Koma ka ga abin da ke ciki

Koma ga abubuwan da ke ciki

Wadanne Irin Hatimai Ne Ake Amfani da Su a Dā?

Wadanne Irin Hatimai Ne Ake Amfani da Su a Dā?

 Ana amfani da hatimai don a sa alama a kan abubuwa, akan yi amfani da tabo ko kuma danko. Siffar hatimi ya kan bambanta, akan yi shi a siffa iri iri kamar su silinda, har da sifar kan dabbobi. Alamar ta kan yi nuni ga mai hatimin ko kuma nuna tabbacin wani takarda, kuma za a iya yin amfani da shi a rufe bakin jaka ko kuma kofar wani wuri kamar kabari.

Hatimi na silinda ya nuna Darius na 1 yana farauta da kuma hatimi na laka

 Ana yin amfani da abubuwa kamar su kashi, da karfe, da duwatsu masu walkiya, ko kuma itace a yi hatimai da su. A wasu lokuta akan rubuta sunan mai hatimin da na babansa a kai. Akan rubuta lakabin mai hatimin a kai.

 Domin mutum ya nuna tabbacin wata takarda, mai hatimin zai buga rubutun hatimin a kan laka, ko tabo, ko kuma wani abu mai laushi akan takardar. (Ayuba 38:14) Abin da aka yi amfani da shi zai bushe, hakan zai sa takardun su dade kamar yadda ake so.

Za a Iya Ba Mutum Matsayi ta Wurin Hatimi

 Wani zai iya ba wani matsayinsa ta wurin ba mutumin hatiminsa. Alal misali, Fir’auna a Masar ta da ya ba Yusuf Ba-Ibrane dan Yakub hatiminsa. Yusuf bawa ne da a Masar. Daga baya an yi masa sharri, kuma an jefa shi cikin kurkuku. Daga baya, sai Fir’auna ya cire shi daga kurkuku kuma ya daukaka shi ya zama firayim minista. Littafi Mai Tsarki ya ce: “Sai Fir’auna ya cire zobensa mai hatimi daga yasarsa ya sa a yasar hannun Yusuf.” (Farawa 41:42) Domin zoben sarki yana dauke da hatimin ikon yin duk wani muhimman aiki, hakan ya ba Yusuf ikon yin duk wani aiki.

 Sarauniya Yezebel a Isra’ila ta da ta yi amfani da hatimin mijinta kuma ta kulla sharri a kashe Nabot. Ta yi amfani da sunan Sarki Ahab, kuma ta rubuta wa dattabai wasiku cewa su kulla wa Nabot sharri cewa ya zagi Allah. Ta buga hatimin sarkin a kan wasikun, hakan ya sa ta yi nassara a makircinta.​—1 Sarakuna 21:​5-14.

 Sarkin Fashiya Ahasuwerus ya yi amfani da zobensa mai hatimi don ya tabbatar wa jama’a da dokar da ya bayar.​—Esta 3:​10, 12.

 Marubucin Littafi Mai Tsarki Nehemiya ya ce yeriman Isra’ila, da Lawiyawa da kuma firistoci su kan hatimce duk wani rubutaccen abu don su nuna cewa sun amince da shi.​—Nehemiya 1:1; 9:38.

 Littafi Mai Tsarki ya ambaci lokuta biyu da aka yi amfani da hatimi don a rufe wuraren shiga. Lokacin da aka jefa annabi Daniyel a ramin zakuna, “sai aka kawo katon dutse aka rufe bakin ramin.” Sai Sarki Dariyus, wanda yake sarautar Mediya da Fasiya, “ya sa hatiminsa da na dattawansa a kai, domin kada a canja kome game da Daniyel.”​—Daniyel 6:17.

 Lokacin da aka saka jikin Yesu Kiristi a kabari, sai makiyansa su ka “tsare kabarin, suka buga hatimin sarki a dutsen kabarin” wanda aka sa domin ya rufe hanyar shiga. (Matiyu 27:66) Wani mai suna David L. Tuner da ya yi tafsirin Littafin Matiyu, ya ce: Idan hatimin na mulkin Romawa ne, to zai zama “an yi hatimin da laka ko kuma tabo aka kuma manne shi a tsakanin dutsen da ke kofar kabarin.”

 Hatimai za su iya bayyana mana abubuwan da suka faru a da, shi ya sa masu ilimin tona kasa da masu ilimin tarihi suke yin bincike akansu sosai. Hakazalika, ilimin sanin ma’anar hatimi ya zama shahararre a fannin ilimi, shi ya sa ake kiransa sigillography.