Koma ka ga abin da ke ciki

TAMBAYOYIN MATASA

Ta Yaya Littafi Mai Tsarki Zai Taimaka Mini?—Sashe Na Daya: Ka Bincika Littafi Mai Tsarki

Ta Yaya Littafi Mai Tsarki Zai Taimaka Mini?—Sashe Na Daya: Ka Bincika Littafi Mai Tsarki

 Wata matashiya mai suna Briana ta ce: “Na yi kokarin karanta Littafi Mai Tsarki, amma girmansa na karya mini gwiwa!”

 Kai ma kana jin haka? Wannan talifin zai taimaka maka!

 Me ya sa ya kamata in rika karanta Littafi Mai Tsarki?

 Shin ba ka jin dadin karanta Littafi Mai Tsarki? Idan haka ne, ba sabon abu ba ne. Za ka iya ganin cewa Littafi Mai Tsarki littafi ne mai dubban rubutu da babu hotuna kuma watakila ba za ka ji dadin karanta shi kamar yadda kake jin dadin kallon telibijin da bidiyo ba.

 Amma ka yi tunani: A ce ka tsinci wani tsohon akwati da watakila akwai abubuwa masu tamani a ciki, shin ba za ka so ka san abin da ke ciki ba?

 Littafi Mai Tsarki yana kama da wannan akwatin. Yana dauke da abubuwa masu tamani da yawa da za su taimaka maka ka

  •   Tsai da shawarwari masu kyau

  •   Zauna lafiya da iyayenka

  •   Sami abokan kirki

  •   Daina damuwa

 Ta yaya tsohon littafin nan zai amfane mu a yau? Zai amfane mu domin “Kowane Nassi hurarre ne daga wurin Allah.” (2 Timoti 3:​16) Wannan na nufin cewa Littafi Mai Tsarki ne tushin shawara mafi kyau.

Littafi Mai Tsarki akwati ne da ke dauke da abubuwan masu tamani.

 A wace hanya ce ya kamata in karanta Littafi Mai Tsarki?

 Wata hanyar ita ce in karanta shi daga fari zuwa karshe. Hakan zai sa ka san abin da Littafi Mai Tsarki ke dauke da shi. Akwai hanyoyin karanta Littafi Mai Tsarki da yawa. Bari mu ga misalai biyu:

  •    Za ka iya karanta littatafai 66 na cikin Littafi Mai Tsarki a yadda aka jera su daga Farawa zuwa Ruya ta Yohanna.

  •    Za ka iya karanta Littafi Mai Tsarki bisa ga labari, wato bi da bi bisa ga shekarun da abubuwan da suka faru.

 Abin Lura: Rataye na A7 a cikin New World Translation ya ba da jerin abubuwan da sun faru a rayuwar Yesu a nan duniya.

 Hanya ta biyu na karanta Littafi Mai Tsarki shi ne, ka zaɓi wani labarin wani da aka rubuta da ya yi kama da irin matsalolin da kake fuskanta. Alal misali:

  •   Za ka so ka sami abokan kirki? Ka karanta labarin Jonathan da Dauda. (1 Sama’ila, surori 18-​20) Bayan hakan sai ka yi amfani da shafin rubutu “Yadda Za Mu Sami Abokai Nagari” domin ka koyi darussa masu kyau daga labarin.

  •   Kana son ka karfafa yadda za ka iya guje wa jarraba? Ka karanta labarin yadda Yusufu ya guje wa jarraba. (Farawa, sura 39) Bayan hakan sai ka yi amfani da fallayen rubutu “Yadda Za Ka Guje wa Jaraba . . . Yusufu​—Sashe na 1” da kuma “An Yi Masa Ƙarya! Yusufu​—Sashe na 2” domin ka koyi darussa masu amfani daga labarin.

  •   Kana son ka san yadda addu’a zai iya taimaka maka? Karanta labarin Nehemiya. (Nehemiya, sura 2) Nan sai ka yi amfani da fallayen rubutu “Allah Ya Amsa Addu’arsa” domin ka koyi darussa masu amfani daga labarin.

 Abin Lura: Yayin da kake karanta Littafi Mai Tsarki, ka tabbata cewa babu abin da zai janye hankalinka a wurin da kake karatun.

 Hanya ta uku na karanta Littafi Mai Tsarki shi ne za ka dauki wani labari ko kuma wani sura a littafin zabura, sai ka karanta kuma bayan hakan, sai ka ga yadda labarin ya shafe ka. Bayan ka karanta, sai ka yi wa kanka tambayoyi kamar haka.

  •    Me ya sa Jehobah ya sa aka rubuta wannan labarin a cikin Littafi Mai Tsarki?

  •    Mene ne ya nuna game da halin Jehobah ko kuma yadda yake yin abubuwa?

  •    Ta yaya zan iya yin amfani da labarin a rayuwata?

 Abin Lura: Ka yi amfani da New World Translation ta nazari domin ka iya samun bidiyoyi da taswira tare da wasu abubuwan da aka tsara a ciki da za su iya taimaka maka ka amfana sosai cikin karatunka na Littafi Mai Tsarki.