Koma ka ga abin da ke ciki

Kun Yarda da Cewa Allah Ya Halicci Kome Cikin Sa’o’i 24 a Kwana Shida?

Kun Yarda da Cewa Allah Ya Halicci Kome Cikin Sa’o’i 24 a Kwana Shida?

 A’a. Shaidun Jehobah sun yarda da cewa Allah ne ya halicci kome. Amma ba mu yarda cewa ya halicci kome cikin kwana shida da ke da sa’o’i 24 ba. Me ya sa? Domin ra’ayin masu gaskata da hakan ya bambanta kwarai da na Littafi Mai Tsarki. Bincika misalai biyu na gaba:

  1.   Tsawon kwana shida na halitta. Wasu da suka amince da halitta suka ce kwana shida na halitta kwanaki na sa’o’i 24 ne. Amma kalmar nan “rana” cikin Littafi Mai Tsarki zai iya nufin wani lokaci.​—Farawa 2:4; Zabura 90:4.

  2.   Dadewar Duniya. Wasu masu gaskata da cewa an yi halitta na sa’o’i 24 na kwana shida suna koyar da cewa duniya shekarunta kalilan dubbai ne kawai. Amma abin da Littafi Mai Tsarki ya ce shi ne cewa duniya da sararin sama sun kasance kafin kwanaki shida na halitta. (Farawa 1:1) Domin haka ne Shaidun Jehobah ba su ki da bincike na kimiyya da ya nuna cewa duniya ta kai shekaru biliyoyi ba.

 Shaidun Jehobah sun gaskata da halitta amma ba sa ki da kimiyya. Mun yarda cewa kimiyya ta gaske ta jitu da Littafi Mai Tsarki.