Koma ka ga abin da ke ciki

TAMBAYOYIN MATASA

Abin da Ya Kamata In Sani Game da Aika Sakon Tsiraici ta Wayar Salula

Abin da Ya Kamata In Sani Game da Aika Sakon Tsiraici ta Wayar Salula

 Me ake nufi da aika sakon tsiraici?

 Aika sakon tsiraici ta waya yana nufin rubuta ma wani sakon da ke ta da sha’awa ko kuma aika hotuna ko bidiyo masu ta da sha’awa ta wayar salula. Wani mutum ya ce “abin da yake tāshe ke nan. Da kun soma tura wa juna sakonni, a hankali sai ku soma tura hotunan da kuka dauka a tsiraice.”

 Me ya sa mutane suke tura irin wadannan sakonnin? Wani shahararren lauya da aka yi kaulinsa a cikin jaridar The New York Times ta ce matasa suna gani kamar “samun hoton tsiraici na saurayinki ko budurwarka a cikin wayarka zai nuna cewa kai hadadde ne a batun jima’i.” Wata matashiya ma ta ce hakan “hanyar yin jima’i marar lahani ce domin ba za ki dauki ciki ba ko kuma ki kamu da wata cuta.”

 Wasu dalilai kuma da suke sa matasa aika sakon tsiraici ta wayar salula su ne:

  •   Suna so su yi kwarkwasa da wani da suke so su fita zance da shi ko ita.

  •   Wani ya tura musu hoton tsiraici kuma suna so su yi masa alheri ta wajen tura nasu hoton su ma.

 Mene ne sakamakon aika sakon tsiraici ta waya?

 Muddin ka tura hoto ta wayar salula, ya fita daga hannunka ke nan kuma ba ka da iko a kan yadda za a yi amfani da hoton ko kuma yadda zai shafi mutuncinka. Wata shahararriyar ‘yar bincike mai suna Amanda Lenhart, ta ce: “Ba a taba yin lokacin da mutane suka adana kurakurai da zunubai don a tura ma wasu su gani kamar yanzu ba.”

 Wasu lokatai

  •    Wani yakan tura hoton tsiraici ga abokansa da yawa domin su sami abin dariya.

  •    Wasu samari da budurwarsu ta ki su sukan rarraba hotunan tsiraici na budurwar don ramako.

 KA SANI? A yawancin lokatai, ana daukan aika hoton tsiraici daya da yin jima’i da yara ko kuma tura wa kananan yara hotunan batsa. A wasu lokatai, akan hukunta wasu yara da suka aika hotunan tsiraicinsu ko da ba su manyanta ba.

 Mene ne Littafi Mai Tsarki ya fada?

 Littafi Mai Tsarki ya nuna cewa ma’aurata ne kawai ya kamata su yi jima’i. (Misalai 5:18) Kuma ya haramta yin jima’i da kowane irin lalata tsakanin wadanda ba su yi aure ba. Ka yi la’akari da nassosin da ke gaba:

  •   “Amma fasikanci, da dukan kazanta, ko sha’awa, kada a ko ambata a cikinku, . . . ko dauda, ko kuwa zancen wauta, ko alfasha.”​—Afisawa 5:​3, 4.

  •   “Ku kashe zukatanku ga sha’awace-sha’awacen duniya, wato fasikanci, da aikin lalata, da muguwar sha’awa, da mummunan buri, da kuma kwadayi.”​—Kolosiyawa 3:​5, Littafi Mai Tsarki.

 Wadannan ayoyin sun hana “fasikanci” (wato, yin jima’i ba tare da aure ba) da “kazanta” (kalmar da ke nufin kowane irin rashin da’a) da kuma “sha’awa” (ba irin sha’awar da ma’aurata suke da shi na yin jima’i ba amma irin sha’awa da ke kai ga lalata).

 Ka tambayi kanka:

  •   A wace hanya ce aika hoton tsiraici ya zama kazanta?

  •   A wace hanya ce yin hakan yana jawo “muguwar sha’awa”?

  •   Me ya sa sha’awar kallon hotunan tsiraici ko kuma aika ma wasu “mummunan buri” ne?

 Nassosin da ke gaba sun ba da karin dalilai masu muhimmanci sosai da suka nuna cewa ya kamata mu guji aika sakon tsiraici ta wayar salula.

  •   “Ka yi kokari ka mika kanka yardaje ga Allah, ma’aikaci wanda babu dalilin kunya gare shi.”​—2 Timotawus 2:15.

  •    “Wadanne irin mutane ya kamata ku zama? Ya kamata ku yi zaman tsarkaka masu ibada.”​—2 Bitrus 3:​11, Littafi Mai Tsarki.

 Nassosin nan sun nuna sakamakon kasancewa da dabi’a mai kyau. Idan kana da hali mai kyau, ba za ka yi da-na-sani saboda irin rayuwar da ka yi ba.​—Galatiyawa 6:7.

 Ka tambayi kanka:

  •    Wane irin mutum ne ni?

  •    Ina damuwa da mutuncin wasu?

  •    Shin ina jin dadin ganin abin da ke sa wasu bakin ciki?

  •    A wace hanya ce aika sakon tsiraici ta wayar salula za ta iya shafan mutuncina?

  •    Ta yaya aika sakon tsiraici ta wayar salula zai iya hana iyayena su yarda da ni?

 LABARI “Ina da wata abokiya da ta fita zance da wani yaro a boye. Sai ta tura masa hotonta na tsiraici kuma shi ma ya tura mata nasa hoton. Bai kai awoyi 48 da suka yi hakan ba sai babanta ya dauki wayarta ya duba abin da ke ciki. Ya ga hotunan kuma hakan ya bata masa rai ba kadan ba. Ya kira ta ya tambaye ta kuma ta yarda da abin da ta yi. Na san ta yi da-na-sani sosai bayan haka, amma abin da ta yi ya rikitar da iyayenta kuma ya bata musu rai sosai. Suna ganin ba za su iya yarda da ita kuma ba.”

 Gaskiyar al’amari: Aika sakon tsiraici ta wayar salula yana zubar da mutuncin wanda ya aika hoton da mai kallon hoton. Wata matashiya da saurayinta ya tilasta mata ta aika masa hoton tsiraicinta ta ce, “Abin ya sa ni kyamar kaina kuma ina bakin ciki sosai.”

 Hakika zai dace mu bi wadannan umurnin daga Littafi Mai Tsarki da yake aika sakon tsiraici ta wayar salula tana da munanan sakamako sosai:

  •   “Ka guje wa sha’awoyin kuruciya.”​—2 Timotawus 2:22.

  •   ‘Ka kawar da idanuna daga duban abin banza.’​—Zabura 119:37.

 Me za ka yi?

 Ka bi shawarar Littafi Mai Tsarki a rayuwarka ta yau da kullum. Ka karanta abin da Janet ta fada sa’an nan ka zabi matakin da kake ganin ya fi dacewa.

 Janet ta ce: “Akwai ranar da na hadu da wani yaro kuma muka ba juna lambobin wayarmu. Mako daya bayan haka sai yaron ya ce in tura masa hotunan da na dauka sanye da kayan iyo.”

 Me kike ganin ya kamata Janet ta yi? Me za ki yi idan ke ce?

  •  ZABI NA 1 Za ki iya cewa: ‘Babu wani matsala da abin da ya fada. Balle ma idan muka je iyo tare, zai gan ni sanye da kayan iyo.’

  •  ZABI NA 2 Za ki iya cewa: ‘Ban san nufinsa ba. Amma bari in tura masa hoton da bai nuna jikina sosai ba don in ga abin da zai fada.’

  •  ZABI NA 3 Za ki iya cewa: ‘Wannan yaron yana neman ya yi lalata da ni ne kawai. Zan share sakonsa daga wayata.’

 Hakika Zabi na 3 ne ya fi dacewa, ko ba haka ba? Domin Littafi Mai Tsarki ya ce: “Mutane masu wayo sukan hangi masifa su buya, amma marasa tunani sukan taka su shiga cikin masifar sa’an nan su yi da-na-sani daga baya.”​—Misalai 22:​3, Good News Translation.

 Wannan gwajin ya nuna ainihin abin da ke sa mutane aika sakon tsiraici ta wayar salula har ma da yin lalata: Shin, kana zaban abokan kirki kuwa? (Misalai 13:20) Wata matashiya mai suna Sarah ta ce: “Ka zabi abokai daga cikin wadanda ba za su yarda da rashin da’a ba.” Wata kuma mai suna Delia ta ce: “Wasu abokai suna neman su bata dabi’unka masu kyau ne kawai, ba wai su taimaka maka ka koyi dabi’un kirki ba. Idan suna da halin da bai jitu da ka’idodin Allah ba, za su karfafa ka ka yi abin da ka sani bai dace ba. Za ka yarda musu su yi hakan?”