Koma ka ga abin da ke ciki

TAIMAKO DON IYALI

Yadda Za Ku Taimaki Yaranku Idan Ba Su Yi Nasara Ba

Yadda Za Ku Taimaki Yaranku Idan Ba Su Yi Nasara Ba

 A kwana-a-tashi yaranku ba za su yi nasara a wasu abubuwa kuma hakan zai sa su bakin ciki. Ta yaya za ku taimaka musu su magance wadannan matsalolin?

 Abin da ya kamata ka sani

 Ba za mu ci nasara a wasu lokuta ba. Littafi Mai Tsarki ya ce “dukanmu mukan yi kuskure.” (Yakub 3:2) Yara ma sukan yi kuskure. Amma yin kuskure zai iya taimaka wa yara su san yadda za su magance matsaloli a nan gaba. Ba a haifan yara da irin wannan halin, amma za su iya koya. Wata mata mai suna Laura ta ce: “Ni da mijina mun lura cewa ya fi kyau yara su koyi yadda za su iya jimre da kasawarsu maimakon su rika yi kamar sun san kome da kome. Kuma za su koya yadda za su natsu sa’ad da ba su cim ma abubuwan da suke zato ba.”

 Yara da dama ba su iya bi da kāsawarsu ba. Wasu yara ba su koyi yadda za su bi da kāsawarsu ba, domin iyayensu suna sa su ga kamar ba su da laifi. Alal misali, idan yaro ya fadi jarrabawa, wasu iyayen sukan dora wa malamin laifi. Idan kuma yaron ya samu sabani da abokinsa, iyayensa za su danka wa abokin laifi.

 Amma, ta yaya yara za su koyi amincewa da kurakuransu kuma su magance matsalar idan iyayensu na kāre su daga sakamakon?

 Abin da za ka iya yi

  •   Ku sa yaranku su san cewa akwai sakamako a duk abin da suka yi.

     Littafi Mai Tsarki ya ce: “Duk abin da mutum ya shuka, shi zai girba.”​—Galatiyawa 6:7.

     Ku taimaka wa yaranku sun san cewa ruwa ba ta tsami banza. Kari ga haka, akwai sakamako a duk abin da muka yi. Ya kamata yara su fahimci abin da ya sa aka ce “duk tsuntsu da ya jawo ruwa, shi ruwa kan doka,” kuma su kasance a shirye su dauki alhakin idan suka “jawo ruwan.” Hakazalika, ku daina dora wa wasu laifi idan yaranku ne ke da laifi. Maimakon hakan, ka bar su su yi fama da sakamakon laifinsu daidai da shekarunsu. Hakan zai taimaka ma yaron ya fahimci cewa abin da ya yi ne ya jawo matsalar.

  •   Ku taimaka wa yaranku su nemi mafita.

     Ka’idar Littafi Mai Tsarki: “Ko da mai adalci ya fādi sau bakwai, zai tashi sau bakwai kuma.”​—Karin Magana 24:16.

     Yin kuskure yakan sa mu bakin ciki, amma ba shi ne abu mafi tsanani da zai faru da mu ba. Ku taimaka wa yaranku su guji maimaita kuskuren, maimakon mai da hankali a kan abin da ya sa abin da ya faru bai dace ba. Alal misali, idan yaronka ya fadi jarrabawa a makaranta, ka taimaka masa ya ga yadda zai magance wannan matsalar ta wurin kara kwazo a yin nazari kuma ya kudiri niyyar cin jarrabawar a wani lokaci. (Karin Magana 20:4) Idan ’yar ku ta yi fada da abokiyarta, ku taimaka mata ta dauki mataki don ta sasanta da abokiyata ko da ba ita ba ce mai laifi.​—Romawa 12:18; 2 Timoti 2:24.

  •   Ku koya wa yaranku su zama masu saukin kai.

     Ka’idar Littafi Mai Tsarki: “Ina yi wa kowane dayanku gargadi cewa kada kowa ya dauki kansa da girma fiye da yadda ya kamata ya yi.”​—Romawa 12:3.

     Ba za ku taimaka wa danku ko ’yarku ba idan kuna yawan gaya mata cewa ita ce ta fi “kowa .” Bugu da kari, ba a kowane lokaci ba ne yaran da ke da ilimi ke cin jarrabawa. Kuma ba a kowane lokaci ne yaran da suka iya wani wasa suke nasara ba. Hakika, zai kasance ma yaran da ke da sauƙin kai su jimre da kasawarsu da kuma damuwarsu.

     Littafi Mai Tsarki ya ce yanayi mai wuya zai iya kara mana ƙarfi kuma ya taimaka mana mu rika jimrewa. (Yakub 1:​2-4) Ko da yake kasawa na sa damuwa, za ka iya taimaka wa yaranka su kasance da bege.

     Koya wa yara su dāge a wani wani yanayi yana bukatar lokaci da kuzari. Amma kwalliya za ta biya kudin sabulu a kurciyarsu. Wani littafi mai suna Letting Go With Love and Confidence ya ce: “Matasan da suka san yadda za su magance matsalolinsu, ba sa saurin yin abin da bai dace ba ko kuma yanke shawara da garaje. Kuma sukan jimre sa’ad da wani abu ya taso ba zato.” Hakika, taimaka wa yara su rika jimrewa zai taimaka musu sa’ad da suka zama matasa.

 Shawara: Ka kafa misali mai kyau. Ka tuna cewa yadda kake bi da munanan yanayi a rayuwa zai taimaka wa yaranka ma su bi da nasu.