Koma ka ga abin da ke ciki

Koma ga abubuwan da ke ciki

YADDA AKE AMFANI DA GUDUMMAWARKA

Karamin Akwati da Ke Karfafa Bangaskiyar Mutane

Karamin Akwati da Ke Karfafa Bangaskiyar Mutane

1 GA SATUMBA, 2020

 Shaidun Jehobah suna samun littattafai da bidiyoyi yanzu fiye da dā. Amma a wurare da dama a duniya, ’yan’uwanmu ba su da kudin da za su rika sayan data. Wasu kuma suna wuraren da sabis yana yawan yankewa ko bai da karfi sosai ko ma babu kwata-kwata.

 Amma yanzu, ’yan’uwa da yawa suna iya saukar da littattafanmu da bidiyoyinmu ko da babu sabis a yankinsu! Ta yaya suke yin hakan?

 Akwai wata karamar na’ura mai suna JW Box da ake tura wa ikilisiyoyin da yake musu wuya su saukar da littattafanmu da kuma bidiyoyi. Akwai na’urar sabis da ake kira router a cikinsa. An sayi na’urar ne daga wani kamfani, sa’an nan Sashen Kwamfuta da ke Bethel sun sarrafa shi yadda za a iya saka littattafai da kuma bidiyoyin jw.org a ciki. Kowane akwati yana cin wajen dala 75 (wajen naira 28,725).

 A Majami’ar Mulki, ’yan’uwa sukan sauke littattafanmu da bidiyoyinmu a wayoyinsu da taimakon na’urar JW Box. Masu wayoyin da suka tsufa ko wadanda ba su da tsada ma suna iya sauke abubuwa. Amma idan babu sabis na Intane a inda ikilisiyar take, ya za su rika samun sabbin abubuwa a JW Box? Reshen ofishinmu yakan sauke sabbin littattafai da bidiyoyi ya saka a na’urar USB, sa’an nan a tura wa ikilisiyoyin don su saka bidiyoyin a nasu JW Box. Ana sayan kowane USB a kan wajen dala 4 (wajen naira 1,544).

 Ta yaya na’urar JW Box ta taimaka wa ’yan’uwanmu? Wani mai suna Nathan Adruandra, da ke zama a Jamhuriyar Dimokuradiyyar Kwango ya ce: “Na dade ina kokari in sauke bidiyoyin nan, ‘Ya Jehobah, . . . A Gare Ka Na Dogara’ da kuma Ku Tuna da Matar Lutu, amma na kasa. Hakan ya sa ni sanyin gwiwa. Amma yanzu zan iya sauke bidiyoyin nan cikin sauki, kuma hakan ya taimaka mana mu inganta yadda muke koyar da yaranmu.”

 Wani dan’uwa da yake taimaka wa ikilisiyoyi a Najeriya su shirya na’urar JW Box ya ce: “’Yan’uwa suna daukan JW Box a matsayin babban kyauta daga wurin Jehobah. Suna farin ciki cewa yanzu za su iya saukar da littattafai da bidiyoyi da ke Kayan Aiki don Koyarwa a saukake.”

 An riga an tura JW Box fiye da 1,700 ga ikilisiyoyin da ke Afirka da Yankunan Teku da kuma Amirka ta Kudu. Kuma ana shirin tura wa wasu ikilisiyoyi da yawa. Daga ina ne aka sami kudaden da aka yi wannan aikin? Gudummawar da ake yi don aikinmu a fadin duniya ne ake amfani da su, kuma da yawa daga cikin gudummawar ta donate.dan124.com ake bayarwa. Mun gode muku sosai don yadda kuke bayarwa hannu sake.