Koma ka ga abin da ke ciki

Koma ga abubuwan da ke ciki

Ka Bauta wa Jehobah Cikin Natsuwa

Ka Bauta wa Jehobah Cikin Natsuwa

“Maryamu, . . . tana jin maganar [Yesu]. Amma Martha ta damu saboda yawan hidima.””LUKA 10:39, 40.

WAƘOƘI: 94, 134

1, 2. Me ya sa Yesu ya ƙaunaci Martha, amma me ya nuna cewa ita ajiza ce?

WANE irin hali ne kake ganin Martha da aka ambata a cikin Littafi Mai Tsarki take da shi? Ko da yake ita kaɗai ce Yesu ya ambaci sunanta kuma ya ce yana ƙaunarta, amma ya ƙaunaci wasu mata masu bauta wa Allah kamar mahaifiyarsa Maryamu, da ’yar’uwar Martha, Maryamu. (Yoh. 11:5; 19:25-27) Shin me ya sa Littafi Mai Tsarki ya ce Yesu ya ƙaunaci Martha?

2 Yesu ya ƙaunaci Martha don ita mai karɓan baƙi ne kuma tana da ƙwazo. Ƙari ga haka, tana da dangantaka mai kyau da Allah. Martha ta gaskata da koyarwar Yesu sosai kuma ta ba da gaskiya cewa shi ne Almasihu. (Yoh. 11:21-27) Duk da haka, ita ajiza ce kamar mu. Wani lokacin da Yesu ya sauka a gidansu, Martha ta tambayi Yesu ya daidaita wani yanayin da take gani bai dace ba. Ta ce: “Ubangiji, ko ba ka kula ba ’yar’uwata ta bar ni in yi hidima ni kaɗai? Sai ka ce mata ta taimake ni.” (Karanta Luka 10:38-42.) Wane darasi ne za mu iya koya daga wannan labarin?

HIDIMOMI SUN RABA HANKALIN MARTHA

3, 4. Ta yaya Maryamu ta zaɓi “rabo mai kyau,” kuma wane darasi ne Martha ta koya? (Ka duba hoton da ke shafi na 18.)

3 Yesu ya ji daɗi da Martha da Maryamu suka gayyace shi zuwa gidansu, sai ya soma koya musu gaskiya game da Allah. Da yake Maryamu ta so ta ƙara sanin gaskiyar da Yesu yake koyarwa, sai ta “zauna a wurin ƙafafun Ubangiji, tana jin maganarsa.” Da a ce Martha ta zauna kuma ta saurari Yesu, da Yesu ya yabe ta.

4 Amma, Martha ta shagala tana shirya abinci na musamman don Yesu ya ci kuma ya ji daɗin ziyarar. Saboda haka, yawan aiki ya sa ta soma damuwa ainun kuma ta soma fushi da Maryamu. Yesu ya lura cewa Martha ta saka hidimomi da yawa a gabanta. Saboda haka, sai ya ce: “Martha, Martha, kin damu, kina wahala kuma a kan abubuwa da yawa.” Sai ya ce abinci daidai gwargwado zai wadatar. Ya mai da hankali ga Maryamu kuma ya ce: “Maryamu ta zaɓi rabo mai-kyau, ba kuwa za a amshe mata ba.” Wataƙila Maryamu ta manta da abincin da ta ci a lokacin, amma ba za ta manta da koyarwa da Yesu ya yi a ranar da kuma yadda ya yabe ta ba. Sama da shekaru 60 bayan haka, manzo Yohanna ya ce: “Yesu dai yana ƙaunar Martha, da ’yar’uwarta.” (Yoh. 11:5) Waɗannan kalmomin sun nuna cewa Martha ta karɓi shawarar da Yesu ya ba ta kuma ta bauta wa Jehobah har mutuwarta.

5. Me ya sa mai da hankali ga abin da ya fi muhimmanci yake da wuya a yau, kuma wace tambaya ce za mu tattauna?

5 A zamaninmu, akwai abubuwa da yawa masu raba hankali fiye da a zamanin Yesu. Sama da shekaru 60 da suka shige, wasu rukunin ɗalibai a Amirka sun ce: “An sami ci gaba sosai a sadarwa da buga littattafai da tsara littattafai masu kyau da rediyo da silima da kuma talabijin. . . . Waɗannan abubuwa suna raba mana hankali kowace rana . . . A dā, mutane suna farin ciki cewa zamaninmu zamanin waye kai ne. Amma zamanin raba hankali ne kuma hakan yana daɗa muni da shigewar lokaci.” An rubuta a Hasumiyar Tsaro ta 15 ga Satumba 1958 cewa: “Abubuwa masu raba hankali . . . za su ƙaru yayin da ƙarshen duniya take gabatowa.” Hakan gaskiya ne! Saboda haka, yana da muhimmanci mu tattauna wannan tambayar: Mene ne za mu iya yi don mu rage abubuwa masu raba hankali kuma mu mai da hankali ga abubuwan da za su ƙarfafa dangantakarmu da Jehobah, kamar yadda Maryamu ta yi?

KADA KA BIƊI ABUBUWAN DUNIYA DA DUKAN ƘARFINKA

6. A waɗanne hanyoyi ne ƙungiyar Jehobah ta yi amfani da fasaha don yaɗa bishara?

6 Ƙungiyar Jehobah tana amfani da fasaha a kowane lokaci don yaɗa bishara. Alal misali, an yi amfani da Photo-Drama of Creation(Majigi mai ɗauke da hotuna da kuma sauti) wajen yi wa mutane bishara. Ƙari ga haka, a ƙarshen fim ɗin an kwatanta yadda sarautar Yesu Kristi na shekara dubu za ta kasance. Miliyoyin mutane sun sami ƙarfafa ta wurin kallon wannan shirin kafin a soma Yaƙin Duniya na ɗaya da kuma a lokacin da ake yaƙin. Daga baya an yi wa’azin bishara ta rediyo kuma miliyoyin mutane a faɗin duniya sun ji saƙon. A yau, ana amfani da fasahar kwamfuta da kuma Intane sosai wajen yaɗa bishara kuma mutane da ke zama a tsibirai masu nisa da kuma ko’ina a faɗin duniya suna samun damar sauraron bishara.

Kada ka bar abubuwan da ba su da muhimmanci su shafi bautarka ga Jehobah (Ka duba sakin layi na 7)

7. (a) Me ya sa yawan biɗan abubuwan duniya yake da lahani? (b) Mene ne ya kamata ya fi kasancewa da muhimmanci a gare mu? (Ka duba ƙarin bayani.)

7 Kamar yadda Littafi Mai Tsarki ya yi mana gargaɗi, yawan morar duniya yana da haɗari. (Karanta 1 Korintiyawa 7:29-31.) Kirista yana iya ɓata lokacinsa a kan abubuwan da ba a haramta ba, kamar yin abubuwan da muke so ko karatu ko kallon talabijin ko yawon shakatawa ko sayayya da biɗan fasaha ko alatu na zamani. Ƙari ga haka, dandalin sadarwa na Intane ko aika saƙoni ta waya ko imel da karanta labarai da kuma wasanni za su iya zama mana jaraba. * (M. Wa. 3:1, 6) Idan ba mu rage lokacin da muke waɗannan abubuwa da ba su muhimmanci ba, hakan zai iya sa mu bar abubuwa mafi muhimmanci, wato bautarmu ga Jehobah.—Karanta Afisawa 5:15-17.

8. Me ya sa yake da muhimmanci mu guji yin sha’awar abubuwan duniya?

8 Shaiɗan yana yin amfani da abubuwan duniya ya janye hankalinmu don mu daina bauta wa Jehobah. Ya yi hakan a ƙarni na farko kuma abin da yake yi a yau ke nan. (2 Tim. 4:10) Saboda haka, ya kamata mu bi wannan shawarar da ta ce: “Kada ku yi ƙaunar . . . abubuwan da ke cikin duniya.” Idan muka ci gaba da daidaita rayuwarmu don mu bi wannan shawarar, abubuwan duniya ba za su iya raba hankalinmu ba kuma za mu kasance da dangantaka ta kud da kud da Jehobah. Hakan zai taimaka mana mu yi nufin Allah kuma mu kasance cikin waɗanda ya amince da su har abada.—1 Yoh. 2:15-17.

KA MAI DA HANKALI GA ABUBUWA MAFI MUHIMMANCI

9. Mene ne Yesu ya koya wa almajiransa su saka kan gaba, kuma ta yaya ya kafa misali mai kyau a wannan fannin?

9 Shawarar da Yesu ya ba Martha cikin sanin yakamata ta jitu da koyarwarsa da kuma rayuwarsa. Yesu ya ƙarfafa almajiransa su mai da hankali “sarai” ga bauta wa Jehobah da kuma yin wa’azin bisharar Mulki. (Karanta Matta 6:22, 33.) Yesu ya kafa misali mai kyau a wannan fannin. Bai biɗi abin duniya ba kuma bai mallaki gida ko fili ba.—Luk. 9:58; 19:33-35.

10. Wane misali mai kyau ne Yesu ya kafa mana?

10 Yesu bai yarda wani abu ya ɗauke hankalinsa daga wa’azin bishara ba. Alal misali, bayan ya koyar da mutane kuma ya yi mu’ujizai a Kafarnahum, mutanen sun roƙe shi kada ya bar birninsu. Amma mene ne Yesu ya yi? Ya ce: “Dole in kai bishara ta Mulkin Allah ga sauran birane kuma: gama saboda wannan aka aiko ni.” (Luk. 4:42-44) Yesu ya je wurare dabam-dabam don yin wa’azi da kuma koyar da mutane. Ko da yake shi kamili ne, a wani lokaci yakan gaji sosai don yadda ya ba da kansa a yin nufin Allah.—Luk. 8:23; Yoh. 4:6.

11. Mene ne Yesu ya gaya wa wani mutum da ke gardama a iyalinsu kuma wane gargaɗi ne Yesu ya bayar?

11 Daga baya, sa’ad da yake koyar da mabiyansa yadda za su bi da hamayya, wani mutum ya katse masa magana kuma ya ce: “Malam, ka ce ma ɗan’uwana shi raba gadō da ni.” Amma Yesu ya ƙi ya saka baki a gardamar. Ya amsa cewa: “Mutum, wanne ya sanya ni alƙali ko mai raba musu a bisanku?” Bayan haka, sai Yesu ya ci gaba da koyar da mabiyansa. Ƙari ga haka, ya yi amfani da zarafin don ya yi wa masu sauraronsa gargaɗi a kan hadarin da ke tattare da biɗan abin duniya don hakan zai iya sa mu yi sanyin gwiwa a ibadarmu ga Jehobah.—Luk. 12:13-15.

12, 13. (a) Mene ne ya burge wasu Helenawa jim kaɗan kafin mutuwar Yesu? (b) Ta yaya Yesu ya bi da wannan yanayi da zai iya raba hankalinsa?

12 Yesu ya damu sosai a kwanakinsa na ƙarshe a duniya. (Mat. 26:38; Yoh. 12:27) Yana da aiki da yawa a gabansa, kuma ya san cewa za a azabtar da shi kuma a kashe shi. Alal misali, a ranar Lahadi ta 9 ga Nisan a shekara ta 33, Yesu ya shiga cikin Urushalima a kan ɗan jaki kamar yadda aka annabta kuma mutane sun yabe shi suna cewa: “Mai albarka ne Sarki mai zuwa cikin sunan Ubangiji.” (Luk. 19:38) Washegari, Yesu ya shiga cikin haikali kuma ya watsar da ’yan kasuwa masu haɗama don suna cutar ’yan’uwansu Yahudawa.—Luk. 19:45, 46.

13 Wasu Helenawa mabiyan addinin Yahudawa da suka je Urushalima don Idin Ƙetarewa sun shaida abubuwan da Yesu ya yi kuma hakan ya burge su. Saboda haka, suka gaya wa manzo Filibus cewa suna son su haɗu da Yesu. Amma da yake Yesu ba ya neman magoya baya da za su kāre shi daga magabtansa, bai bar hakan ya ɗauke hankalinsa daga abubuwan da suka fi muhimmanci ba. Saboda haka, bayan ya bayyana cewa zai mutu ba da daɗewa ba, sai ya gaya wa Andarawus da Filibus cewa: “Mai-son ransa yana ɓatar da shi ke nan: shi kuwa wanda yana ƙin ransa a wannan duniya, za ya riƙe shi zuwa rai na har abada.” A maimakon ya yi abin da zai burge waɗannan Helenawa, ya ba da wannan shawara: “Idan kowane mutum ya yi mini barantaka, Uban zai ba wannan mutum girma.” Babu shakka, wannan saƙo ne mai ban ƙarfafa kuma Filibus ya kai wannan saƙon ga Helenawan.—Yoh. 12:20-26.

14. Ko da yake Yesu ya saka wa’azin bishara farko a rayuwarsa, me ya nuna cewa ya kasance da ra’ayin da ya dace?

14 Ko da yake Yesu bai yarda wani abu ya raba hankalinsa daga wa’azin bishara ba, hakan ba ya nufin cewa ba ya shaƙatawa. Ya je bikin aure aƙalla sau ɗaya, har ya mai da ruwa zuwa ruwan inabi kuma hakan ya taimaka a wurin bikin. (Yoh. 2:2, 6-10) Ƙari ga haka, ya ci abincin yamma tare da abokai na kud da kud da kuma waɗanda suka zama almajiransa. (Luk. 5:29; Yoh. 12:2) Mafi muhimmanci, Yesu ya keɓe lokaci don yin addu’a da bimbini da kuma hutu.—Mat. 14:23; Mar. 1:35; 6:31, 32.

KA SAUKE DUKAN ABUBUWA MASU ‘NAUYI’

15. Wace shawara ce manzo Bulus ya bayar, kuma ta yaya ya kafa misali mai kyau?

15 Manzo Bulus ya ce Kiristoci suna kamar masu tsere kuma ya ce: “Mu tuɓe kowane abin nauwaitawa.” (Karanta Ibraniyawa 12:1.) Hakika, Bulus ya kafa misali mai kyau don ya yi watsi da damar zama mai kuɗi da kuma iko a matsayinsa shugaban addinin Yahudawa. Ya mai da hankali ga “mafifitan al’amura” kuma ya yi wa’azin bishara da ƙwazo a wurare dabam-dabam kamar Suriya da Asiya Ƙarami da Makidoniya da kuma Yahudiya. Ya ce: “Ina manta da abubuwan da ke baya, ina kutsawa zuwa ga waɗanda ke gaba.” (Filib. 1:10; 3:8, 13, 14) Bulus ya yi amfani da yanayinsa na marasa aure don ya “yi hidimar Ubangiji ba da raba hankali ba.”—1 Kor. 7:32-35.

16, 17. Ko da muna da aure ko ba mu da shi, ta yaya za mu iya bin misalin da Bulus ya kafa? Ta yaya Mark da Claire suka yi hakan?

16 Wasu bayin Jehobah sun bi misali mai kyau da Bulus ya kafa. Sun tsai da shawara cewa ba za su yi aure ba don su ƙara ƙwazo a bautarsu ga Jehobah. (Mat. 19:11, 12) Ma’aurata sukan kasance da hidimomin iyali da yawa. Amma ko da muna da aure ko ba mu da aure, dukanmu za mu iya sauke kowane abu mai ‘nauyi’ kuma mu bauta wa Allah cikin natsuwa. Hakan yana nufin cewa za mu rage wasu abubuwan da suke ɓata lokacinmu kuma mu kafa maƙasudai da za su ba mu damar ƙara ƙwazo a hidimarmu ga Allah.

17 Ka yi la’akari da wasu ma’aurata masu suna Mark da Claire daga Wales. Kafin su yi aure, kowannensu ya soma hidimar majagaba bayan ya sauke karatun makarantar sakandare. Bayan sun yi aure, suka ci gaba da hidimar majagaba. Mark ya ce: “Mun ƙara sauƙaƙa rayuwarmu sa’ad da muka sayar da babban gidanmu kuma muka daina aikin da muke yi don mu soma hidimar gine-gine a ƙasashe dabam-dabam.” Sun yi shekaru 20 suna zuwa ƙasashe dabam-dabam a Afirka don gina Majami’un Mulki. Akwai lokacin da kuɗin da suke da shi ya rage dala 15 kawai, amma Jehobah ya kula da su. Matarsa Claire ta ce: “Bauta wa Jehobah kowace rana tana sa mu farin ciki sosai. Mun sami abokai da yawa kuma ba mu rasa kome ba. Ba za mu iya kwatanta farin cikin da muke yi yanzu da sadaukarwa da muka yi don mu bauta wa Jehobah ta yin hidima ta cikakken lokaci ba.” Bayin Jehobah da yawa sun shaida hakan. *

18. Wace tambaya ce ya kamata mu yi la’akari a kai?

18 Kai kuma fa? Mene ne za ka yi idan ka lura cewa ka daina bauta wa Jehobah da ƙwazo kamar yadda ka yi a dā saboda wasu abubuwa masu raba hankali? Wataƙila kyautata karatu da kuma nazarin Littafi Mai Tsarki zai taimaka maka. Ta yaya za ka yi hakan? Za a bayyana a talifi na gaba.

^ sakin layi na 17 Za ka iya karanta labarin Hadyn Sanderson da matarsa Melody a wani talifin Hasumiyar Tsaro ta 1 ga Maris, 2006, mai jigo: Knowing What Is Right and Doing It.” Sun daina sana’arsu a ƙasar Ostareliya kuma suka soma hidima ta cikakken lokaci. Ka karanta don ka san abin da ya faru sa’ad da kuɗinsu ya ƙare yayin da suke hidima a matsayinsu na masu wa’azi a ƙasar waje a Indiya.