Koma ka ga abin da ke ciki

Koma ga abubuwan da ke ciki

WAƘA TA 82

‘Mu Bari Haskenmu Ya Haskaka’

‘Mu Bari Haskenmu Ya Haskaka’

(Matta 5:16)

  1. 1. Yesu ya ce mana

    Mu haskaka fa,

    Kamar ranar da ke

    Haska ko’ina.

    Kalmar Allah tana

    Da iko sosai.

    Mu sa a ga hasken nan

    Ta wa’azinmu.

  2. 2. Mu riƙa wa’azi

    Ga duk mutane.

    Don mu ’yantar da su

    Daga duhun nan.

    Maganar Jehobah

    Muke yaɗawa.

    Za ta taimaka musu

    Su bauta masa.

  3. 3. Muna haskakawa

    Ta halayenmu,

    Furucinmu kuma

    Na da daraja.

    Bari mu haskaka

    Ta ayyukanmu,

    Hakan zai faranta ran

    Allah Jehobah.

(Ka kuma duba Zab. 119:130; Mat. 5:​14, 15, 45; Kol. 4:6.)