Koma ka ga abin da ke ciki

Koma ga abubuwan da ke ciki

ABIN DA KE SHAFIN FARKO | ZA KA IYA KUSANTAR ALLAH

Ka San Sunan Allah Kuma Kana Amfani da Shi Kuwa?

Ka San Sunan Allah Kuma Kana Amfani da Shi Kuwa?

Shin kana da wani aboki da ba ka san sunansa ba? Da kyar. Wata mata mai suna Irina daga ƙasar Bulgeriya ta ce, “Ba zai yiwu ka kusaci Allah ba idan ba ka san sunansa ba.” Abin farin ciki ne cewa Allah yana so ka kusace shi, kamar yadda aka ambata a talifin baya. Saboda haka, Allah yana amfani da Littafi Mai Tsarki don ya gabatar da kansa a gare ka, ta wajen cewa: “Ni ne Jehobah. Sunana ke nan.”—Ishaya 42:8, New World Translation.

Allah yana amfani da Littafi Mai Tsarki don ya gabatar da kansa a gare ka, ta wajen cewa: “Ni ne Jehobah. Sunana ke nan.”—Ishaya 42:8, NW

Shin sanin sunan Allah da kuma yin amfani da shi yana da wani muhimmanci a gare shi kuwa? Ka yi la’akari da wannan: Sunan Allah da aka rubuta da baƙaƙe huɗu na Ibrananci ya bayyana a Nassosin Ibrananci na asali kusan sau 7,000. Babu wani suna da aka ambata sau da yawa haka a cikin Littafi Mai Tsarki. Hakika, wannan tabbaci ne cewa Jehobah yana so mu san sunansa kuma mu yi amfani da shi. *

Abokantaka tsakanin mutane biyu takan soma ne bayan sun san sunayen juna. Ka san sunan Allah kuwa?

Wasu suna iya ji kamar rashin kunya ne a yi amfani da sunan Allah, domin Allah yana da tsarki kuma shi ne maɗaukaki. Hakika, ba zai dace a yi saɓo da sunan Allah ba, kamar yadda ba za ka yi hakan da sunan abokinka ba. Amma, Jehobah yana so waɗanda suke ƙaunarsa su girmama sunansa kuma su sanar da shi. (Zabura 69:30, 31; 96:2, 8) Ka tuna cewa Yesu ya koya wa mabiyansa su yi addu’a haka: “Ubanmu wanda ke cikin sama, a tsarkake sunanka.” Mu ma za mu iya taimaka wajen tsarkake sunan Allah da kuma sanar da shi. Yin hakan zai sa mu kusace shi.—Matta 6:9.

Littafi Mai Tsarki ya nuna cewa Allah yana mai da hankali ga waɗanda suke daraja ko kuma “tunawa da sunansa.” (Malakai 3:16) Jehobah ya yi wa waɗanda suke yin hakan alkawari cewa: ‘Zan tsamar da shi, zan ɗaukaka shi, domin ya san sunana. Za shi kira bisa gare ni, ni kuma zan amsa masa; a cikin ƙunci ina tare da shi.’ (Zabura 91:14, 15) Idan muna so mu kasance da dangantaka ta kud-da-kud da Allah, wajibi ne mu san sunansa kuma mu yi amfani da shi.

^ sakin layi na 4 Abin taƙaici, mafassaran Littafi Mai Tsarki da yawa ba su yi amfani da sunan Allah ba duk da cewa sunan ya bayyana sau da yawa a cikin Nassosin Ibrananci, wato Tsohon Alkawari. Akasin haka, sun sauya sunan Allah da laƙabi kamar su “Ubangiji” da kuma “Allah.” Don ƙarin bayani a kan wannan batun, ka duba littafin nan Menene Ainihi Littafi Mai Tsarki Yake Koyarwa?, shafuffuka na 195-197. Shaidun Jehobah ne suka wallafa.