Koma ka ga abin da ke ciki

Koma ga abubuwan da ke ciki

Ka Sani?

Ka Sani?

Ta yaya mutane a zamanin dā suke ƙirga shekaru da watanni?

YAHUDAWA a Ƙasar Alkawari sukan fara ƙirga shekara daga lokacin da suka fara huɗa da kuma shuki. Yanzu, lokacin yana faɗuwa tsakanin Satumba da Oktoba.

Mutane suna ƙirga kwanaki 29 zuwa 30 da wata yake zagaya duniya a matsayin wata ɗaya. Suna kuma ƙirga yawan shekara daga yawan lokacin da duniya take zagaya rana. Amma idan aka ƙirga kwanakin da ke shekara ta yadda wata yake zagaya duniya, ba za su kai kwanakin da ke shekara da aka ƙirga ta yadda duniya take zagaya rana ba. Don haka, ana bukatar a sami hanyar da za a daidaita hanyoyi biyun nan da ake ƙirga lokaci. Za a iya yin hakan ta wajen ƙara kwanaki ko kuma a wasu lokuta wata ɗaya, mai yiwuwa kafin sabuwar shekara. Wannan ƙirgen zai sa a san lokacin shuki da kuma lokacin girbi.

A lokacin Musa, Jehobah ya gaya wa bayinsa cewa su soma ƙirga shekara ta ibada a watan Abib, ko kuma Nisan, wato tsakanin Maris da Afrilu. (Fit. 12:2; 13:4) Idin da ake yi a wannan watan shi ne na girbin alkama.—Fit. 23:15, 16.

Wani masani mai suna Emil Schürer ya rubuta a cikin littafinsa mai jigo The History of the Jewish People in the Age of Jesus Christ, (175 B.C.–A.D. 135) ya ce: “Yana da sauƙi a san lokacin da ya kamata a ƙara wata a cikin kalanda.” Ya kuma ƙara da cewa: “Ana yin Idin Ƙetarewa a lokacin da wata ta cika a Nisan (14 ga Nisan), wato tsakanin Maris da Afrilu washegarin ranar da tsawon dare da rana sukan daidaita . . . Idan an lura kusa da ƙarshen shekara cewa za a yi Idin Ƙetarewa kafin ranar da tsawon dare da rana suke daidaita, sai su ƙara wata ɗaya kafin watan Nisan.”

Shaidun Jehobah suna yin amfani da wannan tsarin su san ranar da ya jitu da 14 ga watan Nisan a kalandar Yahudawa, don su Tuna da Mutuwar Yesu. Akan gaya wa dukan ikilisiyoyi a faɗin duniya ranar da za a yi taron tun da wuri. *

Amma ta yaya Yahudawa suke sanin ƙarshen wata da kuma sabon wata? A yau, za ka iya duba kwanan wata a kalanda ko kuma wayarka. Amma a zamanin dā, sanin lokacin da wata zai ƙare da kuma soma bai da sauƙi.

A zamanin Nuhu, wata ɗaya ya ƙunshi kwanaki 30. (Far. 7:11, 24; 8:3, 4) Daga baya a zamanin Isra’ilawa, an soma amfani da wata hanya dabam wajen sanin wata ɗaya. A kalandar Ibraniyawa, ana soma ƙirga wata daga lokacin da jinjirin wata ya fito. Daga lokacin zuwa lokacin da wani jinjirin wata zai fito, kwanaki 29 ne ko kuma 30.

Akwai lokacin da Dauda da kuma Jonatan suka yi magana game da sabon wata. Sun ce: “Gobe ne Bikin Sabon Wata.” (1 Sam. 20:5, 18) Don haka, da alama a zamaninsu ana sanin lokacin da sabon wata zai fara tun da wuri. Ta yaya Isra’ilawa suke sanin lokacin da sabon wata zai fara? Littafin da ke ƙunshe da dokoki da kuma al’adun Yahudawa da ake kira Mishnah ya yi bayani a kan hakan. Littafin ya nuna cewa bayan da Isra’ilawa suka dawo daga bauta a Babila, babban kotun Yahudawa da ake kira Sanhedrin ne take tantance lokacin da sabon wata zai fara. A cikin watanni bakwai da ake yin bukukuwa, kotun takan yi zama kowace rana ta 30 na watan. Kotun ce take tantance ranar da sabon wata zai soma. Me ke taimaka wa kotun ta yi hakan?

Akwai mutane da suke tsayawa a wurare masu tsawo a Urushalima don su iya ganin jinjirin wata da zai fito. Da zarar sun ga jinjirin watan, sai su gaya wa kotun nan da nan. Idan mutane da dama sun gaya wa kotun cewa sun ga sabon watan, sai kotun ta sanar da somawar sabon wata. To, me zai faru idan hazo ko hadari ya hana mutanen ganin sabon watan? Sai a sanar cewa watan da ke ci yana da kwana 30. Bayan hakan sai a soma sabon wata washegari.

Littafin nan Mishnah ya bayyana cewa ana sanar da somawar sabon wata ta wurin kunna wuta a kan Dutsen Zaitun da ke kusa da Urushalima. Akan kuma kunna wuta a wasu wurare da ke da tsawo a duk ƙasar Isra’ila don a sanar da somawar sabon wata. Daga baya, an soma aika mutane su yi shelar hakan. Don haka, dukan Isra’ilawa da ke Urushalima, da waɗanda suke wurare dabam-dabam a duk ƙasar Isra’ila suna iya sanin somawar sabon wata. Hakan zai sa dukansu su iya yin bukukuwa a lokaci ɗaya.

Akwatin da ke talifin nan zai taimaka maka ka fahimci yadda watanni da bukukuwa da kuma lokuta suke a zamanin Isra’ilawa.

^ Ka duba Hasumiyar Tsaro ta 15 ga Fabrairu, 1990, shafi na 15, da “Questions From Readers” a Hasumiyar Tsaro ta 15 ga Yuni, 1977, duka a Turanci.