Koma ka ga abin da ke ciki

Koma ga abubuwan da ke ciki

Sun Yi Farin Cikin Saukaka Rayuwarsu

Sun Yi Farin Cikin Saukaka Rayuwarsu

DANIEL DA MIRIAM sun yi aure a watan Satumba a shekara ta 2000 kuma suka zauna a birnin Barcelona da ke ƙasar Sifen. Daniel ya ce: “Muna jin daɗin rayuwarmu, don muna yin aikin da muke samun albashi mai tsoka, muna cin abinci a gidan abinci masu kyau, mu yi tafiya zuwa wata ƙasa kuma muna saka kaya masu tsada. Ƙari ga haka, muna fita wa’azi a kai a kai.” Amma sai muka yi wani canji a rayuwarmu.

A wani taron da aka yi a shekara ta 2006, Daniel ya ji wani jawabi da aka yi wata tambaya: “Shin muna yin iya ƙoƙarinmu don mu taimaka ma waɗanda suke ‘kusa ga yanka’ su soma bin hanyar rai ta madawwami?” (Mis. 24:11) A jawabin an bayyana muhimmancin yi wa mutane wa’azi don hakan zai sa su sami rai na har abada. (A. M. 20:​26, 27) Daniel ya tuna cewa, sai “na ji kamar Jehobah yana yi min magana.” Mai jawabin ya faɗi cewa za mu fi yin farin ciki idan muka ƙara ƙwazo a hidimarmu ga Jehobah. Daniel ya san cewa hakan gaskiya ne. Miriam ta riga ta soma hidimar majagaba kuma tana farin ciki sosai.

Daniel ya ce, “Na ƙuduri aniya cewa lokaci ya yi da zan canja salon rayuwata.” Kuma ya yi hakan. Sai ya rage sa’o’in da yake yi yana aiki, kuma ya soma hidimar majagaba. Ƙari ga haka, ya yi tunanin yadda shi da matarsa za su riƙa farin ciki idan suka yi hidima a inda ake bukatar masu wa’azin Mulkin Allah sosai.

SUN SHA WAHALA KAFIN SU SAMI LABARI MAI DAƊI

A watan Mayu na shekara ta 2007, Daniel da Miriam suka yi murabus daga aikinsu kuma suka ƙaura zuwa ƙasar Panama da suka taɓa zuwa ziyara. A sabon yankin da suka koma, akwai yankuna da yawa da ke gaɓar teku a yankin Bocas del Toro da ke Tekun Caribbea kuma mutanen Guaymi ne suke zama a wurin. Daniel da Miriam suna ganin cewa ta wurin yin amfani da kuɗin da suka tara, za su iya zama a Panama wajen watanni takwas.

Suna tafiya zuwa waɗannan yankuna da kwalekwale da keke. Kuma sun tuna tafiya na farko da suka yi da keke, sun yi tafiya na kilomita 32 suna hawan tuddai sa’ad da ake rana mai zafi. Daniel ya kusan sumewa don gajiya, amma mutanen Guaymi sun marabce su da hannu bibbiyu, musamman ma bayan sun koyi wasu furuci a yarensu. Ba da daɗewa ba, suka soma yin nazarin Littafi Mai Tsarki da mutane 23.

Amma, ma’auratan sun yi baƙin ciki sosai sa’ad da kuɗinsu ya ƙare. Daniel ya ce: “Muna kuka, sa’ad da muka soma tunanin koma Sifen. Mun yi baƙin cikin barin ɗalibanmu.” Amma bayan wata guda, sun sami wani labari mai daɗi. Miriam ta ce: “An gaya mana mu soma hidimar majagaba ta musamman. Mun yi farin ciki da yake za mu ci gaba da hidimarmu a wurin!”

ABIN DA YA FI SA SU FARIN CIKI

Domin canje-canje da aka yi a ƙungiyar Jehobah, Daniel da Miriam sun daina hidimar majagaba ta musamman kuma aka ce su ci gaba da hidimar majagaba ta kullum. Mene ne za su yi? Sun dogara ga alkawarin da ke Zabura 37:5: “Ka danƙa wa Ubangiji tafarkinka; ka dogara gare shi, shi kuma za ya tabbatar da shi.” Sun sami aiki da ke taimaka musu su kula da kansu a hidimarsu. A yanzu, suna hidima a ikilisiya da ke yankin Veraguas a ƙasar Panama.

Daniel ya ce: “Kafin mu bar Sifen, ba mu san ko za mu iya sauƙaƙa rayuwarmu ba. A yanzu mun yi hakan, kuma ba ma rasa wani abu mai muhimmanci.” Mene ne ya fi sa su farin ciki? Sun ce, “Taimaka wa mutane su koya game da Jehobah ne yake sa mu farin ciki sosai!”