Koma ka ga abin da ke ciki

Koma ga abubuwan da ke ciki

WAƘA TA 51

Mun Yi Alkawarin Zama Bayin Allah

Mun Yi Alkawarin Zama Bayin Allah

(Matta 16:24)

  1. 1. Jehobah ne ya jawo mu wurin Yesu,

    Domin mu zama mabiyansa.

    Allah ya koya mana

    Gaskiya game da Shi.

    Muna da bangaskiya,

    Mun yi alkawari fa.

    (AMSHI)

    Mun yi alkawarin bauta wa Allahnmu.

    Shawarar da muka yanke ke nan.

  2. 2. Mun yi alkawari mu bauta wa Allah,

    Mu bauta masa har abada.

    Muna yin murna sosai,

    Muna son kowa ya san

    Sunan Mahaliccinmu.

    Muna shelar Mulkinsa.

    (AMSHI)

    Mun yi alkawarin bauta wa Allahnmu.

    Shawarar da muka yanke ke nan.

(Ka kuma duba Zab. 43:3; 107:22; Yoh. 6:44.)