” Yesu ya yaba mata don bangaskiyarta kuma ya warkar da ’yarta.​—Matta 15:​27, 28.

Shawarar da manzo Bulus ya bayar cewa a ɗan jinkirta tashi daga gaɓar tekun ta dace kuwa?

Hoton wani babban jirgin ruwa (ƙarni na farko bayan haihuwar Yesu)

Bulus ya shiga jirgin ruwan da zai kai shi ƙasar Italiya, kuma sun yi fama da iska mai ƙarfi. Da suka ɗan tsaya, sai manzon ya ce kada su ci gaba da tafiyar. (Ayyukan Manzanni 27:​9-12) Wannan shawarar da ya bayar ta dace kuwa?

A zamanin dā, masu tuƙa jirgin ruwa sun san cewa yin tafiya a Bahar Maliya a lokacin ɗari yana da haɗari sosai. Mutane ba sa iya yin tafiya daga 15 ga Nuwamba zuwa 15 ga Maris. Amma wataƙila a watan Satumba ko Oktoba ne za a yi tafiyar, shi ya sa Bulus ya ce a ɗan dakata. Littafin nan Epitome of Military Science da wani ɗan Roma mai suna Vegetius ya rubuta (a ƙarni na huɗu), ya ce: “A wasu watanni, ana iya yin tafiya da jirgin ruwa amma wasu watanni, yin hakan yana da haɗari ko kuma ba zai yiwu ba.” Vegetius ya nuna cewa irin wannan tafiyar ta fi kyau daga 27 ga Mayu zuwa 14 ga Satumba. Amma yin tafiya daga 15 ga Satumba zuwa 11 ga Nuwamba ko kuma 11 ga Maris zuwa 26 ga Mayu yana da haɗari sosai. Da yake Bulus mai tafiye-tafiye ne, ya san da hakan sosai. Ko da yake mai jirgin da kuma matuƙin sun san da haka, sun ƙi bin shawarar Bulus. A ƙarshe, sun yi hatsari.​—Ayyukan Manzanni 27:​13-44.