Koma ka ga abin da ke ciki

Koma ga abubuwan da ke ciki

Yohanna Mai Baftisma Ya Taba Wanzuwa Kuwa?

Yohanna Mai Baftisma Ya Taba Wanzuwa Kuwa?

 Linjila ta ambaci wani mutum mai suna Yohanna Mai Baftisma, wanda ya yi wa’azi game da Mulkin Allah a Yahudiya. Abin da Littafi Mai Tsarki ya ce game da mutumin gaskiya ce? Bari mu yi la’akari da wadannan:

  •   Littafi Mai Tsarki ya ce: “Yohanna Mai Baftisma ya fito yana wa’azi a cikin dajin yankin Yahudiya, yana cewa: ‘Ku tuba, gama mulkin sama ya kusa.’” (Matiyu 3:​1, 2) Masana sun tabbatar da hakan kuwa? Kwarai kuwa.

     Wani masanin tarihi mai suna Flavius Josephus ya yi bayani a kan wani mutum mai suna “Yohanna da ake ce da shi Mai Baftisma,” wanda ya “gargadi Yahudawa su yi rayuwa da ta dace,” su yi “sujjada ga Allah,” kuma “su zo a yi musu baftisma.”​—Jewish Antiquities, Book XVIII.

  •   TBaibul ya nuna cewa Yohanna ya tsauta wa Hirudus Antibas wanda shi hakimin Galili da Firiya ne. Hirudus Bayahude ne da ke da’awa cewa yana bin Dokar Allah. Yohanna ya gaya wa Hirudus cewa bai dace da ya auri Hirudiya, matar dan’uwansa ba. (Markus 6:18) Bayanin nan ya jitu da abin da masana suka ce.

     Josephus ya ce Antibas “ya yi sha’awar Hirudiya” kuma ya yi “zancen aure da ita.” Sai Hirudiya ta amince, ta bar mijinta kuma ta auri Antibas.

  •   Littafi Mai Tsarki ya ce “sai mutanen Urushalima da na yankin Yahudiya duka, da na dukan kasashen yankin kogin Yodan, suka yi ta zuwa wurinsa [Yohanna], yana yi musu baftisma a Kogin Yodan.”​—Matiyu 3:​5, 6.

     Josephus ma ya amince da wannan bayanin, kuma ya rubuta cewa “jama’a” sun zo wurin Yohanna domin “koyarwarsa ta ratsa zuciyarsu sosai.”

 Babu shakka, Josephus wanda shi masanin tarihi ne a karni na farko ya yarda cewa Yohanna Mai Baftisma ya taba wanzuwa. Mu ma mun amince da hakan.