Koma ka ga abin da ke ciki

TAIMAKO DON IYALI

Yadda Za Ka Taimaka wa Danka Ya Rika Samun Maki Mai Kyau a Makaranta

Yadda Za Ka Taimaka wa Danka Ya Rika Samun Maki Mai Kyau a Makaranta

 Danka bai damu da makaranta ba, ba ya son yin nazari, kuma ba ya yin aikin da aka ba shi makaranta. Wane sakamakon ne hakan zai jawo? Ba zai rika samun maki mai kyau a makaranta ba kuma halinsa zai dada muni. Ta yaya za ka iya taimaka wa danka ya rika samun maki mai kyau?

 Abin da ya kamata ka sani

 Yawan matsi zai dada sa batun yin muni. Idan kana yawan matsa wa danka hakan zai sa ya rika damuwa a makaranta da kuma a gida! Don magance wannan matsalar yana iya yin karya ko ya boye makin da aka ba shi, ko ya yi wa malamansa karya cewa iyayensa sun ga rahotonsa, ko kuma ya rika guduwa daga makaranta. Matsalar dai za ta rika karuwa ne.

 Sakamakon da ba ka yi zato ba. Wani mahaifi mai suna Andrew ya ce: “Don mu karfafa ’yarmu, mukan ba ta kyauta idan ta sami maki mai kyau a makaranta, amma hakan ya sa ta mai da hankalinta ga samun kyautar ne. A duk lokacin da ba ta samu maki mai kyau ba tana fushi, ba don makin da ta samu ba, amma don ba za ta sami kyauta ba.”

 Ganin cewa malaman ne ke da laifi ba zai taimaka wa yaronka ba. Danka zai soma tunanin cewa ba ya bukatar ya saka kwazo kafin ya samu maki mai kyau ba. Kari ga haka, zai koyi daura wa wasu laifi don kurakurensa kuma ya so wasu su magance matsalolinsa. Bugu da kari, danka ba zai koyi hali mai muhimmanci da zai iya yin amfani da shi a lokacin da ya girma ba, wato amincewa da kurakuransa.

 Abin da za ka iya yi

 Ka kame kanka. Idan ranka ta bace, ka bari sai ka huce kafin ka tattauna da danka game da makin da ya samu a makaranta. Wani mahaifi mai suna Brett ya ce, “Ni da matata mun fi samun sakamako mai kyau a lokacin da hankalinmu ke kwance kuma muka nuna mun damu.”

 Ka’idar Littafi Mai Tsarki: Ka “kasance mai saurin ji, amma ba mai saurin magana ba ko mai saurin fushi ba.”—Yakub 1:19.

 Ka nemi sanin ainihin matsalar. Wadansu abubuwan da sukan hana yaro samu maki mai kyau a makaranta su ne, cin zali ko canjin makaranta ko tsoron rubuta jarrabawa ko matsala a iyali ko rashin isasshen barci ko rashin tsari ko kuma rashin mai da hankali. Kada ka yi tunanin cewa kyuya ne ya hana danka samun maki mai kyau.

 Ka’idar Littafi Mai Tsarki: “Wanda ya mai da hankali ga koyarwa, zai yalwata.”—Karin Magana 16:20.

 Ka taimaka wa danka ya ji dadin yin nazari. Ka tsara lokacin da danka zai rika yin nazari da kuma ayyukan makaranta. Ka samu wurin da yaronka zai rika yin ayyukansa na makaranta ba tare da wani abin da zai rika daukan hankalinsa ba (hakan ya kunshi talabijin da waya). Ka raba lokacin da danka zai rika yin ayyukan makaranta, yin hakan zai taimaka masa ya mai da hankali. Wani mahaifi mai suna Hector daga Jamus ya ce, “Idan ana so a soma jarrabawa, muna daukan dan lokaci kowace rana mu yi nazari maimakon mu jira har sai lokacin da jarrabawar ta kusa.”

 Ka’idar Littafi Mai Tsarki: “Ga kowane abu akwai lokacinsa.”—Mai-Wa’azi 3:1.

 Ka karfafa danka ya so yin karatu. Idan yaronka ya fahimci yadda yake amfana daga makaranta yanzu, hakan zai sa ya so ci gaba da koya. Alal misali, lissafi zai taimaka masa ya san yadda zai rika kashe kudi.

 Ka’idar Littafi Mai Tsarki: “Sami hikima, sami ganewa, . . . ka ɗaukaka ta sosai.”—Karin Magana 4:5, 8.

 Shawara: Ka taimaka wa yaronka ya yi ayyukansa na makaranta, amma kada ka yi masa. Wani mai suna Andrew ya ce, “’Yarmu ta fi so mu yi mata ayyukanta na makaranta maimakon ita ta yi da kanta.” Ka koya wa yaronka yadda zai rika yin ayyukan makarantarsa da kansa.