Koma ka ga abin da ke ciki

Koma ga abubuwan da ke ciki

 AMSOSHIN TAMBAYOYI DAGA LITTAFI MAI TSARKI

Amsoshin Tambayoyi Daga Littafi Mai Tsarki

Mene ne sunan Allah?

Mambobin iyalinmu duka suna da sunaye. Shin, bai kamata Allah ma ya kasance da suna ba? Littafi Mai Tsarki ya nuna cewa Allah yana da laƙabi da yawa. Wasu daga cikin laƙabin Allah su ne, Allah Maɗaukakin Sarki, Mamallakin sama da ƙasa da kuma Mahalicci. Amma Allah yana da suna na musamman.—Ka karanta Fitowa 6:3.

A cikin juyin Littafi Mai Tsarki da yawa, an ambaci sunan Allah a Zabura 83:18. Alal misali, a juyin da aka yi amfani da shi a wannan talifin, ayar ta ce: “Kai, wanda sunanka Jehovah ne, kai kaɗai ne Maɗaukaki bisa dukan duniya.”

Me ya sa ya kamata mu yi amfani da sunan Allah?

Allah yana son mu yi amfani da sunansa. Mukan kira ’yan’uwanmu da abokanmu da sunayensu. Shin, bai kamata mu yi amfani da sunan Allah sa’ad da muke masa addu’a ba? Ƙari ga haka, Yesu Kristi ya ɗaukaka sunan Allah kuma ya ce mu yi amfani da shi.—Ka karanta Matta 6:9; Yohanna 17:26.

Mukan kira ’yan’uwanmu da abokanmu da sunayensu

Duk da haka, idan muna son mu zama aminan Allah, ya kamata mu san shi sosai ba sunansa kawai ba. Akwai tambayoyin da fahimtar amsoshinsu zai taimaka mana mu san shi sosai. Alal misali: Wane irin hali ne Allah yake da shi? Za mu iya kusantar Allah kuwa? Za ka sami amsoshin waɗannan tambayoyin a cikin Littafi Mai Tsarki.