Koma ka ga abin da ke ciki

Koma ga abubuwan da ke ciki

DAGA TARIHINMU

Sun Yi Iya Kokarinsu

Sun Yi Iya Kokarinsu

 A karshen Yakin Duniya na 2 a 1945, an lalata abubuwa da yawa a Jamus. An hallaka birane, an lalata makarantu da asibitoci kuma an bar su bam da ba su fashe ba a ko’ina. An yi karancin abinci kuma hakan ya sa farashinsa ya haura. Alal misali, farashin rabin kilo na dunkulen man shanu ya kai kudin albashin makonni shida!

 Wannan yanayin ya shafi darurruwan Shaidun Jehobah da suka yi shekaru a kurkuku da kuma sansanoni dabam-dabam saboda imaninsu. A 1945 sa’ad da aka sake su, an bar su da rigunan da ke jikinsu ne kadai. Wasu shaidu kuma sun yi hasarar dukiyoyinsu da kayayyakinsu. Tsananin yunwa yakan sa wasu daga cikin su su sume sa’ad da ake taron ikilisiya.

Shaidun Jehobah Daga Wasu Kasashe Sun Taimaka Nan da Nan

 Jehobah daga wasu kasashe sun taimaka da abinci da kuma kayan sakawa nan da nan. Hukumar da Ke Kula da Ayyukanmu a hedkwata sun gaya wa ’yan’uwa a ofishinmu da ke Bern, a Switzerland cewa su taimaka ma ’yan’uwansu a Jamus. Nathan H. Knorr, wakilin hedkwarmu ya ziyarci Turai don ya taimaka a hanzarta aikin ba da agajin.

Dan’uwa Nathan H. Knorr yana ba ’yan’uwa jawabi a birnin Wiesbaden, a Jamus a 1947. Ta saman kansa an rubuta jigon shekarar a kan allo a Jamusanci da ta ce: “Praise Jehovah, All Nations” (“Ku Yabi Jehobah, Ya Ku Dukan Al’ummai”)

 Shaidun Jehobah a Switzerland sun taimaka wajen ba da abinci da kayayyakin sakawa da kuma kudi hannu a sake. An fara aika kayayyakin zuwa Bern inda aka zabi masu kyau daga cikin kayayyakin kafin aka tura su Jamus. Shaidun Jehobah a wasu kasashe kamar Sweden, da Kanada, da Amirka ma sun taimaka da ba da agaji. Ba ’yan’uwanmu a Jamus ne kadai suka amfana daga hakan ba, har da ’yan’uwa a Turai da Asiya inda yakin ya shafe su.

Sakamako Mai Kyau da Aka Samu

 A cikin ’yan watanni kawai, ofishinmu da ke Switzerland sun tura shayin kofi da madara da sukari da hatsi da busassun ’ya’yan itatuwa da kayan lambu da nama da kuma kifin gwangwani. Sun kuma ba da kudade.

 Kari ga haka, Shaidun Jehobah a Switzerland sun ba da kayayyakin da nauyinsu ya wuce kilo 4500 kuma kayayyakin sun hada da dogayen rigunan sanyi da rigunan mata da kwat na maza. A cikin Hasumiyar Tsaro ta 15 ga Janairu, 1946 a Turanci, an rubuto cewa: “’Yan’uwa masu bi sun bayar da abubuwa mafi kyau da suke da su. Sun yi sadaukarwa sosai don su taimaka ma ’yan’uwansu a Jamus.”

 ’Yan’uwa da ke Switzerland sun bayar da takalma kusan 1000, kuma an dudduba takalman don a tabbata cewa ba su yage ba kafin aka aika. ’Yan’uwa a birnin Wiesbaden, a Jamus da suka saukar da kayayyakin sun yi mamakin ingancin kayayyakin da yadda aka bayar da su iri-iri. Wani Mashaidi ya ce: “Na tabbata cewa babu wani kanti a Jamus da ke da kyawawan riguna da kuma takalma kamar wadannan.”

 An ci gaba da bayar da wannan agajin har sai Agusta na 1948. A karshe, Shaidun Jehobah da ke Switzerland sun aika wa ’yan’uwansu a Jamus kayan agajin a cikin akwatuna 444 da nauyinsu ya wuce kilo 22,679. Kamar yadda aka ambata dazu, ba Shaidun Jehobah da ke Switzerland ne kadai suka ba da agaji ba. Amma su ne mafi kankanta a cikin wadanda suka ba da agajin domin Shaidu 1,600 ne kawai suke kasar a lokacin!

Ku Yi “Ƙaunar Juna”

 Yesu Kristi ya ce: “Ta haka kowa zai sani ku almajiraina ne, in dai kuna ƙaunar juna.” (Yohanna 13:​34, 35) Kauna ta sa bayin Jehobah sun bayar da abubuwa mafi kyau da suke da su, ba abin da ba sa bukata ne suka bayar ba. (2 Korintiyawa 8:​1-4) A cikin wata wasikar daga birnin Zurich, an rubuto cewa: “’Yan’uwa masu bi da yawa da su kansu ma ba su da abubuwan biyan bukata sun ba da kudi don su taimaka.”

 Bayin Jehobah a Jamus sun farfado da wuri daga tsanantawa da kuma sakamakon yakin da suka fuskanta. Wani dalilin da ya sa hakan ya yiwu shi ne yadda ’yan’uwa masu bi suka nuna kauna da sadaukarwa ta wajen ba da agaji hannu sake da kuma yadda aka tsara aikin ba da agajin da kyau.

Shaidun Jehobah a ofishinmu da ke Bern, a Switzerland suna zaba da kuma shirya kayayyakin da aka bayar kafin su tura wa ’yan’uwansu a Jamus

Ana lodin akwatunan kayayyakin da aka tura zuwa ofishinmu da ke Bern

Wata mota cike da akwatunan da aka loda kuma a jikin motar an rubuta “Relief Program Jehovah’s Witnesses”

Ana sassaka akwatunan kayayyakin a cikin jirgin kasa don a kai Jamus