Koma ka ga abin da ke ciki

Koma ga abubuwan da ke ciki

TALIFIN NAZARI NA 24

Jehobah Mai Gafartawa Ne da Babu Kamar Sa

Jehobah Mai Gafartawa Ne da Babu Kamar Sa

“Bari ya komo ga Yahweh, shi kuwa zai yi masa jinƙai, ya komo ga Yahweh gama a shirye yake ya gafarce shi.”—ISHA. 55:7.

WAƘA TA 42 Addu’ar Bawan Allah

ABIN DA ZA A TATTAUNA *

1. Mene ne Sarki Sulemanu ya faɗa a Mai-Wa’azi 7:20?

 SARKI Sulemanu ya ce: “Babu mutum mai adalci a duniyar nan mai aikata abin da yake daidai a kowane lokaci, ba tare da yin zunubi ba.” (M. Wa. 7:20) Hakan gaskiya ne domin dukanmu masu zunubi ne! (1 Yoh. 1:8) Don haka, muna bukatar Allah da kuma ʼyan Adam su gafarta mana.

2. Ya za ka ji idan abokinka ya gafarta maka?

2 Babu shakka za ka iya tuna lokacin da ka ɓata ma wani abokinka rai, amma ka ba shi haƙuri don kana so ku sasanta. Ya ka ji sa’ad da abokinka ya gafarta maka? Ka yi farin ciki sosai, ko ba haka ba?

3. Mene ne za mu tattauna a wannan talifin?

3 Muna so Jehobah ya zama abokinmu na kud da kud, amma a wasu lokuta mukan faɗi ko kuma yi abin da zai ɓata masa rai. Me ya sa za mu kasance da tabbaci cewa Jehobah yana a shirye ya gafarta mana? Wane bambanci ne ke tsakanin yadda Jehobah yake gafartawa da kuma yadda muke gafartawa? Kuma wane ne Jehobah yake gafarta wa?

JEHOBAH YANA A SHIRYE YA GAFARTA MANA

4. Me ya sa muke da tabbaci cewa Jehobah yana a shirye ya gafarta mana?

4 Kalmar Allah ta tabbatar mana cewa Jehobah yana a shirye ya gafarta mana. A Dutsen Sinai, Jehobah ya yi amfani da mala’ika ya gaya wa Musa cewa: ‘Ni ne Yahweh, ni ne Yahweh! Allah mai jinƙai ne, mai alheri, marar saurin fushi, mai yawan ƙauna marar canjawa, cike da aminci kuma, mai kiyaye ƙauna marar canjawa ga ’ya’ya har zuwa tsara ta dubu, mai gafarta laifi, da zunubin ganganci, da kowane irin zunubi.’ (Fit. 34:6, 7) Jehobah Allah mai alheri da jinƙai ne kuma yana a shirye ya gafarta wa masu zunubi da suka tuba.—Neh. 9:17; Zab. 86:15.

Jehobah ya san dukan abubuwan da suka faru a rayuwarmu da kuma yadda suka shafe mu (Ka duba sakin layi na 5)

5. Kamar yadda Zabura 103:13, 14 suka nuna, mene ne Jehobah yake yi domin ya san mu sosai?

5 Da yake Jehobah ne ya halicce mu, ya san kome game da mu. Abin al’ajabi ne cewa Jehobah ya san kome game da kowa a duniya. (Zab. 139:15-17) Don haka, ya san dukan ajizancin da muka gāda daga iyayenmu. Ban da haka, ya san abubuwan da suka faru da mu da yadda suka shafi halinmu. Mene ne Jehobah yake yi domin ya san mu sosai? Yana nuna mana jinƙai kuma yana gafarta mana.—Zab. 78:39; karanta Zabura 103:13, 14.

6. Ta yaya Jehobah ya nuna cewa yana marmarin gafarta mana?

6 Jehobah ya nuna cewa yana marmarin gafarta mana. Ya san cewa saboda zunubin da Adamu ya yi, dukanmu mun gāji zunubi da kuma mutuwa. (Rom. 5:12) Babu abin da za mu iya yi don mu ceci kanmu daga zunubi da kuma mutuwa. (Zab. 49:7-9) Amma Ubanmu mai ƙauna ya tausaya mana kuma ya buɗe hanya da za ta sa mu tsira. Mene ne ya yi? Kamar yadda Yohanna 3:16 ta nuna, Jehobah ya ba da makaɗaicin Ɗansa domin ya mutu a madadinmu. (Mat. 20:28; Rom. 5:19) Yesu ya sha wahala kuma ya mutu a madadinmu domin duk wanda ya ba da gaskiya gare shi, ya sami ’yanci. (Ibran. 2:9) Ganin yadda Ɗansa da yake ƙauna ya sha wahala da wulaƙanci sosai kafin ya mutu, ya yi wa Jehobah zafi sosai! Hakika, da a ce ba ya so ya gafarta mana, da Jehobah ba zai bar Ɗansa ya mutu a madadinmu ba.

7. Su waye ne a Littafi Mai Tsarki Jehobah ya gafarta wa?

7 Littafi Mai Tsarki yana ɗauke da labaran mutanen da Jehobah ya gafarta musu. (Afis. 4:32) Waye ne za ka iya tunaninsa? Wataƙila ka tuna da Sarki Manasse. Wannan mugun mutumin ya yi abubuwa da yawa da Jehobah ba ya so. Ya bauta wa gumaka kuma ya ƙarfafa wasu ma su yi hakan. Ya yi hadaya da ʼyaʼyansa ga allolin ƙarya. Har ma ya kafa gunki a haikalin Jehobah. Ga abin da Littafi Mai Tsarki ya faɗa game da shi cewa: “Ya aikata mugunta sosai a idon Yahweh, wanda ya sa Yahweh ya yi fushi sosai.” (2 Tar. 33:2-7) Amma da Manasse ya tuba da gaske, Jehobah ya gafarta masa. Har ma ya sake mai da shi sarki. (2 Tar. 33:12, 13) Ƙila ma za ka yi tunanin Sarki Dauda wanda ya yi zunubai masu tsanani, kamar zina da kuma kisan kai. Amma da Dauda ya tuba da gaske, kuma ya amince da laifinsa, Jehobah ya gafarta masa. (2 Sam. 12:9, 10, 13, 14) Mu kasance da tabbaci cewa Jehobah yana so ya gafarta mana. Kuma kamar yadda za mu gani, yadda Jehobah yake gafartawa ya bambanta da na ’yan Adam.

YADDA JEHOBAH YAKE GAFARTAWA

8. Tun da Jehobah ne alƙali da babu kamar sa, yaya hakan yake shafan yadda yake gafartawa?

8 Jehobah shi ne mai “shari’an dukan duniya.” (Far. 18:25) Mai shari’a nagari yana bukatar ya san dokoki sosai. Haka yake da Jehobah, shi ne Mai Shari’armu ko Alƙali da kuma Mai Ba Mu Doka. (Isha. 33:22, New World Translation) Ba wanda ya san abin da ya dace da wanda bai dace ba kamar Jehobah. Mene ne kuma mai shari’a nagari yake bukatar ya sani? Yana bukatar ya san kome da kome game da wani batu kafin ya yanke hukunci. Jehobah shi ne mai shari’a da babu kamar shi domin ya san kome da kome.

9. Mene ne Jehobah ya sani da zai sa ya gafarta wa mutum ko kuma ya ƙi yin hakan?

9 Jehobah ya bambanta da ʼyan Adam masu shari’a, domin ya san kome da kome game da kowane batu da zai yi shari’a a kai. (Far. 18:20, 21; Zab. 90:8) Yana iya ganin abubuwan da ʼyan Adam ba sa iya gani kuma yana iya jin abubuwan da ʼyan Adam ba sa iya ji. Jehobah ya san cewa halin da muka gāda daga iyayenmu da yadda aka rene mu, da wurin da muke zama, da kuma lafiyar jikinmu suna iya shafan ayyukanmu. Ban da haka, Jehobah yana ganin abin da ke zuciyar mutum. Ya san dalilin da yake sa mutane yin abubuwa da suke yi, babu abin da za a iya ɓoye masa. (Ibran. 4:13) Saboda haka, sa’ad da Jehobah ya gafarta wa mutum, yana yin hakan ne domin ya san kome da kome game da batun.

Jehobah yana yin shari’a da adalci. Ba wanda zai iya ba shi cin hanci (Ka duba sakin layi na 10)

10. Me ya sa za mu iya cewa a kowane lokaci Jehobah yana yin adalci a shari’arsa? (Maimaitawar Shari’a 32:4)

10 A kowane lokaci, Jehobah yana yin shari’a da adalci. Ba ya nuna bambanci ko kaɗan, ba siffar mutum ko kuɗi ko matsayinsa ko kuma iyawarsa ne yake sa Jehobah ya gafarta masa ba. (1 Sam. 16:7; Yak. 2:1-4) Ba wanda zai iya matsa wa Jehobah ko kuma ya ba shi cin hanci. (2 Tar. 19:7) Ba ya tsai da shawara domin yana fushi ko kuma bisa ga yadda yake ji. (Fit. 34:7) Hakika, Jehobah ne ya fi dacewa ya yi mana shari’a domin ya fahimci kome game da mu da kuma yanayinmu.—Karanta Maimaitawar Shari’a 32:4.

11. Ta yaya yadda Jehobah yake gafartawa ya bambanta da yadda ʼyan Adam suke yi?

11 Marubutan Nassosin Ibrananci sun fahimci yadda Jehobah yake gafartawa a hanya ta musamman. A wasu lokuta, sun yi amfani da kalmar Ibrananci da wani littafi ya ce “ana yin amfani da kalmar ne don a nuna yadda Allah yake gafarta wa masu zunubi, amma ba a yin amfani da wannan kalmar don a bayyana yadda ʼyan Adam suke gafarta wa juna.” Jehobah ne kaɗai yake da ikon gafarta wa mai zunubi. Mene ne yake faruwa sa’ad da Jehobah ya gafarta mana?

12-13. (a) Mene ne mutum zai mora idan Jehobah ya gafarta masa? (b) Har tsawon wane lokaci ne za mu iya amfana daga gafartawar Jehobah?

12 Idan muka gaskata cewa Jehobah ya gafarta mana, za mu sami “wartsakewa” da salama kuma zuciyarmu ba za ta riƙa damun mu ba. Jehobah ne kaɗai zai iya gafarta mana haka. (A. M. 3:19, Tsohuwar Hausa a Sauƙaƙe) Idan Jehobah ya gafarta mana, zai yarda mu sake zama abokansa.

13 Bayan Jehobah ya gafarta mana, ba zai zarge mu ko ya hukunta mu domin zunubin ba. (Isha. 43:25; Irm. 31:34) Kamar “yadda gabas take nesa da yamma,” haka Jehobah yake sa zunubanmu su yi nesa da shi. * (Zab. 103:12) Idan muka yi tunanin yadda Jehobah yake gafarta mana, hakan yana ratsa zuciyarmu sosai kuma yana sa mu nuna godiya. (Zab. 130:4) Amma waye ne Jehobah zai gafarta wa?

WA ZAI SAMI GAFARAR JEHOBAH?

14. Mene ne muka koya game da abubuwan da suke sa Jehobah ya gafarta wa mutum?

14 Kamar yadda muka gani, ba girman zunubi ko ƙanƙancinsa ne yake sa Jehobah ya gafarta wa mutum ba. Ƙari ga haka, mun koyi cewa Jehobah yana yin amfani da iliminsa a matsayin Mahaliccinmu da Mai Ba Mu Dokoki da kuma Mai Shari’a don ya yanke shawarar gafarta mana. Amma waɗanne abubuwa ne Jehobah yake tunani a kai yayin da yake so ya gafarta mana?

15. Kamar yadda Luka 12:47, 48 suka nuna, mene ne Jehobah yake tunani a kai kafin ya gafarta mana?

15 Wani abin da Jehobah yake tunani a kai shi ne ko mai zunubin ya san abin da yake yi bai dace ba. Yesu ya bayyana hakan sarai a Luka 12:47, 48. (Karanta.) Mutumin da ya zaɓi ya yi mugun abin da ya san cewa Jehobah ba ya so, yana yin zunubi mai tsanani. Jehobah yana iya zaɓa ya ƙi gafarta wa irin mutumin nan. (Mar. 3:29; Yoh. 9:41) Gaskiyar ita ce, a wasu lokuta, mukan yi abubuwan da mun san cewa ba su dace ba. Allah zai iya gafarta mana kuwa? E! Domin akwai wani abu kuma da Jehobah yake tunani a kai yayin da yake yanke shawarar gafarta mana.

Za mu iya kasancewa da tabbaci cewa Jehobah zai gafarta mana idan mun tuba da gaske (Ka duba sakin layi na 16-17)

16. Mene ne tuba, kuma me ya sa hakan yake da muhimmanci idan muna so Jehobah ya gafarta mana?

16 Wani abu kuma da Jehobah yake tunani a kai shi ne ko mai zunubin ya tuba da gaske. Mene ne tuba yake nufi? Tuba yana nufin mutum ya canja ra’ayinsa da halinsa da kuma dalilin da ya sa yake yin abubuwa. Ya ƙunshi yin nadama da kuma baƙin ciki don zunuban da mutumin ya yi ko kuma don bai yi abin da ya kamata ya yi ba. Ƙari ga haka, zai yi baƙin ciki don yadda ya bar dangantakarsa da Jehobah ta yi sanyi har ya kai shi ga yin zunubi. Ka tuna cewa Sarki Manasse da Sarki Dauda duk sun yi zunubai masu tsanani, amma Jehobah ya gafarta musu domin sun tuba da gaske. (1 Sar. 14:8) Jehobah zai gafarta mana ne idan ya ga cewa mun tuba da gaske. Amma yin da-na-sani don abin da bai dace ba da muka yi ba shi ne kaɗai abin da muke bukatar mu yi ba. Muna bukatar mu ɗau mataki. * Akwai wani abu kuma da Jehobah yake tunani a kai.

17. Me ake nufi da juyowa ga Allah, kuma me ya sa muke bukatar mu yi hakan? (Ishaya 55:7)

17 Wani abu kuma da Jehobah yake tunani a kai shi ne ko mai zunubin ya juyo gare shi, wato, mai zunubin ya canja salon rayuwarsa, ya daina yin munanan abubuwa, kuma ya soma bin ƙa’idodin Jehobah. (Karanta Ishaya 55:7.) Mutumin yana bukatar ya sabunta tunaninsa kuma ya soma tunani yadda Jehobah yake so. (Rom. 12:2; Afis. 4:23) Yana bukatar ya ƙuduri niyyar barin mugun tunani da kuma ayyukansa. (Kol. 3:7-10) Hakika yadda muka ba da gaskiya ga hadayar Yesu ne yake sa mu kasance da tabbaci cewa Jehobah zai gafarta mana kuma ya wanke mu daga zunubanmu. Jehobah zai gafarta mana domin wannan hadayar idan ya ga cewa muna yin iya ƙoƙarinmu domin mu canja salon rayuwarmu.—1 Yoh. 1:7.

KA KASANCE DA TABBACI CEWA JEHOBAH ZAI GAFARTA MAKA

18. Mene ne muka tattauna game da yadda Jehobah yake gafarta mana?

18 Bari mu yi bitar wasu daga cikin abubuwa masu muhimmanci da muka tattauna. Jehobah shi ne ya fi kowa gafartawa. Me ya sa muka ce hakan? Na farko, a kowane lokaci yana a shirye ya gafarta mana. Na biyu, ya san mu sosai. Ya san yadda aka yi mu, don haka, zai iya sani ko mun tuba da gaske. Na uku, idan Jehobah ya gafarta mana, a gabansa zai zama kamar ba mu yi zunubin ba sam-sam. Hakan zai sa zuciyarmu ta daina damun mu kuma mu mori albarka daga gare shi.

19. Ko da yake mu ajizai ne kuma za mu ci gaba da yin zunubi, me zai sa mu yi farin ciki?

19 Hakika, da yake mu ajizai ne, za mu ci gaba da yin zunubi. Amma za mu iya samun ƙarfafa daga kalmomin da ke cikin littafin nan Insight on the Scriptures Littafi na 2, shafi na 771, cewa: “Da yake Jehobah yana nuna mana jinƙai domin mu ajizai ne, ba zai dace mu bar zuciyarmu ta riƙa damun mu domin wani zunubi da muka yi sanadiyyar ajizancinmu ba. (Za 103:8-14; 130:3) Idan mun yi iya ƙoƙarinmu mu riƙa bin ƙa’idodinsa, za mu yi farin ciki. (Fib 4:4-6; 1Yo 3:19-22).” Hakika, sanin hakan yana da ban ƙarfafa!

20. Mene ne za mu tattauna a talifi na gaba?

20 Muna matuƙar godiya cewa Jehobah yana a shirye ya gafarta mana idan mun tuba da gaske daga zunuban da muka yi. Amma ta yaya za mu yi koyi da yadda Jehobah yake gafartawa? A waɗanne hanyoyi ne yadda muke gafartawa sun yi ɗaya da na Jehobah, kuma a waɗanne hanyoyi ne suka bambanta? Me ya sa sanin wannan bambancin yake da muhimmanci? Za mu tattauna waɗannan tambayoyin a talifi na gaba.

WAƘA TA 45 Abubuwan da Nake Tunani a Kai

^ A Kalmarsa, Jehobah ya tabbatar mana cewa yana a shirye ya gafarta wa masu zunubi da suka tuba. Amma a wasu lokuta, za mu iya ji kamar ba mu cancanci ya gafarta mana ba. A wannan talifin, za mu tattauna abin da ya sa ya kamata mu kasance da tabbaci cewa Allahnmu yana a shirye ya gafarta mana zunubanmu idan mun tuba da gaske.

^ MA’ANAR WASU KALMOMI: “Tuba” yana nufin mutum ya canja ra’ayinsa, ya yi da-na-sani kuma ya daina yin abubuwan da yake yi da ba su dace ba. Tuban gaske yana sa mutum ya canja salon rayuwarsa.