Koma ka ga abin da ke ciki

Yesu Wani Nagarin mutum ne Kawai?

Yesu Wani Nagarin mutum ne Kawai?

Amsar Littafi Mai Tsarki

 Yesu ba nagarin mutum ne kawai ba. A taƙaice dai, mutum ne da ya yi tasiri a dukan tarihi. Ka lura da abin da waɗannan sanannun ’yan tarihi da marubuta suka ce game da shi:

 “Yesu Banazari . . . shi ne ya fi suna a dukan tarihi.”—H. G. Wells, ɗan tarihi Bature.

 “Rayuwar [Yesu] ya yi tasiri ƙwarai fiye da wani a duniya kuma ya ci gaba da haka.”—Kenneth Scott Latourette, Ɗan tarihi ɗan Amirka kuma mawallafi.

 Littafi Mai Tsarki ya faɗi abin da ya sa Yesu yake da tasiri ƙwarai fiye da wani mutum nagari da ya taɓa rayuwa. Sa’anda Yesu ya tambayi mabiyansa na kud da kud ko suna ganin shi wanene ne, ɗaya cikinsu ya amsa daidai cewa: “Kai Kristi ne, Ɗan Allah mai-rai.”—Matta 16:16.