Koma ka ga abin da ke ciki

Na Shaku da Kallon Hotunan Batsa

Na Shaku da Kallon Hotunan Batsa

Abin da za ka iya yi

 Ka fahimci abin da hotunan batsa yake nufi. Kallon hotunan batsa yana kaskantar ne da abin da Allah ya halitta da daraja. Idan ka fahimci abin da ake nufi da kallon hotunan batsa hakan zai taimake ka ka guji “mugunta.”—Zabura 97:10.

 Ka yi la’akari da sakamakonsa. Kallon hotunan batsa yana kaskantar da wadanda suke ciki. Yana kuma kaskantar da wanda yake kallonsu. Domin haka, Littafi Mai Tsarki ya ce: “Mutum mai-hankali ya kan hangi masifa, ya buya.”—Misalai 22:3.

 Ka yi alkawari. Ayuba ya ce: “Na yi alkawarin cewa ba zan taba sha’awar yin lalata da budurwa ba.” (Ayuba 31:1, juyin Today’s English Version) Ga wasu ‘alkawura’ da za ka iya yi:

  •  Ba zan yi amfani da intane ba idan ni kadai ne a wurin.

  •  Zan rufe duk wani abin banza da zai bullo mini a Intane ko kuma wani wajen da ban gane ba.

  •  Zan gaya wa wani aboki da ya manyanta idan na sake fada wa halin.

Kallon hotunan batsa bai da kyau—da zarar ka fara, fita za ta yi wuya

 Ka yi addu’a game da hakan. Mai zabura ya roki Jehobah Allah: “Ka kawar da idanuna ga barin duban abin banza.” (Zabura 119:37) Allah yana son ka yi nasara, kuma idan ka roke shi zai ba ka karfi da za ka iya yin abin da ke da kyau!—Filibiyawa 4:13.

 Ka yi magana da wani. Tattauna wannan matsalar da amininka babban mataki ne, da zai taimake ka ka daina halin.—Misalai 17:17.

 Ka tuna cewa: Duk lokacin da ka guje wa kallon hotunan batsa, ka ci wani babban nasara ne. Ka yi addu’a ga Jehobah Allah game da nasarar, kuma ka gode masa domin karfin da ya ba ka. Idan ka guje wa kallon hotunan batsa, kana faranta masa rai!—Misalai 27:11.