Koma ka ga abin da ke ciki

Koma ga abubuwan da ke ciki

TALIFIN NAZARI NA 26

Yadda Kauna Take Taimaka Mana Mu Shawo Kan Tsoro

Yadda Kauna Take Taimaka Mana Mu Shawo Kan Tsoro

“Yahweh yana tare da ni, ba zan ji tsoro ba.”—ZAB. 118:6.

WAƘA TA 105 “Allah Ƙauna Ne”

ABIN DA ZA A TATTAUNA *

1. Waɗanne abubuwa ne za su iya ba mu tsoro?

 KA YI la’akari da labaran nan. Wani ɗan’uwa mai suna Nestor da matarsa María, sun so su yi hidima a inda ake bukatar masu shela. * Amma kafin su iya yin hakan, suna bukatar su sauƙaƙa salon rayuwarsu. Sun ji tsoro cewa ba za su ji daɗin rayuwa ba idan ba su da kuɗi mai yawa. Sa’ad da Biniam ya zama Mashaidin Jehobah a ƙasar da aka hana ayyukan Shaidun Jehobah, ya fahimci cewa za a iya tsananta masa. Hakan ya tsorata shi. Amma abin da ya fi ba shi tsoro shi ne tunanin abin da iyalinsa za su yi idan suka ji cewa ya zama Mashaidin Jehobah. Wata ’yar’uwa mai suna Valérie ta kamu da cutar kansa mai tsanani kuma ta yi ta neman likita da zai yi mata tiyata ba tare da ƙarin jini ba. Sai ta soma jin tsoro cewa za ta mutu.

2. Me ya sa muke bukatar mu yi ƙoƙari don kada tsoro ya shawo kanmu?

2 Ka taɓa jin tsoro haka? E, ya taɓa kama da yawa daga cikin mu. Idan muka bar irin tsoron nan ya shawo kanmu, za mu yanke shawarar da ba ta dace ba kuma hakan zai shafi dangantakarmu da Jehobah. Abin da Shaiɗan yake so ke nan. Ƙari ga haka, yana ƙoƙarin tsorata mu don ya sa mu ƙi bin dokokin Jehobah haɗe da dokar da aka ba mu cewa mu yi wa’azi. (R. Yar. 12:17) Shaiɗan mugu ne, marar tausayi, kuma yana da iko. Amma za ka iya kāre kanka daga Shaiɗan. Ta yaya?

3. Mene ne zai taimaka mana kada mu bar tsoro ya shawo kanmu?

3 Idan muna da tabbaci cewa Jehobah yana tare da mu kuma yana ƙaunar mu, Shaiɗan ba zai sa mu tsoro ba. (Zab. 118:6) Alal misali, marubucin Zabura 118 ya fuskanci matsaloli da dama. Yana da maƙiya da yawa kuma wasun su suna da matsayi sosai (ayoyi 9 da 10). Akwai lokutan da ya damu sosai (aya ta 13). Kuma Jehobah ya yi masa horo (aya 18). Duk da haka, marubucin zaburar ya ce: “Ba zan ji tsoro ba.” Me ya sa marubucin zaburar bai ji tsoro ba kuma ya kasance da kwanciyar hankali? Ya san cewa ko da yake Jehobah ya yi masa horo, Ubansa na sama yana ƙaunarsa sosai. Marubucin zaburar ya kasance da tabbaci cewa ko da wane yanayi ne ya shiga, Allahnsa mai ƙauna yana shirye ya taimaka masa.—Zab. 118:29.

4. Idan muna da tabbaci cewa Jehobah yana ƙaunar mu, waɗanne irin tsoro ne ba za mu bari su shawo kanmu ba?

4 Muna bukatar mu kasance da tabbaci cewa Jehobah yana ƙaunar mu. Idan muna da wannan tabbacin, ba za mu bar tsoro ya shawo kanmu ba. Alal misali, (1) ba za mu ji tsoro cewa ba za mu iya tanada wa iyalinmu ba, (2) ba za mu ji tsoron mutum ba, kuma (3) ba za mu ji tsoron mutuwa ba. ’Yan’uwa da aka ambata a sakin layi na farko sun daina jin tsoro domin sun tabbatar wa kansu cewa Jehobah yana ƙaunar su.

JIN TSORO CEWA BA ZA MU IYA TANADA WA IYALINMU BA

Wani ɗan’uwa yana kamun kifi tare da ɗansa domin ya yi wa iyalinsa tanadi (Ka duba talifin nazari na 26, sakin layi na 5)

5. Waɗanne irin yanayoyi ne za su iya sa magidanci ya damu? (Ka duba hoton da ke shafin farko.)

5 Kirista da ke da iyali ba ya wasa da hakkin da yake da shi na kula da iyalinsa. (1 Tim. 5:8) Idan kai magidanci ne, mai yiwuwa a lokacin annobar korona ka damu cewa za ka rasa aikinka. Ka damu cewa hakan zai iya sa ka kasa yi wa iyalinka tanadin abinci da wurin kwana. Ban da haka, mai yiwuwa ka ji tsoro cewa idan ka rasa aikinka, zai yi maka wuya ka sake samun wani aiki. Ko kuma kamar Nestor da matarsa María, mai yiwuwa ka ji tsoro cewa ba za ka ji daɗin rayuwa ba idan ba ka da kuɗi mai yawa. Shaiɗan ya yi nasarar hana mutane da yawa bauta wa Jehobah domin irin wannan tsoron.

6. Wane ra’ayi ne Shaiɗan yake so mu kasance da shi?

6 Shaiɗan yana ƙoƙari ya sa mu ji kamar Jehobah bai damu da mu ba kuma ba zai iya taimaka mana mu tanada wa iyalinmu ba. Hakan zai iya sa mu ɗauka cewa muna bukatar mu yi duk abin da za mu iya yi don kar mu rasa aikinmu, ko da hakan zai taka dokar Allah.

7. Wane tabbaci ne Yesu ya ba mu?

7 Yesu ya san Jehobah fiye da kowa kuma ya tabbatar mana da cewa Allahnmu ‘ya san abin da muke bukata kafin ma mu roƙe shi.’ (Mat. 6:8) Kuma Yesu ya san cewa a shirye Jehobah yake ya tanada mana abin da muke bukata. A matsayinmu na Kiristoci, muna cikin iyalin Jehobah, kuma za mu iya kasancewa da tabbaci cewa da yake Jehobah ne Ubanmu, zai yi abin da ya gaya wa magidanta a 1 Timoti 5:8.

Jehobah zai tabbata cewa mun sami abubuwan da muke bukata. Zai iya yin amfani da ’yan’uwanmu ya taimaka mana (Ka duba sakin layi na 8) *

8. (a) Me zai taimaka mana mu daina tsoro cewa ba za mu iya tanada wa iyalinmu ba? (Matiyu 6:31-33) (b) Kamar yadda hoton ya nuna, ta yaya za mu iya yin koyi da ma’aurata da suka kai ma wata ’yar’uwa abinci?

8 Idan mun kasance da tabbaci cewa Jehobah yana ƙaunar mu kuma yana ƙaunar iyalinmu, ba zai yi mana wuya mu gaskata cewa zai yi mana tanadin abubuwan da muke bukata ba. (Karanta Matiyu 6:31-33.) Jehobah yana so ya yi mana tanadi kuma shi Mai bayarwa hannu sake ne! Sa’ad da ya halicci duniya, ya ba mu abubuwa da dama fiye da abubuwa da muke bukata don mu rayu. Ya halicci abubuwa da dama a duniya da za su sa mu ji daɗin rayuwa. (Far. 2:9) Ko da yake a wasu lokuta ba ma samun abubuwa da yawa, ya kamata mu yi farin ciki cewa muna samun waɗanda muke bukata. Jehobah ba ya fasa yi mana tanadi. (Mat. 6:11) Ya kamata mu riƙa tuna cewa abin da Jehobah zai ba mu a yanzu ya fi duk wata sadaukarwa da za mu yi, kuma a gaba zai ba mu rai na har abada. Abin da Ɗan’uwa Nestor da matarsa María suka fahimta ke nan.—Isha. 65:21, 22.

9. Mene ne ka koya daga labarin Nestor da matarsa María?

9 Ɗan’uwa Nestor da matarsa María suna da gida mai kyau a ƙasarsu Kolombiya. Sun ce: “Mun so mu sauƙaƙa rayuwarmu kuma mu daɗa ƙwazo a hidimarmu ga Jehobah. Amma mun ji tsoro cewa ba za mu ji daɗin rayuwa ba idan ba mu da kuɗi da yawa.” Me ya taimake su su daina tsoro? Sun yi tunanin hanyoyi da yawa da Jehobah ya nuna musu ƙauna. Hakan ya tabbatar musu cewa Jehobah zai ci gaba da kula da su. Sai suka yi murabus daga aikinsu da ake biyan su sosai. Sun sayar da gidansu kuma sun ƙaura zuwa yankin da ake bukatar masu shela a ƙasarsu. Ya suke ji game da matakin da suka ɗauka? Nestor ya ce: “Jehobah ya yi mana abin da ya faɗa a Matiyu 6:33. Ba mu taɓa rasa abin da muke bukata ba kuma yanzu muna farin ciki fiye da dā.”

TSORON MUTUM

10. Me ya sa ba abin mamaki ba ne cewa mutane suna tsoron juna?

10 Tun daga lokacin da Adamu da Hauwa’u suka yi tawaye ga Jehobah, ’yan Adam sun ci gaba da yi wa juna mugunta. (M. Wa. 8:9, Mai Makamantu Ayoyi) Alal misali, mutane suna amfani da ikonsu su danne wasu, masu aikata laifi suna yin mugunta, wasu ɗalibai suna cin zalin ’yan makarantarsu, kuma wasu mutane suna wulaƙanta iyalinsu. Shi ya sa mutane suna tsoron juna. Ta yaya Shaiɗan yake amfani da tsoron mutum?

11-12. Ta yaya Shaiɗan yake amfani da tsoron mutum?

11 Shaiɗan yana amfani da tsoron mutum don ya hana mu yin wasu abubuwa da Jehobah ya ce mu yi har da wa’azi. A wasu lokuta, Shaiɗan yakan sa gwamnatoci su sa wa Shaidun Jehobah takunkumi kuma su tsananta musu. (Luk. 21:12; R. Yar. 2:10) Ban da haka, mutane sukan yaɗa ƙarya game da Shaidun Jehobah. Mutane da suka gaskata da ƙaryar sukan yi mana ba’a ko su kai mana hari. (Mat. 10:36) Ba ma mamaki don wannan dabarar da Shaiɗan yake amfani da ita. Ya yi amfani da dabarar a ƙarni na farko.—A. M. 5:27, 28, 40.

Ko da iyalinmu suna hamayya da mu, za mu iya kasancewa da tabbaci cewa Jehobah yana ƙaunar mu (Ka duba sakin layi na 12-14) *

12 Ba tsoron hamayya daga gwamnatoci ne kaɗai Shaiɗan yake amfani da shi ba. Wasu sun fi tsoron abin da iyalinsu za su yi idan sun ji cewa sun zama Shaidun Jehobah. Suna ƙaunar ’yan’uwansu sosai kuma suna so ’yan’uwansu su san game da Jehobah. Ba sa jin daɗi idan suka ji iyalinsu suna maganganu da ba su dace ba game da Jehobah da bayinsa. Amma a wasu lokuta, waɗanda suka yi hamayya da ’yan’uwansu daga baya sukan soma bauta wa Jehobah. Amma idan ’yan’uwanmu sun yashe mu saboda mun zama Shaidun Jehobah fa? Me ya kamata mu yi?

13. In mun tabbata cewa Jehobah yana ƙaunar mu, ta yaya hakan zai taimake mu idan iyalinmu sun yashe mu? (Zabura 27:10)

13 Za mu iya samun ƙarfafa idan mun yi bimbini a kan Zabura 27:10. (Karanta.) Idan mun tuna yadda Jehobah yake ƙaunar mu, ba za mu ji tsoro ba ko da iyalinmu sun yashe mu. Kuma mun tabbata cewa zai albarkace mu domin yadda muka jimre. Jehobah zai ba mu abubuwan da muke bukata, zai ba mu kwanciyar hankali da farin ciki, kuma ya sa mu daɗa kusantar sa. Babu wanda zai fi shi yin hakan. Abin da Ɗan’uwa Biniam, da muka ambata ɗazu ya shaida ke nan.

14. Me za ka iya koya daga labarin Biniam?

14 Biniam ya zama Mashaidin Jehobah ko da yake ya san cewa gwamnatin ƙasarsu tana tsananta wa Shaidun Jehobah. Ka yi la’akari da yadda sanin cewa Jehobah yana ƙaunar sa ya taimaka masa kada ya bar tsoron mutum ya shawo kansa. Ya ce: “Tsanantawar ta wuce yadda na yi tsammani. Amma abin da ya fi ba ni tsoro shi ne yadda iyalina za su yi hamayya da ni. Na ji tsoro cewa babana, wanda ba Mashaidi ba ne, zai yi baƙin ciki domin na zama Mashaidin Jehobah kuma iyalina za su daina daraja ni.” Amma Biniam ya tabbata cewa Jehobah yana kula da waɗanda yake ƙaunar su a kullum. Biniam ya ce: “Na yi tunani a kan yadda Jehobah ya taimaka ma wasu su jimre talauci da wariya da tsanantawa. Na san cewa idan na ci gaba da bauta wa Jehobah zai yi min albarka. Da aka kama ni sau da yawa kuma aka min duka, na shaida yadda Jehobah yake taimaka mana a lokacin da muke cikin damuwa in mun riƙe amincinmu.” Jehobah ya zama Uba ga Biniam kuma mutanensa sun zama iyalin Biniam.

TSORON MUTUWA

15. Me ya sa muke tsoron mutuwa?

15 Littafi Mai Tsarki ya kira mutuwa abokiyar gāba. (1 Kor. 15:25, 26) Za mu iya damuwa idan muka yi tunani game da mutuwa musamman idan mu ko wani ɗan’uwanmu yana rashin lafiya mai tsanani. Me ya sa muke tsoron mutuwa? Domin Jehobah ya halicce mu da sha’awar yin rayuwa har abada. (M. Wa. 3:11, New World Translation) Tsoron mutuwa zai iya taimaka mana mu kāre kanmu. Alal misali, irin wannan tsoron yana iya sa mu riƙa cin abincin da ya dace kuma mu riƙa motsa jiki, mu sayi magunguna kuma mu nemi taimakon likitoci idan da bukata. Ƙari ga haka, zai taimaka mana mu guji yin abubuwan da za su sa rayukanmu cikin haɗari.

16. Ta yaya Shaiɗan yake amfani da yadda muke tsoron mutuwa?

16 Shaiɗan ya san cewa muna ɗaukan ranmu da daraja sosai. Ya yi da’awar cewa za mu iya sadaukar da dukan abubuwan da muke da su, har ma da dangantakarmu da Jehobah don mu kāre ranmu. (Ayu. 2:4, 5) Abin da Shaiɗan ya faɗa ƙarya ne! Duk da haka, da yake shi ne “yake riƙe da ikon mutuwa,” Shaiɗan yana ƙoƙarin yin amfani da tsoron mutuwa don ya sa mu daina bauta wa Jehobah. (Ibran. 2:14, 15) A wasu lokuta, Shaiɗan yana sa mutane su yi barazanar kashe mu idan ba mu daina bauta wa Jehobah ba. A wasu lokuta kuma, idan Shaiɗan ya ga cewa muna rashin lafiya mai tsanani, zai iya amfani da damar don ya sa mu taka dokar Jehobah. Likitoci ko iyalanmu da ba Shaidu ba za su iya matsa mana mu karɓi ƙarin jini, kuma yin hakan zai taka dokar Jehobah. Ko kuma wani zai iya matsa mana mu yi jinyar da ba ta jitu da ƙa’idodin Jehobah ba.

17. Bisa ga Romawa 8:37-39, me ya sa ba ma bukatar mu ji tsoron mutuwa?

17 Ko da yake ba ma so mu mutu, mun san cewa ko da mun mutu, Jehobah ba zai daina ƙaunar mu ba. (Karanta Romawa 8:37-39.) Idan bayin Jehobah suka mutu, yana tunawa da su kamar ba su mutu ba. (Luk. 20:37, 38) Yana marmarin tā da su. (Ayu. 14:15) Jehobah ya ba da Ɗansa da yake ƙauna domin mu “sami rai na har abada.” (Yoh. 3:16) Mun san cewa Jehobah yana ƙaunar mu sosai kuma yana kula da mu. Don haka, a maimakon mu daina bauta wa Jehobah a lokacin da muke rashin lafiya, ko kuma aka yi barazanar kashe mu, zai dace mu nemi taimakonsa don ya ƙarfafa mu, ya ba mu hikima kuma ya ba mu ƙarfin jimrewa. Abin da Valérie da maigidanta suka yi ke nan.—Zab. 41:3.

18. Mene ne ka koya daga labarin Valérie?

18 Sa’ad da Valérie take shekara 35, ta kamu da cutar kansa mai tsanani da ba a cika kamuwa da ita. Ka yi la’akari da yadda ƙauna ta taimaka mata ta daina jin tsoron mutuwa. Ta ce: “Rashin lafiyar ya canja rayuwarmu farat ɗaya. Na bukaci a yi min tiyata don kada in rasa raina. Na tuntuɓi likitoci da dama amma sun ce ba za su yi min tiyata ba sai da ƙarin jini. Na ji tsoro sosai, amma na ƙi karɓan ƙarin jini domin ba na so in taka dokar Jehobah. Jehobah ya riga ya nuna mini ƙauna sosai a duk rayuwata. Yanzu na sami dama da zan nuna masa cewa ina ƙaunarsa. A duk lokacin da likitoci suka gaya mini cewa rashin lafiyata ya daɗa muni, ina daɗa ƙudura cewa zan yi abin da zai sa Jehobah farin ciki, kuma ba zan sa Shaiɗan farin ciki ba. A ƙarshe, an yi min tiyata ba tare da ƙarin jini ba. Ko da yake har yanzu ina fama da rashin lafiya, Jehobah ya ci gaba da ba mu abubuwan da muke bukata. Alal misali, ’yan kwanaki kafin a gano cewa ina da cutar kansa, mun tattauna talifin nan ‘Yadda Za Mu Jimre Da Matsalolinmu Da Gaba Gaɗi.’ * Talifin ya ƙarfafa mu sosai. Mun karanta shi sau da yawa. Karanta talifofi kamar haka da yin ayyukan ibada kullum sun taimaka mana mu sami kwanciyar hankali kuma mu yanke shawarwarin da suka dace.”

YADDA ZA MU DAINA JIN TSORO

19. Mene ne zai faru nan ba da daɗewa ba?

19 Da taimakon Jehobah, Kiristoci sun jimre matsaloli da dama kuma sun yi tsayayya da Shaiɗan. (1 Bit. 5:8, 9) Kai ma za ka iya yin hakan. Ba da jimawa ba Jehobah zai sa Yesu da abokan sarautarsa su “rushe ayyukan Shaiɗan.” (1 Yoh. 3:8) Bayan haka, bayin Allah a duniya ba za su ji tsoron kome ba. (Isha. 54:14; Mik. 4:4) Amma kafin lokacin, muna bukatar mu yi ƙoƙari don kada mu bar tsoro ya shawo kanmu.

20. Me zai taimaka mana mu daina jin tsoro?

20 Dole ne mu ci gaba da kasancewa da tabbaci cewa Jehobah yana ƙaunar bayinsa kuma yana kāre su. Yin bimbini da kuma tattauna yadda Jehobah ya kāre bayinsa a dā zai taimake mu. Kuma zai dace mu riƙa tuna yadda ya taimaka mana mu jimre matsaloli a baya. Da taimakon Jehobah, za mu iya daina jin tsoro.—Zab. 34:4.

WAƘA TA 129 Za Mu Riƙa Jimrewa

^ Tsoro yana taimaka mana mu guji haɗari. Amma a wasu lokuta ba zai yi kyau mu ji tsoro ba. Shaiɗan zai yi ƙoƙari ya sa mu ji tsoro sosai har mu yi abin da bai dace ba. Don haka, muna bukatar mu guji irin wannan tsoro. Me zai taimaka? Kamar yadda za mu koya a wannan talifin, idan muna da tabbaci cewa Jehobah yana tare da mu kuma yana ƙaunar mu, tsoro ba zai hana mu yin abin da ya kamata ba.

^ An canja wasu sunayen.

^ Ka duba Hasumiyar Tsaro ta 15 ga Oktoba, 2012, shafuffuka na 7-11.

^ BAYANI A KAN HOTUNA: Wasu ma’aurata da suke ikilisiya ɗaya da wata ’yar’uwa mai ƙwazo sun kai mata da iyalinta abinci.

^ BAYANI A KAN HOTUNA: Iyayen wani matashi ba sa so ya bauta wa Jehobah, amma ya gaskata cewa Jehobah zai taimaka masa.