Koma ka ga abin da ke ciki

Koma ga abubuwan da ke ciki

Mene ne Littafi Mai Tsarki Ya Ce?

Mene ne Littafi Mai Tsarki Ya Ce?

Shin za a daina yin rashin adalci a duniya kuwa?

Me za ka ce?

  • E

  • A’a

  • Wataƙila

Abin da Littafi Mai Tsarki ya ce

“Na sani kai, ya Ubangiji, kana kāre matsalar talakawa, da hakkin matalauta.” (Zabura 140:12, Littafi Mai Tsarki) Mulkin Allah zai sa a daina rashin adalci a duniya.

Me kuma za mu iya koya daga Littafi Mai Tsarki?

  • Allah yana ganin abin da yake faruwa a yau, kuma zai gyara su.Mai-Wa’azi 5:8.

  • Adalcin da Allah zai yi zai kawo mana salama da kwanciyar hankali a duniya.Ishaya 32:16-18.

Shin Allah yana da mutanen da ya fi ƙauna fiye da wasu ne?

Wasu sun yi imani cewa Allah yana wa wasu albarka kuma yana tsine wa wasu. Wasu kuma sun gaskata cewa Allah ba ya fifita kowa. Mene ne ra’ayinka?

Abin da Littafi Mai Tsarki ya ce

“Allah ba mai-tara ba ne: amma a cikin kowace al’umma, wanda yake tsoronsa, yana aika adalci kuma, abin karɓa ne gare shi.” (Ayyukan Manzanni 10:34, 35) A wajen Allah, dukanmu ɗaya ne.

Me kuma za mu iya koya daga Littafi Mai Tsarki?

  • Littafi Mai Tsarki yana ɗauke da “bishara” ga “kowane iri da ƙabila da harshe da al’umma.”Ru’ya ta Yohanna 14:6.