Koma ka ga abin da ke ciki

Koma ga abubuwan da ke ciki

Me Zai Taimake Ka Idan Ka Soma Rashin Lafiya Mai Tsanani Ba Zato?

Me Zai Taimake Ka Idan Ka Soma Rashin Lafiya Mai Tsanani Ba Zato?

 Ka soma rashin lafiya mai tsanani ba zato? Babu shaka ka gane cewa rashin lafiya yana sa mutum damuwa, yana gajiyar da shi, kuma jinya tana cin kudi sosai. Me zai taimaka maka ka iya jimre wannan yanayin? Me za ka iya yi don ka taimaka wa danginka ko abokinka da yake fama da rashin lafiya? Ko da yake Littafi Mai Tsarki ba littafin likitoci ba ne, ya ba da shawarwari da za su iya taimaka maka ka jimre yanayinka.

Abubuwan da za su taimaka maka idan kana rashin lafiya mai tsanani

  •   Ka je asibiti

     Abin da Littafi Mai Tsarki ya ce: “Masu lafiya ba sa bukatar likita, sai dai marasa lafiya.”​—Matiyu 9:12.

     Abin da hakan yake nufi: Ka nemi taimakon likita idan da bukata.

     Ga abin da za ka yi: Ka je wurin likitan da ya kware sosai a yankinku. A wasu lokuta, zai fi kyau ka je wurin likita fiye da daya. (Karin Magana 14:15) Ka bayyana ma likitan abin da ke damunka da kyau. Ka tabbata ya fahimci alamomin rashin lafiya da ke damunka, kuma kai ma ka tabbata ka fahimci bayaninsa. (Karin Magana 15:22) Ka yi bincike a kan rashin lafiyar da ire-iren jinya da za a iya yi maka. Idan ka fahimci yanayinka da kyau, za ka kasance a shirye kuma za ka iya tsai da shawarwari masu kyau.

  •   Ka kula da jikinka

     Abin da Littafi Mai Tsarki ya ce: “Wasa jiki tana da amfaninta.”​—1 Timoti 4:​8, Tsohuwar Hausa a Saukake.

     Abin da hakan yake nufi: Za ka amfana idan kana yin abubuwa da za su inganta lafiyar jikinka kamar motsa jiki a kai a kai.

     Ga abin da za ka yi: Ka rika motsa jikinka a kai a kai, ka ci abinci mai gina jiki kuma ka sami isasshen barci. Ko da yake ba ka saba da sabon yanayinka ba, masana sun ce za ka amfana sosai idan ka yi kokarin yin abubuwan da za su taimaka wa lafiyar jikinka. Amma ka tabbata cewa abin da za ka yi ba zai dada bata lamarin ba, kuma ba zai saba wa abin da likitanka ya fada ba.

  •   Ka nemi taimakon abokanka da danginka

     Abin da Littafi Mai Tsarki ya ce: “Abokin kirki yana nuna kauna a koyaushe kuma shi dan’uwa ne da ke ba da taimako a lokacin damuwa.”​—Karin Magana 17:​17, New World Translation.

     Abin da hakan yake nufi: Abokanka za su iya taimaka maka ka jimre yanayi mai wuya.

     Ga abin da za ka yi: Ka gaya wa amininka yadda kake ji. Hakan zai iya kwantar maka da hankali kuma zai taimake ka ka dada yin farin ciki. Mai yiwuwa danginka da abokanka suna so su taimaka maka amma ba su san yadda za su yi hakan ba. Don haka, ka gaya musu abin da za su iya yi don su taimaka maka. Kada ka dauka cewa za su yi maka kome da kome, kuma ka rika godiya don duk wani abin da suka yi maka. Ko da yake abokanka suna so su taimaka maka ne, zai dace ka gaya musu lokacin da za su rika zuwa, kuma idan suka zo, kada su rika dadewa sosai, don kar su hana ka samun isasshen hutu.

  •   Kar ka fid da rai

     Abin da Littafi Mai Tsarki ya ce: “Zuciya mai murna magani ne mai kyau, amma zuciya mai bakin ciki tana shanye karfin mutum.”​—Karin Magana 17:22.

     Abin da hakan yake nufi: Idan ka kasance da ra’ayi mai kyau kuma ka sa rai cewa abubuwa za su gyaru, hakan zai iya kwantar maka da hankali kuma ya ba ka karfin jimre rashin lafiyar.

     Ga abin da za ka yi: Yayin da kake fama da yanayinka, ka mai da hankali ga abin da za ka iya yi ba ga abin da ya fi karfin ka ba. Kada ka rika gwada kanka da sauran mutane, kuma kada ka rika gwada yadda kake yanzu da yadda kake kafin ka soma rashin lafiyar. (Galatiyawa 6:4) Idan kana shirya abubuwa da kake so ka yi, ka zabi abubuwan da suke daidai karfinka, hakan zai sa ka farin ciki. (Karin Magana 24:10) Ka rika taimaka wa mutane, daidai karfinka. Bayarwa tana sa mutum farin ciki, kuma zai sa ka rage damuwa a kan matsalolinka.​—Ayyukan Manzanni 20:35.

Shin Allah zai taimaka maka idan kana rashin lafiya?

 Littafi Mai Tsarki ya nuna cewa Jehobah a zai iya taimaka maka ka jimre rashin lafiya. Ko da yake ba za mu ce Allah zai warkar da mu ta hanyar mu’ujiza ba, Allah zai iya taimaka wa wadanda suke bauta masa ta wajen ba su abubuwan nan:

 Salama. Jehobah zai iya ba mutum “salama iri wadda ta wuce dukan ganewar dan Adam.” (Filibiyawa 4:​6, 7) Wannan salamar ko kwanciyar hankali, zai iya taimaka wa mutum ya rage yawan damuwa. Allah yana ba da irin wannan salamar ga wadanda suke rokonsa kuma suna gaya masa abubuwan da suke damunsu.​—1 Bitrus 5:7.

 Hikima. Jehobah zai iya ba ka hikima don ka tsai da shawarwari masu kyau. (Yakub 1:5) Mutum zai sami irin hikimar nan idan ya karanta Littafi Mai Tsarki kuma ya bi ka’idodinsa. Wadannan ka’idodin suna da amfani a koyaushe.

 Bege mai ban karfafa. Jehobah ya yi alkawari cewa rana na zuwa da “ba mazaunin kasar da zai ce, ‘Ina ciwo.’ ” (Ishaya 33:24) Wannan alkawarin yana taimaka wa mutane da yawa kar su fid da rai ko da suna fama da rashin lafiya mai tsanani.​—Irmiya 29:​11, 12.

a Jehobah ko Yahweh shi ne sunan Allah bisa ga Littafi Mai Tsarki.​—Psalm 83:18.