Koma ka ga abin da ke ciki

Koma ga abubuwan da ke ciki

Ana koyar da wasu dalibai a Makarantar Gilead a 2017

YADDA AKE AMFANI DA GUDUMMAWARKA

Makarantar Gilead Tana Koyar da Mutane Daga Dukan Duniya

Makarantar Gilead Tana Koyar da Mutane Daga Dukan Duniya

1 GA DISAMBA, 2020

 Kowace shekara, ana gayyatar wasu masu hidima ta musamman daga duk fadin duniya su je Makarantar Littafi Mai Tsarki ta Gilead, da ake yi a Cibiyar Koyarwa da Ke Patterson, a New York. a Makarantar tana taimaka wa daliban su inganta yadda suke gudanar da ayyukansu a kungiyar Jehobah. Suna amfani da horarwa da suke samu wajen karfafa ikilisiyoyi da ofisoshinmu a fadin duniya.

 Daliban makarantar Gilead sukan fito daga kasashe da dama. Alal misali, dalibai 56 na aji na 147 da aka yi a 2019, sun fito ne daga kasashe 29. Akan dauko daliban Gilead ne daga ’yan’uwan da suke hidima ta musamman, kamar masu hidima a Bethel, da masu kula da da’ira, da masu wa’azi a kasashen waje da majagaba na musamman.

 Akan soma yin shirye-shirye domin ajin da dadewa kafin a soma. Alal misali, Sashen Shirya Tafiye-tafiye da Ke Hedkwatarmu takan sayo wa wadanda aka gayyata tikitin jirgin sama. A aji na 147, kudin da aka kashe don zuwa da dawowa na kowane dalibin da ya fito daga wata kasa, ya kai akalla dala 1,075 (wajen naira 409,067). Daliban da suka fito daga kasar Solomon Islands sun hau jirgin sama sau hudu kafin su kai Patterson, sa’an nan sun hau jirgin sama sau uku da suke komawa gida. Wato sun yi tafiyar kilomita 35,400 (ko mil 22,000)! An kashe dala 2,300 (wajen naira 875,213) a kan tafiyar kowannen su. Don a rage kudaden da ake kashewa, Sashen Shirya Tafiye-tafiye da Ke Hedkwatarmu yakan yi amfani da kwamfuta wajen sayan tikitin jirgin sama don a duba da kyau ko za a sami mai sauki. Kuma ko da sun riga suna saya tikiti, suna amfani da kwamfuta wajen ci gaba da bincike na tsawon makonni ko watanni ko za a sami tikitin da ya fi sauki. Sashen Shirya Tafiye-tafiye da Ke Hedkwatarmu na kuma amfani da kyaututtukan da ake samuwa daga ’yan’uwa da kuma kamfanonin jiragen sama su sayi tikiti.

 Da yawa daga cikin daliban suna bukata a samo musu biza don su iya shiga Amirka. Don haka, Sashen da Ke Kula da Shari’a a Hedkwatarmu yakan taimaka wajen samo wa daliban biza. Kudin biza da kudin yin rajista yakan kai wajen dala 510 don kowane dalibi.

 Ta yaya muke amfana daga koyarwar da ake yi wa daliban Gilead? Wani dattijo mai suna Hendra Gunawan da ya fito daga Kudu Maso Gabashin Asiya, yana ikilisiyar da akwai ma’aurata da suka taba zuwa Gilead. Kuma ya ce: “A dā ba mu da majagaba na kullum a ikilisiyarmu. Amma da ma’auratan nan suka zo ikilisiyarmu kuma ’yan’uwa sun ga kwazonsu, sai wasu a ikilisiyar suka soma hidimar majagaba. Har daga baya wata ’yar’uwa a ikilisiyarmu ta je Makarantar Masu Yada Bisharar Mulki!”

 Wani dan’uwa mai suna Sergio Panjaitan yana aiki da ’yan’uwan da suka taba zuwa Gilead a wani Bethel da ke Kudu Maso Gabashin Asiya. Dan’uwan ya ce: “Ba su kadai suke amfana daga koyarwar da aka yi musu ba, mu ma muna amfana sosai. Sun koyi abubuwa da yawa! Amma maimakon su yi kamar sun fi kowa, suna gaya mana abubuwan da suka koya. Hakan yana karfafa mu, mu kuma sai mu karfafa wasu.”

 Daga ina ake samun kudin gudanar da makarantar? Gudummawar da ake bayarwa don aikinmu a fadin duniya ne ake amfani da su. Da yawa daga cikin su ta hanyoyin ba da gudummawa da ke donate.dan124.com ake yin su. Muna muku godiya don gudummawar da kuke bayarwa hanu sake, wanda ake amfani da ita wajen tafiyar da makarantar nan da dalibanta suke fitowa daga duk fadin duniya.

a Sashen Makarantun Hidima ta Allah ne yake shirya da kuma kula da darrusan da ake koyarwa a makarantar. Suna aiki ne a karkashin Kwamitin Koyarwa na Hukumar da Ke Kula da Ayyukanmu. A sashen ne malaman da suke koyarwa suke, amma a wasu lokuta, akan gayyaci ’yan’uwan da ba sa sashen su zo su yi koyarwa, har da wasu cikin membobin Hukumar da Ke Kula da Ayyukanmu.