Koma ka ga abin da ke ciki

Koma ga abubuwan da ke ciki

TALIFIN NAZARI NA 22

Ka Ci Gaba da Yin Tafiya a “Hanyar Tsarki”

Ka Ci Gaba da Yin Tafiya a “Hanyar Tsarki”

“Hanya mai kyau za ta kasance a wurin, . . . ‘Hanyar Tsarki.’”​—ISHA. 35:8.

WAƘA TA 31 Ka Bi Allah!

ABIN DA ZA A TATTAUNA a

1-2. Wace shawara mai muhimmanci ce Yahudawa da suke zama a ƙasar Babila suke bukatar su yanke? (Ezra 1:​2-4)

 SARKI ya yi wata sanarwa! Yahudawa da suka yi shekaru 70 suna bauta a Babila sun sami ꞌyanci, kuma za su iya komawa ƙasarsu Israꞌila. (Karanta Ezra 1:​2-4.) Jehobah ne kawai zai iya sa hakan ya faru. Me ya sa muka faɗi hakan? Domin Babiloniyawa ba sa ba wa bayinsu ꞌyanci. (Isha. 14:​4, 17) Amma an ci ƙasar Babila da yaƙi, kuma sabon sarkin ya gaya wa Yahudawan cewa za su iya barin ƙasar. Don haka, dukan Yahudawan musamman ma magidanta suna bukatar su yanke shawara ko za su ci gaba da zama a Babila ko za su koma Israꞌila. Mai yiwuwa yanke shawarar nan bai yi musu sauƙi ba. Me ya sa?

2 Da yawa daga cikin Yahudawan ba za su iya komawa Israꞌila ba saboda tsufa. Kuma da yake an haifi yawancin Yahudawan a Babila, ba su taɓa yin rayuwa a wani wuri ba. A ganinsu, ƙasar Israꞌila ƙasar kakaninsu ce. Da alama wasu Yahudawa sun yi arziki sosai a Babila. Don haka, zai yi musu wuya su bar ƙasar Babila inda suke da arziki su koma ƙasar da ba su sani ba.

3. Wace albarka ce Yahudawan da suka koma Israꞌila za su samu?

3 A ganin Yahudawa masu aminci, komawa ƙasar Israꞌila zai kawo musu albarka sosai fiye da sadaukarwa da za su yi. Albarka mafi muhimmanci da za su samu ita ce bautar da za su yi wa Jehobah. Ko da yake akwai haikali fiye da 50 na allolin ƙarya a Babila, babu haikali inda Yahudawan za su riƙa miƙa hadayu ga Jehobah kamar yadda Dokar Musa ta ce, kuma babu firistoci. Ƙari ga haka, mutanen da suke bauta ma allolin ƙarya sun fi waɗanda suke bauta wa Jehobah yawa sosai. Don haka, dubban Yahudawa da suke ƙaunar Jehobah suna marmarin lokacin da za su koma ƙasarsu domin su maido da bauta ta gaskiya.

4. Wane taimako ne Jehobah ya yi alkawari zai yi wa Yahudawan da suke komawa Israꞌila?

4 Wannan tafiyar za ta iya ɗauki Israꞌilawan watanni huɗu. Amma Jehobah ya yi alkawari cewa zai kawar da duk wani abin da zai iya hana su komawa. Ishaya ya rubuta cewa: “Ku shirya wa Yahweh hanya a daji, . . . za a gyara hanyar gargada ta miƙe, mummunan wurare za su zama sumul!” (Isha. 40:​3, 4) Ka ɗauka kana ganin hanya sumul a daji, ba shakka matafiya za su ji daɗin yin tafiya a hanyar. Zai fi musu sauƙi su yi tafiya a kan hanya da take sumul, maimakon su riƙa hawa da sauka a kan tuddai ko su yi tafiya a cikin kwari. Ƙari ga haka, za su yi saurin isa inda za su.

5. Wane suna ne aka ba wa hanyar da ke tsakanin Babila da Israꞌila?

5 A yau, akan ba wa hanyoyi sunaye ko lamba. Littafi Mai Tsarki ya ce: “Hanya mai kyau za ta kasance a wurin, za a kira ta, ‘Hanyar Tsarki.’ Ba mai ƙazanta wanda zai bi ta hanyar nan.” (Isha. 35:8) Ta yaya Israꞌilawan za su amfana daga alkawarin nan, kuma ta yaya mu ma muke amfana daga alkawarin a yau?

“HANYAR TSARKI” A DĀ DA KUMA YANZU

6. Me ya sa aka ba wa hanyar sunan nan, “Hanyar Tsarki”?

6 Sunan nan “Hanyar Tsarki” suna ne mai kyau sosai. Me ya sa aka ba wa hanyar suna tsarki? Domin ba za a yarda “mai ƙazanta” ya kasance a cikin ƙasar Israꞌila ba, wato duk Baꞌyahuden da ya ci gaba da yin lalata da bautar gumaka da kuma wasu zunubai masu tsanani. An bukaci Yahudawan da suka koma ƙasar Israꞌila su zama alꞌumma mai “tsarki ga Yahweh” Allahnsu. (M. Sha. 7:6) Hakan ba ya nufin cewa waɗanda suka koma Israꞌila ba sa bukatar su yi wasu canje-canje a rayuwarsu don su faranta wa Allah rai.

7. Waɗanne canje-canje ne Yahudawan suke bukatar su yi? Ka ba da misali.

7 Kamar yadda muka gani a somawar talifin nan, an haifi yawancin Yahudawan ne a Babila, kuma da yawa daga cikinsu sun saba da yadda mutanen Babila suke tunani da kuma yin abubuwa. Shekaru 69 bayan rukunin Yahudawa na farko sun dawo Israꞌila, Ezra ya sami labari cewa Yahudawan sun soma auran waɗanda ba sa bauta wa Jehobah. (Fit. 34:​15, 16; Ezra 9:​1, 2) Bayan wasu lokuta kuma, Gwamna Nehemiya ya yi mamakin jin cewa wasu yara da aka haifa a Israꞌila ba sa jin Ibrananci. (M. Sha. 6:​6, 7; Neh. 13:​23, 24) Ta yaya yaran za su koya game da Jehobah kuma su ƙaunace shi idan ba sa jin Ibrananci, harshen da aka rubuta Littafi Mai Tsarki da shi? (Ezra 10:​3, 44) Don haka, Israꞌilawan suna bukatar su yi canje-canje sosai a rayuwarsu. Amma yin waɗannan canje-canjen ba zai yi musu wuya sosai ba domin a ƙasar Israꞌila suke, kuma an soma maido da bauta ta gaskiya a-hankali-a-hankali.​—Neh. 8:​8, 9.

Tun shekara ta 1919 bayan haihuwar Yesu, miliyoyin mutane, maza da mata da yara sun bar Babila Babba kuma suka soma tafiya a “Hanyar Tsarki” (Ka duba sakin layi na 8

8. Me ya sa muke bukatar mu mai da hankali ga abubuwan da suka faru shekaru da yawa da suka shige? (Ka duba hoton da ke shafin farko.)

8 Wasu za su iya ce ‘wannan labari ne mai daɗi, amma shin abin da ya faru da Yahudawa tun dā ya shafe mu a yau?’ Ƙwarai kuwa, domin mu ma kamar dai muna tafiya ne a “Hanyar Tsarki.” Ko da mu shafaffu ne ko “waɗansu tumaki” muna bukatar mu ci gaba da bin “Hanyar Tsarki” domin za ta taimaka mana mu ci gaba da bauta ma Jehobah a yanzu da kuma a nan gaba saꞌad da Mulkin Allah zai mai da duniya aljanna. b (Yoh. 10:16) Tun daga 1919, miliyoyin maza da mata da yara sun bar Babila Babba wadda ita ce daular addinin ƙarya, kuma suka soma tafiya a “Hanyar Tsarki.” Da alama kana cikinsu. Ko da yake wajen shekaru 100 da suka shige ne aka soma tafiya a hanyar nan, akwai wasu da suka yi shekaru suna shirya hanyar kafin lokacin.

YADDA AKA SHIRYA HANYAR

9. Kamar yadda Ishaya 57:14 ta ce, waɗanne shirye-shirye ne aka yi a “Hanyar Tsarki”?

9 Saꞌad da Yahudawan suke barin Babila, Jehobah ya cire duk wani abin da zai hana su tafiya. (Karanta Ishaya 57:14.) Waɗanda suke tafiya a “Hanyar Tsarki” a yau kuma fa? Ɗarurruwan shekaru kafin 1919, Jehobah ya sa waɗanda suke ƙaunar sa su kyautata hanyar don mutane su iya barin Babila Babba. (Ka kuma duba Ishaya 40:3.) Sun yi gyare-gyare da ake bukata a hanyar domin mutane masu zukatan kirki su iya barin bautar ƙarya, kuma su soma bauta ma Jehobah tare da bayinsa. Mene ne shirye-shiryen suka ƙunsa? Ka yi laꞌakari da wasu shirye-shiryen da suka yi.

Mutanen da suke tsoron Allah sun yi Ɗarurruwan shekaru suna  gyara hanyar da mutane za su bi don su fita daga Babila Babba (Ka duba sakin layi na 10-11)

10-11. Ta yaya buga Littafi Mai Tsarki da fassara shi ya sa koyarwar gaskiya ta ƙara yaɗuwa? (Ka kuma duba hoton.)

10 Buga littattafai. Kafin shekara ta 1450, da hannu ne ake kwafan Littafi Mai Tsarki. Aikin yana ɗaukan dogon lokaci, kuma Littafi Mai Tsarki yana da tsada da kuma wuyar samuwa. Amma saꞌad da aka fitar da injin buga littattafai, buga Littafi Mai Tsarki da kuma rarraba shi ya zo da sauƙi.

11 Fassara. An yi ɗarurruwan shekaru ana amfani da Littafi Mai Tsarki a harshen Latin kawai kuma mutane masu ilimi ne kaɗai suke iya karantawa. Da aka samu injunan buga littattafai da dama, masu tsoron Allah sun soma fassara Littafi Mai Tsarki a harsuna da mutane da yawa za su iya karantawa. Don haka, mutane sun soma gwada abin da limaman coci suke koya musu da abin da suka karanta a Littafi Mai Tsarki.

Mutanen da suke tsoron Allah sun gyara hanyar da mutane za su bi don su fita daga Babila Babba (Ka duba sakin layi na 12-14) c

12-13. Ta yaya wasu ɗaliban Littafi Mai Tsarki suka soma fallasa koyarwar ƙarya a ƙarni na 19?

12 Littattafai da suke bayyana Littafi Mai Tsarki. Ɗaliban Littafi Mai Tsarki sun yi nazari da kyau kuma sun koyi abubuwa daga Kalmar Allah. Ƙari ga haka, sun gaya wa mutane abubuwan da suka koya, amma hakan bai yi ma limaman coci daɗi ba. Alal misali, a wajen shekara ta 1835, da yawa daga cikin ɗaliban sun soma rarraba warƙoƙi da suka fallasa koyarwar ƙarya da malaman addinai suke yi.

13 Wajen shekara ta 1835, wani mai tsoron Allah mai suna Henry Grew, ya wallafa wata warƙa da ta bayyana abin da yake faruwa da mutum bayan ya mutu. A warƙar, ya bayyana cewa ba a haife mu da rai marar mutuwa ba kamar yadda ake koyarwa a yawancin coci. A maimakon haka, rai marar mutuwa kyauta ce daga wurin Allah. A 1837, wani limami mai suna George Storrs ya sami kofi na warƙar yayin da yake tafiya a cikin jirgin ƙasa. Ya karanta warƙar kuma ya amince cewa abin da ya koya gaskiya ne. Sai ya soma gaya ma wasu abin da ya koya. A 1842, ya ba da jerin jawabai mai jigo “An Inquiry—Are the Wicked Immortal?” wato, mugayen mutane suna da rai marar mutuwa ne? Abin da George Storrs ya rubuta ya burge wani matashi mai suna Charles Taze Russell.

14. Ta yaya Ɗanꞌuwa Russell da abokansa suka amfana daga shirye-shirye da aka yi kafin lokacinsu? (Ka kuma duba hoton.)

14 Ta yaya shirye-shirye da mutanen nan suka yi ya taimaka wa Ɗanꞌuwa Russell da abokansa? Da suke bincike, sun yi amfani da littattafai da ke bayyana maꞌanar kalmomi, da na muhimman kalmomi da inda aka yi amfani da su a Littafi Mai Tsarki, da kuma fassarar Littafi Mai Tsarki da mutanen nan suka yi kafin su. Sun kuma amfana daga bincike da mutane kamar Henry Grew da George Storrs da ma wasu suka yi game da Littafi Mai Tsarki. Ɗanꞌuwa Russell da abokansa ma sun taimaka wajen shirya hanyar. Sun yi hakan ta wajen wallafa littattafai da warƙoƙi da suka bayyana abin da Littafi Mai Tsarki ya koyar.

15. Wane abu mai muhimmanci ne ya faru a shekara ta 1919?

15 A shekara ta 1919, bayin Jehobah sun sami ꞌyanci daga Babila Babba. A shekarar nan, “bawan nan mai aminci, mai hikima” ya soma aiki sosai domin mutane su soma yin tafiya a “Hanyar Tsarki.” (Mat. 24:​45-47) Saboda aikin da bayin Allah a dā suka yi don su shirya hanyar, waɗanda suka soma tafiya a hanyar sun koyi abubuwa da yawa game da Jehobah da kuma nufinsa. (K. Mag. 4:18) Kuma za su iya soma yin rayuwa da ta jitu da nufinsa. Jehobah bai bukaci mutanensa su yi canje-canjen da suke bukata farat ɗaya ba. A maimakon haka, ya ci gaba da kyautata halayen mutanensa a-hankali-a-hankali. (Ka duba akwatin nan “ A Hankali, Jehobah Ya ꞌYantar da Bayinsa Daga Bauta ta Ƙarya.”) Hakika, idan lokacin da za mu iya faranta wa Allah rai a dukan abubuwan da muke yi ya zo, za mu yi farin ciki sosai!​—Kol. 1:10.

HAR YANZU “HANYAR TSARKI” TANA A BUƊE

16. Tun daga 1919, waɗanne gyare-gyare ne aka ci gaba da yi a “Hanyar Tsarki”? (Ishaya 48:17; 60:17)

16 Kowace hanya tana bukatar gyara a-kai-a-kai. Tun daga 1919, an ci gaba da yin aiki a “Hanyar Tsarki” domin a taimaka wa mutane da yawa su iya barin Babila Babba. Bawan nan mai aminci mai hikima da aka naɗa ya soma aiki nan take. Kuma a shekara ta 1921, ya wallafa littafin da ke bayyana Littafi Mai Tsarki don ya taimaka ma waɗanda suka soma koyan gaskiyar Littafi Mai Tsarki. Sunan littafin shi ne, The Harp of God. An rarraba kusan kofi miliyan shida na littafin a harsuna 36, kuma mutane da yawa sun koyi gaskiya daga littafin. A kwanan nan, an samar mana littafi mai kyau da muke amfani da shi mu yi nazari da mutane, wato Ka Ji Daɗin Rayuwa Har Abada! A wannan kwanakin ƙarshe, Jehobah yana amfani da ƙungiyarsa don ya tanada mana abubuwan da za su taimaka mana mu ci gaba da yin tafiya a “Hanyar Tsarki.”​—Karanta Ishaya 48:17; 60:17.

17-18. Ina ne “Hanyar Tsarki” za ta kai mu?

17 Za mu iya ce a duk lokacin da mutum ya yarda a yi nazarin Littafi Mai Tsarki da shi, ya sami damar yin tafiya a “Hanyar Tsarki” ke nan. Wasu idan suka soma tafiya a hanyar, sai su daina daga baya. Wasu kuma sun ƙudiri niyyar yin tafiya a hanyar har sai sun kai inda za su. Ina ne za su?

18 Ga shafaffu, hanyar za ta kai su ga yin rayuwa a cikin aljannar Allah a sama. (R. Yar. 2:7) Waɗanda za su yi rayuwa har abada a duniya kuma, hanyar za ta kai su ga zama kamilai bayan Sarautar Yesu na Shekara 1000. Idan kana tafiya a wannan hanyar a yau, kada ka juya baya, kuma kada ka bar hanyar har sai ka kai inda za ka, wato sabuwar duniya! Muna fatan za ka sauka lafiya.

WAƘA TA 24 Ku Zo Tudun Jehobah

a Jehobah ya kira hanyar da ta taso daga Babila zuwa Israꞌila “Hanyar Tsarki.” Shin Jehobah ya shirya wa mutanensa hanya a zamaninmu? Ƙwarai kuwa! Tun daga shekara ta 1919, miliyoyin mutane sun bar Babila Babba kuma sun soma tafiya a “Hanyar Tsarki.” Dukanmu muna bukatar mu ci gaba da yin tafiya a hanyar har sai mun kai inda za mu.

c BAYANI A KAN HOTO: Ɗanꞌuwa Russell da abokansa sun yi amfani da littattafai da ke bayyana Littafi Mai Tsarki da aka shirya kafin lokacinsu.