Koma ka ga abin da ke ciki

TAMBAYOYIN MATASA

Shin Mu Abokai Ne Ko Kuma Masoya?—Sashe na 2

Shin Mu Abokai Ne Ko Kuma Masoya?—Sashe na 2

 A kowane lokaci kana so ka saurari abokanka sa’ad da suke so su tattauna da kai. Amma yanzu a cikinsu, akwai wani ko wata da kake yawan magana da ita. Kana iya gaya wa kanka cewa: “Ai mu abokai ne kawai,” kuma kana ganin cewa haka ne dayan ma take ji. Ya kamata ku damu da hakan ne?

 Abin da zai iya faruwa

 Ba laifi ba ne mu samu abokai ko namiji ne ko tamace. Amma idan ka kulla abokantaka na kud da kud da wata fiye da sauran kuma fa? Idan hakan ya faru, za ta iya ji kamar son ta kake yi.

 Son ta kake yi da gaske? Ku yi la’akari da abubuwan da za su iya nuna cewa kuna so mutum.

  •   Kana yawan tattaunawa da ita.

     Wata matashiya mai suna Sierra ta ce: “Ko da yake ba za ka iya sanin yadda mutumin yake ji a zuciyarsa ba, bai kamata ki sa mutumin cikin wani mummunan hali ta wajen kira da kuma tattaunawa da shi a kowane lokaci amma kuma kina daukansa a matsayin aboki kawai.”

  •   Kana yawan saurarar ta a lokacin da take so ta yi magana.

     Wani matashi mai suna Richard ya ce: “Ko da yake ba ni nake soma tura mata sako amma ina amsawa a duk lokacin da ta tura mini sako. Bayan haka, ya kasance mini da wuya in gaya mata cewa na dauke ta a matsayin abokiyata kawai.”

  •   Kana sa ta ci gaba da tattaunawa da kai.

     Wata matashiya mai suna Tamara ta ce: “Wasu mutane suna ganin kwarkwasa ba wani abin damuwa ba ne. Suna wasa da hankalin mutum kuma suna kulla dangantaka ba tare da nufin yin aure a nan gaba ba.”

 Gaskiyar al’amarin: Idan kuna yawan tattaunawa da kuma kula da juna, hakan zai iya nuna cewa kuna son juna.

 Abin da ya sa ya kamata ku mai da hankali

  •   Yakan sa mutumin bakin ciki.

     Abin da Littafi Mai Tsarki ya ce: “Muradin da ba a biya ba yakan sa zuciya ta yi ciwo.” (Misalai 13:12) Wane tunani ne za ka yi idan wata ta soma yin abubuwan da suke nuna kamar son ka take yi?

     Wata matashiya mai suna Jessica ta ce: “Idan mutum bai shirya fita zance ba kuma ya soma yin abubuwan da suke nuna kamar yana son wata, hakan yana kamar kama kifi da mutumin ya ki ci kuma bai kyale kifin ya tafi ba. Zai sa ta bakin ciki sosai.”

  •   Zai bata sunanka.

     Littafi Mai Tsarki ya ce: “Kowannenku kada ya kula da harkar kansa kawai, sai dai ya kula, har da ta ɗan’uwansa ma.” (Filibiyawa 2:4, Littafi Mai Tsarki) Wane irin hali ne za ka ce mutumin da yake damuwa da kansa kawai yake da shi? Ta yaya hakan zai shafi sunansa?

     Wata matashiya mai suna Julia ta ce: “Ba na son saurayin da yake son yin kwarkwasa da ’yammata. Wanda yake yin kwarkwasa ba zai iya rike amana a aure ba. Sa’ad da kake kwarkwasa, kana amfani da ita ne don a san cewa kai ma kana da abokiya, kuma hakan ba shi da kyau, son kai ne.”

 Gaskiyar al’amarin: Mutanen da suke nuna cewa suna son wani amma kuma ba da niyyar yin aure ba suna sa wasu bakin ciki da kuma kansu.

 Abin da za ka iya yi

  •   Littafi Mai Tsarki ya ce ku bi da ‘samari ... kamar ’yan’uwanku,’ kuma ‘’yammata kuwa kamar ’yan’uwanku.’ (1 Timotawus 5:1, 2, Littafi Mai Tsarki) Idan kuna bin wannan shawarar, za ku ci gaba da dangantaka da mutane ko namiji ne ko kuma tamace.

     Wata matashiya mai suna Leah ta ce: “Idan na yi aure ba zan yi kwarkwasa da mijin wata ba. Saboda haka, zai fi dacewa tun yanzu da ban yi aure ba in rika mai da hankali da yadda nake sha’ani da maza.”

  •   Littafi Mai Tsarki ya ce: “A cikin yawan maganganu ba a rasa saɓo ba.” (Misalai 10:19) Wannan ka’idar ba ta nufin tattaunawa da baki kawai ba, amma ta shafi tura sakonni da kuma yawan yadda ake hakan da irin sakon da ake turawa.

     Wani matashi mai suna Brian ya ce: “Idan ba ka so ka soma fita zance da wata yarinya, ban ga amfanin tura mata sako kowane lokaci ba.”

  •   Littafi Mai Tsarki ya ce: “Hikima mai-fitowa daga bisa tsatsarka ce.” (Yaƙub 3:17) Za ka iya rungume mutum ba da wata manufar soyayya a zuciya ba ko kuma ka yi hakan a yadda zai nuna cewa kana da niyyar yin soyayya da mutumin.

     Wata matashiya mai suna Maria ta ce: “Ina iya kokarina don kada abokaina su yi tunanin wani abu dabam a zuciyarsu sa’ad da nake tattaunawa da su.”

 Gaskiyar al’amarin: Ka ko ki bincika yadda kike yin sha’ani da maza. Wata matashiya mai suna Jennifer ta ce: “Yana da wuya mutum ya sami abokan kirki, don hakan ba za ka so ka bata dangantakarka da abokanka ba ta wajen yin abubuwan da ba su dace ba.”

 Shawara

  •    Ka rika mai da hankali ga abubuwan da mutane suke fada. Idan wani ya tambaye ka, “Wannan yarinyar budurwarka ce?” hakan yana nuna cewa kai da yarinyar kun shaku sosai.

  •    Ka rika sha’ani da dukan abokanka mata. Kada ka ware guda daya kuma ka rika cudanya da ita fiye da sauran.

  •   Ka mai da hankali da yadda kake yawan tura sako da abin da kake fada da kuma lokacin da kake tura sakon. Wata yarinya mai suna Alyssa ta ce, “bai kamata ku rika tura wa namiji ko tamace sako da tsakar dare ba.”