Koma ka ga abin da ke ciki

Koma ga abubuwan da ke ciki

Abin da Zai Taimaka wa Wadanda Ake Cin Zarafinsu a Gida

Abin da Zai Taimaka wa Wadanda Ake Cin Zarafinsu a Gida

 Hukumar Lafiya ta Duniya ta ce: “A duk duniya mutane suna cin zalin mata. Hakan ya zama kamar annobar da ta bazu ko’ina. Yana da muhimmanci a dauki mataki don a kowa karshensa.” Hukumar ta kuma ce kusan kashi 30 “na dukan matan da suke da miji ko saurayi, sun taba fuskantar cin zarafi daga mazajensu ko samarinsu.” Wani rahoto daga Majalisar Dinkin Duniya ya kimanta cewa a daya daga cikin shekarun baya-bayan nan, mata 137 sun mutu kowace rana sakamakon cin zarafi daga mazansu ko samarinsu ko kuma wani danginsu. a

 Rahotanni game da yadda ake cin zarafin mutane a gida zai iya nuna yadda matsalar ta yi kamari, amma ba zai iya bayyana irin zafi da kuma bakin cikin da wadanda ake cin zarafinsu suke fama da shi ba.

 Ana cin zarafinki a gida? Ko kin san wata da ake cin zarafinta? Idan haka ne, ga wasu abubuwan da Littafi Mai Tsarki ya fada da za su taimaka.

  Idan ana cin zarafinki, ba laifinki ba ne

  Za ki iya samun taimako

  Allah zai iya taimaka miki

  Za a daina cin zarafin mata

  Yadda za a iya taimaka wa wadda ake cin zarafinta

 Idan ana cin zarafinki, ba laifinki ba ne

 Abin da Littafi Mai Tsarki ya ce: “Kowane dayanmu zai ba da lissafin rayuwarsa ga Allah.”​—Romawa 14:12.

 Ki tuna cewa: Wanda yake cin zarafinki ne yake da laifi.

 Idan maigidanki ya ce ke ce kike sa ya ci zarafinki, wannan karya ne. Ya kamata a kaunaci mata ne ba wai a ci zarafinsu ba.​—Kolosiyawa 3:19.

 A wasu lokuta, matsalar kwakwalwa ko yawan shan giya ko yanayin iyalinsu ne ke sa wasu maza su dinga cin zarafin matansu. Duk da haka, Allah zai shari’anta shi don abin da yake miki. Kuma shi ne ya kamata ya yi iya kokarinsa ya canja halinsa.

 Za ki iya samun taimako

 Abin da Littafi Mai Tsarki ya ce: “Tare da shawara mai yawa, akwai cin nasara.”​—Karin Magana 15:22.

 Ki tuna cewa: Idan kina jin tsoro ko ba ki san abin da za ki yi ba, za ki iya samun taimako daga wasu mutane.

 Me ya sa kike bukatar taimako daga wurin wasu? Wadanda ake cin zarafinsu suna fama da tunani iri-iri. Zai iya miki wuya ki tsai da shawara domin kina tunanin ko wane batu ne za ki sa a kan gaba, batutuwa kamar:

  •   Lafiyarki

  •   Lafiyar yaranki

  •   Za ki iya biyan bukatun kanki?

  •   Yadda kike kaunar mijinki

  •   Mai yiwuwa kina so ku ci gaba da kasancewa tare idan ya canja halinsa

 Za ki iya rasa na yi kuma ki ji kamar ba ki da mafita. Wa zai iya taimaka miki?

 Wata abokiyarki ko danginki za ta iya taimaka miki kuma ta kwantar miki da hankali. Yin magana da wadda ta damu da ke kawai ma, zai iya sa ki ji sauki.

 Kiran lambobin neman taimakon gaggawa don wadanda ake cin zarafinsu a gida zai iya sa ki sami taimako nan da nan. Wadanda suke amsa kiran za su iya taimaka miki ki san abin da za ki yi don ki kāre kanki. Idan kuma maigidanki ya amince cewa yana bukatar a taimaka masa don ya canja halinsa, wadanda suke amsa kiran za su iya ba shi shawara a kan abin da zai yi.

 Wasu masu ba da taimakon gaggawa za su iya taimaka miki idan ranki na cikin hadari. Irin mutanen sun hada da likitoci da nas-nas da kuma wasu kwararru.

 Allah zai iya taimaka miki

 Abin da Littafi Mai Tsarki ya ce: “Ga wadanda an karya musu karfin gwiwa, Yahweh b yana kusa da su, yakan kubutar da masu fid da zuciya.”​—Zabura 34:18.

 Ki tuna cewa: Allah ya yi alkawarin taimaka miki.

 Jehobah ya damu da ke sosai. (1 Bitrus 5:7) Ya san abin da kike tunani da ainihin yadda kike ji. Zai iya karfafa ki ta wurin Kalmarsa Littafi Mai Tsarki. Yana so ki yi adda’u kuma ki gaya masa yadda kike ji. Yayin da kike addu’a, za ki iya rokonsa ya ba ki hikima da kuma karfin yin abin da zai taimaka miki.​—Ishaya 41:10.

 Za a daina cin zarafin mata

 Abin da Littafi Mai Tsarki ya ce: “Kowane mutum zai zauna cikin salama a karkashin itacen inabinsa da na baurensa. Ba wanda zai tsoratar da shi.”​—Mika 4:4.

 Ki tuna cewa: Littafi Mai Tsarki ya yi alkawari cewa lokaci na zuwa wanda kowa zai zauna lafiya a gidansa.

Jehobah ne kadai zai iya magance matsalolinmu gabaki daya. Kuma Littafi Mai Tsarki ya yi alkawari cewa: “Zai share musu dukan hawaye daga idanunsu. Babu sauran mutuwa, ko bakin ciki, ko kuka, ko azaba.” (Ru’uyar da Aka Yi wa Yohanna 21:4) A lokacin, ko tunanin munanan abubuwan da suka taba faruwa da mu za su bace, kuma tunanin abubuwa masu kyau ne za mu ta yi. (Ishaya 65:17) Abin da Allah ya miki alkawari cewa za ki iya samu ke nan.

a A talifin nan an ambata wadanda ake cin zarafinsu a matsayin mata, amma maza da ake cin zarafinsu ma za su iya amfana.

b Yahweh ko Jehobah shi ne sunan Allah a cikin Littafi Mai Tsarki.