Koma ka ga abin da ke ciki

Mene Ne Watch Tower Bible and Tract Society?

Mene Ne Watch Tower Bible and Tract Society?

 Watch Tower Bible and Tract Society of Pennsylvania kungiya ce wadda ba ta cin riba ba. An kafa ta a shekara ta 1884 a karkashin dokokin Kungiyar Kasashe Rainon Ingila da ke Pennsylvania. Shaidun Jehobah suna amfani da wannan kungiyar su bunkasa aikin da suke yi a fadin duniya, wato, aikin buga Littafi Mai Tsarki da kuma littattafai da ke bayyana Littafi Mai Tsarki.

 A cikin sharudan kungiyar, an nuna cewa manufar kafa wannan kungiyar ita ce don “inganta ibada da taimaka wa jama’a, musamman a fannin yin wa’azi da koyar da albishirin Mulkin Allah da Yesu Kristi ne zai zama sarkinsa.” Sai an gayyace mutum kafin ya zama memban wannan kungiyar, kuma ba a yin hakan bisa ga yawan gudummawar da mutumin ya bayar. Membobin wannan kungiyar da darektocinta suna taimaka wa Hukumar da Ke Kula da Ayyukan Shaidun Jehobah.

Kungiyoyin da Aka Yi Wa Rajista Bisa Doka

 Ban da Watch Tower Bible and Tract Society of Pennsylvania, Shaidun Jehobah suna amfani da kungiyoyi da dama a kasashe dabam-dabam. Wadannan kungiyoyin sukan hada kalmomi kamar “Watch Tower,” “Watchtower,” ko kuma fassarar makamancin haka a cikin sunan kungiyarsu.

 Wadannan kungiyoyin sun taimaka mana mu cim ma abubuwa da yawa kamar:

  •   Rubuce-rubuce da kuma buga littattafai. Mun buga Littafi Mai Tsarki wajen kwafi miliyan 220 da kuma littattafai da ke bayyana Littafi Mai Tsarki kwafi wajen biliyan 40 a harsuna sama da 700. Mutane suna iya karanta Littafi Mai Tsarki kyauta a dandalinmu na jw.org a harsuna fiye da 120 kuma suna samun amsoshi ga tambayoyi kamar “Mene ne Mulkin Allah?

  •   Ilimantarwa. Muna da makarantu dabam-dabam da ke koyar da Littafi Mai Tsarki. Alal misali, tun shekara ta 1943, Shaidun Jehobah sama da 8,000 sun amfana daga koyarwar Makarantar Littafi Mai Tsarki ta Gilead, kuma hakan ya taimaka musu su yi wa’azi a kasashen waje ko kuma su karfafa hidimar da Shaidun Jehobah suke yi a fadin duniya. Kuma a kowane mako, miliyoyin mutane wato, Shaidun Jehobah da wadanda ba Shaidu ba, suna samun koyarwa a taron da kowace ikilisiya take yi. Kari ga haka, muna da makarantu don koyan karatu da rubutu kuma an buga wani littafi don wannan makarantar a harsuna 110.

  •   Agaji. Mun yi tanadin agaji ga wadanda bala’i ya shafa, kamar wadanda kisan kāre dangi da aka yi a shekara ta 1994 a kasar Ruwanda ya shafa ko kuma wadanda girgizar kasa ta shafa a kasar Haiti a shekara ta 2010.

 Ko da yake wadannan kungiyoyin sun taimaka mana mu cim ma abubuwa da yawa, ba mu dangana da su a aikinmu ba. Kowane Kirista yana da hakkin yin wa’azi ga mutane da kuma koyar da su. (Matta 24:14; 28:19, 20) Mun yi imani da cewa Allah yana goyon bayan aikinmu kuma zai ci gaba da zama wanda yake “ba da amfani.”—1 Korintiyawa 3:6, 7.