Koma ka ga abin da ke ciki

Koma ga abubuwan da ke ciki

“Ku yi kusa da Allah, shi kuwa zai yi kusa da ku.”​—Yaƙub 4:8

Allah Yana Jin Addu’o’inmu Kuwa?

Allah Yana Jin Addu’o’inmu Kuwa?

Ka taɓa shakkar ko Allah yana jin addu’o’inka? Idan haka ne, ba kai kaɗai ba ne. Mutane da yawa sukan roƙi Allah ya magance musu wasu matsalolinsu, amma Allah bai kawar musu da matsalolin ba. Shin, hakan na nufin Allah bai damu da addu’o’inmu ba ne? A’a! Littafi Mai Tsarki ya tabbatar mana cewa Allah zai amsa addu’armu idan muka yi addu’a a hanyar da ta dace. Ga wasu abubuwan da Littafi Mai Tsarki ya faɗa.

ALLAH YANA JIN ADDU’O’INMU.

“Ya kai mai jin addu’o’i! A gare ka ne dukan halitta za su zo.”​—Zabura 65:2.

Wasu mutane suna yin addu’a ne don yana kwantar musu da hankali, ko da yake sun yi imani cewa ba wanda yake sauraronsu. Amma addu’a ba magani ba ne da zai magance matsalolinmu kawai. Littafi Mai Tsarki ya gaya mana cewa “Yahweh * yana kurkusa ga masu kira gare shi, ga waɗanda suke kira gare shi cikin gaskiya. . . . Yakan kuma ji kukansu ya cece su.”​—Zabura 145:​18, 19.

Wannan ya tabbatar mana cewa Allah yana jin addu’o’in bayinsa. Domin Allah yana ƙaunar bayinsa, ya ce: “Sa’an nan za ku yi kira gare ni, ku juyo, ku yi addu’a gare ni, ni zan kuwa ji ku.”​—Irmiya 29:12.

ALLAH YANA SO KA RIƘA YIN ADDU’A.

“Ku nace da addu’a.”​—Romawa 12:​12, Littafi Mai Tsarki.

Kalmar Allah ta ce mu “dinga yin addu’a,” ta kuma ce mu ‘yi addu’a kullum.’ Hakan ya nuna mana cewa Allah yana so mu riƙa yin addu’a.​—Luka 18:1; Afisawa 6:18.

Me ya sa Allah yake so mu riƙa yin addu’a? Ku yi tunani a kan wannan, mahaifi zai ji daɗi idan ɗansa ya zo ya ce masa, “Baba, ka taimaka min da abu kaza.” Ko da mahaifin ya riga ya san abin da yaron yake bukata da yadda yake ji, a duk lokacin da ya ji yaron ya gaya masa haka, zai san cewa yaron ya yarda da shi. Hakazalika, yin addu’a ga Jehobah yana nuna cewa mun yarda da shi kuma muna so mu kusace shi.​—Karin Magana 15:8; Yaƙub 4:8.

ALLAH YA DAMU DA KAI SOSAI.

“Ku danƙa masa dukan damuwarku, gama shi ne mai lura da ku.”​—1 Bitrus 5:7.

Allah yana so mu riƙa yin addu’a domin yana ƙaunarmu kuma ya damu da mu. Ya san dukan abubuwan da suke damunmu kuma yana so ya taimaka mana.

Sarki Dauda ya yi addu’a ga Allah kuma ya gaya masa abubuwan da suka dame shi a duk rayuwarsa. (Zabura 23:​1-6) Me Allah ya yi game da hakan? Allah ya ƙaunaci Dauda kuma ya saurari addu’o’insa. (Ayyukan Manzanni 13:22) Mu ma Allah yana sauraron addu’o’in da muke yi domin ya damu da mu.

“INA ƘAUNAR YAHWEH GAMA YANA JIN MURYATA”

Abin da wani marubucin Zabura ya faɗa ke nan. Ya kasance da tabbaci cewa Allah ya ji addu’o’insa kuma hakan ya taimaka masa sosai. Ya ji kamar Allah yana tare da shi. Hakan ya ba shi ƙarfin jimre matsalolin rayuwa.​—Zabura 116:​1-9.

Idan muka san cewa Allah yana jin addu’o’inmu, za mu ci gaba da yin addu’a. Ka yi la’akari da labarin Pedro daga arewacin ƙasar Sifen. Ɗansa mai shekara 19 ya rasu a hatsarin mota. Da yake makoki, Pedro ya gaya wa Allah damuwarsa kuma ya yi ta roƙon Allah ya ƙarfafa shi ya kuma taimaka masa. Me ya faru bayan hakan? Pedro ya ce, “Jehobah ya amsa addu’ata ta wurin yin amfani da ’yan’uwa da muke ibada tare, sun ta’azantar da mu kuma sun taimaka mini da matata.”

Sau da yawa, Allah yakan amsa addu’o’inmu ta wajen sa abokanmu su taimaka mana kuma su ƙarfafa mu

Ko da yake yin addu’a bai tā da ɗan Pedro daga mutuwa ba, yin hakan ya taimaka masa da iyalinsa sosai. Matarsa María Carmen ma ta ce: “Yin addu’a ya taimaka mini in iya jimre rashin da na yi. Na san cewa Jehobah ya fahimci halin da nake ciki domin a duk lokacin da na yi addu’a, nakan sami salama da kwanciyar hankali.”

Kalmar Allah da kuma abin da ya taɓa faruwa da mutane da dama sun nuna cewa Allah yana jin addu’o’i. Amma ba dukan addu’o’i ne Allah yake amsawa ba. Me ya sa Allah yake amsa wasu addu’o’i sa’an nan ya ƙi amsa wasu?

^ sakin layi na 5 Yahweh ko Jehobah shi ne sunan Allah.​—Zabura 83:18.